Showing posts with label KANNYWOOD. Show all posts
Showing posts with label KANNYWOOD. Show all posts

Saturday, 18 May 2019

Kalli Zafaffan hotunan Jaruma Maryam Yola Nas

 Kyawawan Hotunan jaruma maryam yahya yola wanda tayi film din nas kuma tsohuwar matar Jaruma adam a zango.





Dalilin Da Ya Sa Nake Auri-saki – Adam Zango

Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya rabu da su. Jarumin ya bayyana cewa ba wai baya iya zama da mace bane, sai dai
" ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba."
“ Allah yana hada mata, mace da namiji. Allah ya halicci mata domin su kasance ni’ima a garemu maza. Don mu Allah ya halicce su."
Adam ya kuma bayyana cewa Allah ya rigada ya tsara ma mutum kaddararsa da abunda zai faru da shi tun kan a haifasa har izuwa ranar da zai amsa kiran mahallicinsa.
Dan wasan ya bayyana hakan ne a hira da yayi da shafin BBC Hausa inda yake cewa:
" Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa." “Kuma wannan kaddarar da Allah yayi mun itace tawa, saboda ni , Allah yana gani, Allah ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace wanda nake zaman aure da su.
“Sannan kuma ina so na gayawa mutane wani abu cewa, duk mutin da ya kasance zai yi aure ya rabu da mace, ya kara yi kuma ya kara rabuwa da ita, toh ya kamata su gane cewa wannan mutumin ba mazinaci ba ne. Saboda ni Adamu Zango Allah ya ba ni, duk duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda mata ke so iri na. Toh me zan yi da aure?”

Ban Taba Tsammanin wani A Masana'antar kannywood Zai Iya kaini Kotu ba Balle Ali nuhu - Adam A Zango

Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam Zango ya ce ya ji matukar kunya da mutumin da yake kira ubangidansa a masana'antarsu wato Ali Nuhu ya kai shi kara kotu.
Adamu ya ce bai taba tsammanin cewa wani a masana'antar zai iya kai shi kotu balle Ali.
"Ai muna da shugabanni, na yi tsammanin komai ya faru su za a gayawa su sasanta, amma sai aka kai kotu, gaskiya abin ya ban kunya," in ji Adamu.
A kwanakin baya ne dai jarumi Adam Zango ya wallafa wani sako inda ya yi ikirarin cewa tun da Ali ya sa aka zagi mahaifiyarsa shi ma sai ya rama.
Daga bisani ne Ali ya kai Adamu kotu, inda har aka aike wa Zangon sammaci.
Duk da yake a yanzu an sasanta jaruman biyu, sai dai ba dai wannan ne karo na farko da suka taba rikici har aka sasanta su ba, amma dai ba a taba batun zuwa kotu ba sai wannan karon.
Sai dai duk wannan rikici da ke faruwa tsakaninsu, a duk lokacin da BBC ta tuntubi Ali Nuhu ba ya cewa komai.
Ko a rigimar zuwa kotun ma, an tuntube shi kuma ya ce ba zai tofa komai ba sai dai a ji ranar zaman kotun.
A hirar tasa da Nasidi Adamu Yahaya kan batun kai masa sammacin, Adam ya kara da cewa: "Da na yi rubutu na zagi Ali ba alfahari nake da hakan ba, na san ba daidai ba ne.
"Sai dai daga bisani na fahimci abin da na yi ban kyauta ba, da nemansa na yi gaba da gaba na gaya masa maimakon shaida wa duniya.
"Amma na yi hakan ne saboda wadanda suka zage ni a dalilinsa su ma sun yada ne duniya ta gani."
Daga bisani dai an sasanta jaruman biyu da suka kasance na kut da kut a da.
"Amma daga baya manyanmu sun zaunar da mu sun sasanta mu, kuma na ba shi hakuri.
"Sai dai kamar yadda aka sa na ba shi hakurin nan, ai ya kamata shi ma a kalla ya sa yaransa masu zagina su ba ni hakuri ko da sau daya ne," in ji Zango.
HABAICI
A cikin hirar an kuma tabo Adamu kan dalilin da ya sa yake yawan yi wa makiyansa habaici a shafukan sada zumunta, sai ya ce yawan makiyan da yake da su ne ya sa yake yawan wallafa sakon habaice-habaice a shafinsa na Instagram.
Jarumin ya ce abin da ya dauka makiyi shi ne duk mutumin da ba ya bukatar ya ga "ci gabanka ko kuma idan ka yi wani abin burgewa, amma shi bai ga hakan ba, to makiyinka ne."
"Ko kuma mutumin da idan wani abu ya zo maka na karuwa kamar karramawa ko taron kalankuwa ko na biki, amma sai ya ce kar a bai wa wane, gara a bai wa wane, to makiyinka ne.
"Dole ne a masana'antarmu sai ka samu makiya, wasu na jikinka ne, ko daraktoci, ko jarumai ko furoduoshi ko 'yan wasa.
"Dan Adam bai son kishiya, duk wanda ya ga wani yana daga wa ko yana neman ya wuce shi a daukaka to zai ji haushi," a cewar Adamu.
Jarumin ya ci gaba da cewa idan ya yi maganar makiya to ba da mutum daya ko biyu yake ba, yana magana ne kan mutane da dama da suke nuna masa irin wadancan halayyar da ya ambata.
Wanda ya tsargu da shi ake.
Jarumin ya ce idan mutum ya yi habaici to duk wanda ya tsargu, tabbas yana cikin wadanda ya rubuta sakon saboda su.
"Sannan akwai masu bin mu wato fans, amma kuma makiya ne.
Za ka yi abin da ba wanda ya taba yi a duniya, amma sai su ce karya ne kwaikwayon wani ka yi.
"Don haka na kan yi wasu abubuwan ne don na burge masoyana, a hannu guda kuma na aikewa makiyana sako a fakaice cewa na san irin kiyayyar da suke min," in ji Adamu Zango.

BBChausa.

Friday, 17 May 2019

Kotu Ta Bada Umarnin A Kamo Hadiza Gabon Cikin Awanni 24

RIKOCI TSAKANIN GABON DA NABRASKA

Kotu Ta Bada Umarnin A Kamo Hadiza Gabon Cikin Awanni 24
Wata Kotun Majistari da ke zama a Birnin Kano, karkashin jagorancin Alkali Muntari Gambo Dandago, ta umurci Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano da ya kamo mata Jarumar Fim din Hausa, Hadiza Gabon. Sannan kuma kotun ta umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya binciki zargin da mai kara, Jarumi Mustapha Naburaska ya shigar a kan zargin cin zarafinsa da Hadiza Gabon din ta yi.
Alkalin ya yanke wannan hukunci ne sakamakon kauracewa zaman kotu da Hadiza Gabon ta yi a yau Alhamis.
Idan dai ba a manta ba, tun a kwanakin baya ne Naburaska ya shigar da karar Gabon kan zargin cin zarafi.

Rariya

Adam Zango Ya Bayyana Ko Su Waye Makiyansa

Fitaccen jarumin Kannywood Adamu Abdullahi Zango ya bayyana ko su waye ya dauka makiya da kuma dalilin da yasa yake musu habaici.
A hirar shi da Nasidi Adamu Yahaya, an tambayi Adam Zango akan dalilin da ya sa yake yawan yi wa makiyansa habaici a shafukan sada zumunta, sai ya ce yawan makiyan da yake da su ne ya sa yake yawan wallafa sakon habaice-habaice a shafinsa na Instagram.
Jarumin ya ce abin da ya dauka makiyi shi ne duk mutumin da ba ya bukatar ya ga “ci gabanka ko kuma idan ka yi wani abin burgewa, amma shi bai ga hakan ba, to makiyinka ne.”
“Ko kuma mutumin da idan wani abu ya zo maka na karuwa kamar karramawa ko taron kalankuwa ko na biki, amma sai ya ce kar a bai wa wane, gara a bai wa wane, to makiyinka ne.
“Dole ne a masana’antarmu sai ka samu makiya, wasu na jikinka ne, ko daraktoci, ko jarumai ko furoduoshi ko ‘yan wasa.
“Dan Adam bai son kishiya, duk wanda ya ga wani yana daga wa ko yana neman ya wuce shi a daukaka to zai ji haushi,” a cewar Adamu.
Jarumin ya ci gaba da cewa idan ya yi maganar makiya to ba da mutum daya ko biyu yake ba, yana magana ne kan mutane da dama da suke nuna masa irin wadancan halayyar da ya ambata.
Wanda ya tsargu da shi ake.
Jarumin ya ce idan mutum ya yi habaici to duk wanda ya tsargu, tabbas yana cikin wadanda ya rubuta sakon saboda su.
“Sannan akwai masu bin mu wato fans, amma kuma makiya ne.
Za ka yi abin da ba wanda ya taba yi a duniya, amma sai su ce karya ne kwaikwayon wani ka yi.
“Don haka na kan yi wasu abubuwan ne don na burge masoyana, a hannu guda kuma na aikewa makiyana sako a fakaice cewa na san irin kiyayyar da suke min,” in ji Adamu Zango.

Thursday, 11 April 2019

WANI MATASHI YA SHA ALWASHIN KARBAR BASHIN BANKI DAN ZUWA GURIN NAFISA ABDULLAHI SU YI WANI ABU

Soyayya takan sa mutum yayi abinda shi kanshi zai baiwa kanshi mamaki, musamman idan ya kamu sosai, kusan hakannne ke shirin faruwa da wani matashi da yace jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi na birgeshi.
A sakon daya aika mata ta Twitter,yace ana girma ana rage kyau amma Nafisa kullun kara kyau kike, sai na amshi bashin banki dan inzo in ganki mu dauki hoto.
Ban taba ganin mace me kyanki ba.
Nafisar dai tace ba fashin baki, hoto kawai.


JARUMI ALI NUHU YA MAKA ADAM A ZANGO KOTU

A yaune dai shahararren jarumi kuma mai fada aji a masana’antar kannywood wato jarumi Ali Nuhu ya maka fitaccen jarumi Adam A Zango a kotu bisa abinda ya kira bata suna da cin mutunci da Zango yayi masa.
A takardar sammaci da kotun ta aikewa da jarumi Adam zango a yau alhamis, kotun ta bukaci da ya bayyana a gabanta a ranar litinin mai zuwa (15/04/2019) don amsa ko kare kansa bisa wannan tuhuma da jarumin yake masa.
A yayin da jarumi Adam A Zango ya karbi wannan sammaci, sai ya maida martani kamar haka:
Idan baku manta ba a cikin yan kwanakin nan ne dai aka samu rashin jituwa tsakanin manyan jaruman guda biyu inda har ta kaiga jarumin Adam Zango ya rinka zagin Ali Nuhu.
Ko kuna ganin wannan mataki da jarumi Ali Nuhu ya dauka yayi daidai duba da yadda wasu jaruman ke daukar doka da hannunsu idan aka yi musu ba daidai ba?

Monday, 1 May 2017

Jaruma Hadiza Gabon Na Cin Kilishin O&B .


Ban taba cin kilishi mai daadin O&B kilishi ba. Nasan zaku ce santi amma hausawa sun ce maganin karya hallara ku saya ku zo ku bani labari.

Jarumar Ta Wallafa A Shafinta Na Instagram.

® www.Amanagurus.Com.ng

Sunday, 30 April 2017

Takai Taccen Tarihin Mawaki Umar M Shareef





Tarihina a takaice

Assalamu alaikum, sunana Umar Muhammad Sharif, an haife ni a Rigasa da ke Jihar Kaduna a shekarar 1987. Na yi makarantar firamare da sakandare duk a Rigasa. 

Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka

Waka ta fado mini kwatsam da rana tsaka ne, amma a gaskiya ban taba tunanin zan yi sana’ar waka ba, saboda tun tasowata ni dalibi ne, ina karatun boko da na addini, na ma fi ba da karfi a bangaren addini. Silar fara waka kuwa ita ce akwai wata budurwa da nake matukar so da kauna, amma na kasa sanar da ita abin da ke zuciyata.

A gaskiya jin nauyin abin shi ne ya hana ni sanar da ita. Nakan je har kofar gidansu, na aika a yi mini sallama da ita, amma inda gizo ke sakar shi ne da zarar ta fito don ganin wanda ke neman ta, sai na buya, ta gama dube-dubenta daga nan idan ba ta ga kowa ba sai ta koma gida.

To na yi hakan kusan har sau uku ba tare da samun damar tsayawa da ita ba. Daga nan wata rana sai na yi ta maza na ce zan ga abin da zai ture wa buzu nadi. 

Da na je sai na aika kamar yadda na saba amma sai a wannan karon ba ta fito ba. Na yi ta jira amma shiru kake ji.

To daga nan ne fa kamar wasa sai na fara yin waka a kan halin da na samu kaina ciki. Daga kofar gidansu na fara waka har na isa gida ban daina ba. Haka na yi tayi duk lokacin na tuna da wannan baiwar Allah.

A cikin wannan halin ne sai na samu biro da takarda na rubuta wakar. Akwai wani mawaki Ibrahim Suleiman (Zaki) wanda ya kasance abokin yayana ne. Kamar wasa da ya ga wakar kuma ya umarce na rera ta. Bayan ya saurari wakar sai ya yaba kuma ya yi min wasu gyararraki, kana ya karantar da ni kabli da ba’adin waka. Daga nan ne fa na fara waka gadan-gadan.

Kalubale

Da farko na fuskanci kalubale daga gida, daga bisani muka fahimtar da iyayenmu. Bayan ba su ga canji daga irin tarbiyyar da suka yi mana ba, sai suka fara sa mana albarka da fatan alheri. Shakka babu addu’o’insu na tasirin sosai a kan nasarorin da muke ci gaba da samu.

Wakokin da na yi

A kalla wakokina za su kai 700

Kundin waka

Akwai su kamar haka: ‘Duniya Ce’ da ‘Nadiya’ da ‘Shahuda’ da ‘Madubi’ ‘Mai Atamfa’ ‘Babbar Yarinya’ ‘Wacece’ ‘Kalaman Bakina’ ‘Bako’ Da dai sauran su...

Bakandamiyata
Duka wakokina.

Fitowa a fim

Ina fitowa a fim, sannan nakan shirya nawa. Fina-finan da na fito sun hada da: ‘Mahaifiyata’ da ‘Nas’. Fina-finan da na shirya sun hada da: ‘Ba Zan Barki Ba’ ’Ka So A So ka’ da ’Jinin Jikina ’ Sannan Akwai Wani Film Dana Fito A Cikin sa a wannan shekarar Mai suna Mansoor.

Burina

Ba ni da wani burina saboda ko yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba. Sunana ya kai duk inda ba ka zato, saboda na sha samun kira ta waya daga Amurka da sauran kasashen duniya, wanda jama’a ne masu sauraren wakokinmu ke yaba mana.

Iyali

Ina da mata daya Maryam da da daya ana kiransa Aliyu.

Source : www.HausaMedia.Com

Saturday, 29 April 2017

Shiganan Ku kalli kyawawan hotunan rahama sadau

Je kasa



Sunday, 23 April 2017

Banyi Dana Sanin Zuwana Kasar Amurka Ba -- Rahama Sadau.


Jaruma Rahma Sadau ta musanta zargin da akeyi ma ta cewa tayi danasanin zuwa kasar America. - Acewar jarumar ba wani da nasani da nayi domin adalilin sana'a naje bada niyar shashanci ba. 

Amma abinda nasan nace shine, "tabbas akwai banbanci tsakanin America da Nigeria awajen yin fim," banbancin abayane yake.

idan kai bahaushe ne to kayi sana'ar fim din hausa yafi maka amfani. domin shine wanda zai kare mutuncin mutum.

Dan haka a ra'ayina Hausa fim yafi min American fim, amma awajen hausawa.

kuma ni da America gwara kasata Nigeria. wannan maganar nasan kawai na fada amma jama'a sai suka canja min magana.

Sannan kuma Jarumar ta kara da cewa zanyi amfani da wannan damar nayi godiya zuwaga Ali Nuhu, Sani Danja da sauran mutanen da suke kokari awajen ganin nadawo masana'antar hausa fim.

® Naij Hausa

Zamu Saki Film Din Mansoor Da Karamar Sallah_Ali Nuhu

Ali Nuhu


Shahararre kuma gogarman Kannywood, jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewar fim din kamfanisa, Mansoor da aka kammala dauka kwanan baya za a sake shi a sinumun Nijeriya lokacin bukukuwan karamar Sallah.

Jarumin ya bayyana haka ne yayin tattaunawar musamman da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce duba da yanayin irin aikin da aka yi wa fim din, kamfanin FKD sun yanke shawarar sakinsa a bukukuwan sallah.

“Mansoor fim ne da aka kashe makudan kudade wajen yin sa, saboda haka hanyoyin tallata shi kadai sun bambanta da yadda ake yi wa saura finafinai. Mun zabi lokacin bukukuwan karamar sallah ne domin domin bawa mutane damar kallon sa kasnacewar ana hutu.” A cewar Ali Nuhu. 

“Mutane da yawa sun kagu su ga wane sako Mansoor ke dauke da shi, abin da nake so in tabbatar shi ne, fim din ya zo da wani irin salo wanda ba a saba gani ba. 

“Duk wanda ya ga yanayin jaruman da aka sanya a cikin fim din, zai ga cewa sabbi ne, watau wadanda ba su taba fitowa a matsayin cikakkun jarumai ba. Da ma shi kamfani FKD ba bako ba ne wajen dauko kananan jarumai ya wanke su, sannan ya saka su a finafinansa.” In ji shi. 

Mansoor fim ne da ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Abba El-Mustapha, Tijjani Faraga; sai kuma sabbin jarumai, Umar M Shareef da Maryam Yahaya. 

Wannan dai shi ne fim na farko da FKD ta shirya tun bayan fim din da ya tara zaratan jarumai maza zalla watau Ga Mu Nan Dai. 

® Leadership Hausa

Rahma Sadau Ta Maka Nafisa Abdullahi A Kotu.

 Nafisa Abdullahi Da Rahama Sadau

Jaruma Rahma Sadau ta maka Nafisa Abdullahi a kotu. wanda tace tana neman hakin ta agun Nafisa Abdullahi. 

Wanda tace ta hana ta kudin ta har naira dubu tamanin da tara. Wanda Rahma Sadau taba Nafisa Abdullahi domin ta fito acikin fim din ta maisuna RARIYA. Amma har aka gama yin fim din Nafisa Abdullahi bata fito koda sau daya acikin fim din ba.

Anayin wannan sharia'a ne akotun Nomans land dake jihar Kano.

Majiyar mu ta kotu Sadiya Rk Panshekara ta ruwaito mana cewa: za'aci gaba da sauraron shar'ar ranar litinin.

Kamar yadda majiyarmu ta tattaro cewa a zantawar da wakiliyar mu tayi da wadda akeyin kara Nafisa Abdullahi sai jarumar tace: ni ba wasu kudi da Rahma ta bani dan nayi mata fim.

Abinda nasani shine, tace tanaso na fito acikin fim din ta maisuna RARIYA nace zan fito amma sabida wasu dalilai ban fito ba, amma ni ba wasu kudi da ta bani. Inji Nafisa Abdullahi.

To, mu dai aikin mu bibiya. zamu ci gaba da kawo maku yanda shari'ar take tafiya.

® Naij Hausa

Yadda Wakokin Film Din Mansoor Suka Samu Karbuwa Tun Kafin Film Din Ya Fito


A kwanakin baya ne shahararren kamfanin shirya finafinan Hausa FKD, ya fitar da taba ka lashen sabbin wakokin fim dinsa mai suna Mansoor, wadanda yanzu haka suka yamutsa hazo a farfajiya Kannywood, duk da cewa ba a fitar da su kasuwa ba.
Da yake zantawa da wakilinmu game da yadda wakokin suka samu karbuwa a zukatan al’umma, wani darakta da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce hakika idan ana batun zuwa da wakoki masu dadi a cikin finafinan Hausa, to kamfanin FKD shi ne kan gaba wajen ganin ya zo da dadadan wadodin masu sanyaya zuciyar mai sauraro.
“Kamfanin FKD ya yi kaurin suna ta wannan bangaren tun shekaru da dama da suka gabata. Domin sun fitar da wakoki wadanda har yau din nan an kasa mantawa da su irinsu: Mujadala, Fil’Azal, Sai Wata Rana, Madubin Dubawa, Adamsy, Sirrin Da Ke Raina, Halacci, Halwa da kuma baya bayan nan Gamun Nan Dai.” In ji shi.
Wannan karon kamfanin ya sake zuwa da wani salon na daban, wanda za a iya cewa shi ne irinsa na farko a cikin wani sabon shiri mai suna MANSOOR. Wakokin fim din; Abin Da Yake Raina, Zan Rayu Da Ke, Makullin Zuciya, Macukule, Jirgin So Zai Tashi da Ya Mansoor Na, tuni sun hau kan kadamin zamowa shahararru da za su dade a kunnunwa masoya.
Hakika Umar M Shareef, Abdul D. One, Murja Baba, Maryam Fantimoti, da Khairat Abdullahi da suka bada muryoyinsu wajen rera wadannan wadodi na madaukakiyar soyayya sun taka rawar gani. Da ma me ake tsammani daga wurin mutanen da suke da tarin basira wajen sarrafa murya don yi wakar soyayya? Bari mu dan kalli wakokin don yin bayani a kansu…
Abdul D. One (Marubucin Waka kuma Mai Rerawa), ya yi amfani da muryarsa wajen rera wakar ‘Abin Da Yake Raina’ da a yanzu samari da ‘yan mata ke yin guzurinta don farantawa juna rai. Tabbas dadin wakar ya kai matsayin da idan mutum ya kunna sai dai ya yi ta ji ba tare da ya canja wata ba, saboda muryarsa tana da dadin sauraro. Maryam Fantimoti, ita ma ba a bar ta a baya ba, domin wakar da ta rera ‘Ya Mansoor Na’ tuni ta shiga sahun shahararrun wakoki ababen saurare.
Macukule,’ duk da ba irin wakokin da Umar ya saba yi ba ne, amma ya yi matukar kokari tun daga farkonta har karshe. Babu wani sabon abu a cikinta, amma tsarin kid’anta ya yi matuk’ar dadi. Har ila yau, lafuzan da aka yi amfani da su sun tsaru tsaf, ta yadda za a nishadantar da mai sauraro. Hakika idan wakar ta samu talla sosai, za ta zamo daya tamkar da dubu a wurin masoya sauraron waka.
Fitar wakar ‘Zan Rayu Da Ke’ ya sauya salon album din gaba daya, domin Umar M. Shareef ya kara nuna wa duniya cewar indai bangaren wakar soyayya ne to ba shi da na biyu. Duk wani masoyi, ko masoyiya, zai so a ce shi ake rerawa wannan waka. Tuni ya sanya hatta manyan jaruman a Kannywood da sauran mutane rera wakar suna dora ta a shafukansu na Instagram, yayin da jarumi Ali Nuhu ke bayyana farin cikinsa da zarar sun yin hakan.
Jirgin So Zaya Tashi’ wadda Umar suka rera tare da Murja Baba ta yi dadi matuka, hakan yana kara bayyana basirar mawakin a fili. Kidan ya tsaru matuka, zubin tsarin zantukan da aka yi amfani da abun burgewa ne. Kai da nemi wakar kawai ka saurara.
Makullin Zuciyata’ irin wakokin nan ne da idan mutum ya fara saurara shi kenan sun shiga jikinsa, batun dainawa ma sam bai taso ba. Waka ce da ke bayyana irin yadda masoyi ya kamu da son masoyiyarsa, da kuma irin fatan da yake da shi na ganin ta karbi soyayyarsa da hannun biyu.
Wadannan su ne wakokin da fim MANSOOR yake dauke da su. Ana sa ran fitarsu nan ba da jimawa ba.
Babban abinda aka fi mayar da kai yanzu haka shi ne, yanayin yadda labarin fim din zai kasance, domin an ga mawaki Umar M. Shareef ya yi tsalle tare da fadowa duniyar jarumai don a dama shi. Ganin Umar cikin fim din ya sanya masoya zuba ido, suna jiran ganin yadda zata kaya.

Labari: Ali Nuhu
Tsarawa: Jamil Nafseen
Rubutawa Waka: Umar M Shareef, Abdul D One
Rerawa: Umar M. Shareef, Abdul D. One, Maryam Fantimoti, Murja Baba da Khairat Abdullahi.
Koyar Da Rawa: Ali Nuhu
Shiryawa: Nazir Dan Hajiya
Bada Umarni: Ali Nuhu
© HausaMini.Com

Ummi Zee Zee - Har Yanzu Nafi 'Yan Matan Kannywood Aji.

 Ummi Zee Zee


Ummi Ibrahim ZeeZee ta kasance shahararriyar ‘yar fim ce wacce ta ci zamanin ta a baya – Jarumar ta bayyana cewa ita ta fi ‘yan fim aji ta kuma jadadda soyayyarta da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida Ummi Ibrahim ZeeZee ta kasance shahararriyar ‘yar fim ce wacce ta ci zamanin ta tsakanin 2004 zuwa 2006.

A cikin wata hira da akayi da jarumar, ta bayyana cewa tafi yan fim aji, domin ita asali a kasar Saudiyya take zaune. Asali ma ta shiga harkan fim ne kawai don sha’awa da ra’ayi amma ba wai domin kudin da za’a biya ta ba.

Da aka tambayi jarumar kan cewa ko ta taba yin furucin cewa ta fi yan fim aji, Jarumar tace: “Wannan ma ai ba sai ka tambaya ba. 

Ka tuna fa ni da farko a Saudiyya ma na ke zaune. Amma da na yi wani zuwa Nijeriya, sai na yi sha’awar harkar fim. To tun cikin 2004 ban sake zama Saudiyya ba, sai dai na je aikin Hajji ko Umra na dawo.

Ni fa har yau ban taba fashin zuwa Umra ba. Kuma aikin Hajji na sha yi ba sau daya ko sau biyu ba.” Har yau na fi ‘Yan matan fim aji – Ummi ZeeZee Tsohuwar yar wasan Kannywood, Ummi Ibrahim ZeeZee “Ko a lokacin da na ke yin fim, ni ba don neman kudi na ke yi ba. 

Kawai sha’awa ce.Kusan kashi 95% bisa 100% idan na yi fim ba na ma karbar ladar da za a biya ni. Su kan su furodusoshin ma sun sani, ko sun ba ni wani lokaci a wurin zan rabar da kudin, ko kuma idan na je gida na ba mabukata.”

Sannan Da aka zo kan al’amarin soyayyar ta da tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ta ce: “To ni dai tun ina sakandare IBB shi ne gwarzo kuma gwani na a duk cikin shugabannin kasar nan da aka yi.

To daga baya muka hadu, kuma da aure na ke son sa. “Idan babu soyayya a tsakanin mu zan fito na ce akwai ne? Ya taba cewa karya na ke yi? Ko ya taba cewa na daina fada? “Babban mutum kamar IBB na isa na fito na yi masa karya ne? Idan bai san da maganar ba, ai sai ya fito ya ce karya na ke yi. Shi ya sa wai idan ka ji an ce wai na ce a kasuwa na ke ko kaza da kaza, to ni ba a kasuwa na ke ba.

Na fi karfin na yi tallar kai na. Aji na ya wuce na tallata kai na. Roko na a yi mana addu’ar fatan alheri kawai.” 

© Mujallarmu

Monday, 17 April 2017

KANNYWOOD: INASO NAFI MAHAIFINA SUNA DA DAUKAKA INJI YARO AHMAD ALI NUHU

Ahmad Ali Nuhu Yarone Wanda Yake Da Ga Jarumi Ali Nuhu Yanzu Haka Yana Mutukar Kokari Acikin Masana'antar Ta Yadda Har Yake Fatan Yafi Mahaifinsa Suna Da Daukaka. 

Yanzu haka dai yaron yayi finafinai masu Armashi irin su
1. Da Da Uba
2. Carbin Kwai
3. Dace Da Juna
4. Dan Almajiri
Dadai Sauransu
Kuna ganin Yaron Zai iyafin
Mahaifinshi Ali Nuhu Suna Da Daukaka?

CIKAKKEN BAYANI AKAN YADDA BIKIN MAWAKI NURA M INUWA ZAI KASANCE

Ga Yadda Shirye Shiryen Zai Kasance
1..Kamu___on 27/4/2017  
Lokaci_____5PM 
Wuri_____Soli Center Katsina.
2..DINNER____On 28/4/2017.  Lokaci_____8.PM.  
Wuri_____NYSC Camp KT.
3..Football_____ On 28/4/2017.  Lokaci____10.AM.
Wuri_____Karakanda Stadium. 
4.. Aure_____On 29/4/2017
Lokaci_______2:00PM Wuri_____Malunfashi Local Government....
Allah yabada ikon halarta amen kuma allah yasa ayi lfy

Friday, 14 April 2017

KANNYWOOD: ABUBUWAN ALLAH WADAI GUDA 5 DASUKA FARU A MASANA'ANTAR KANNYWOOD A SHEKARAR 2016

Abubuwa da dama sun faru tun bayan kafuwar fannin fina-finai na Kannywood fiye da shekara 20, sai dai akwai fitattun abubuwan da suka fi janyo cece-kuce musamman a 'yan shekarun baya-bayan nan.
Mun yi nazari kan abubuwa biyar da suka fi tayar da kura a a masana'antar, wacce ke da farin jini sosai:
Abubuwan kace-nace 6 da suka shafi taurarin Kannywood a shekarar 2016
1. Auren jinsi
Wani abu da ya jan hankali sosai kuma ya tayar da jijiyar wuya shi ne zargi hada auren jinsi da aka yi wa wasu taurarin Kannywood hudu da yi a birnin Kano a watan Afrilun shekarar 2007.
Lamarin da ya sa suka shiga buya, bayan hukumar shari'a ta Hizba ta samu labarin sannan ta shiga nemansu.
Ko da yake a wata hira da BBC Aunty Maiduguri wadda aka zarga da hada auren ta musanta zargin.
2. Fim din batsa ko Blue Film
'Yan Kannywood sun samu kansu a tsaka mai wuya a watan Agustan shekarar ta 2007, inda aka zargi Maryam Usman Hiyana da Saurayinta Usman Bobo da yin fim din batsa.
Fim din da aka yita yadawa kuma ya janyo matukar suka ga masu harkar fina-finan.
Fim din batsan ne kuma ya kawo karshen fitowar Hiyana a fina-finan Hausa bayan an kore ta.. 
3. Zargin luwadi
A watan Agustan bana ne kuma zargin luwadi ya dabaibayi masana'antar.
Lamarin da ya kai har fitaccen jarumin nan kuma mawaki, Adam A Zango, rantsuwa da alkur'ani mai tsarki yana kare kansa.
Batun ya taso ne bayan da aka zargi wasu daga cikin masu harkar fimdin da cewa 'yan luwadi ne.
Sai dai a wannan karon babu wani da aka fayyace sunansa.
Abubuwan kace-nace 6 da suka shafi taurarin Kannywood a shekarar 2016
4. Gina alkaryar fim
Batun gina alkaryar fim a jihar Kano wanda gwamnatin tarayyar ta so gudabarwa ya tayar da jijiyoyin wuya a baya a watan Julin bana.
Malaman addini da jama'a ne suka nuna adawa da shirin, suna masu cewa zai daurewa badala da shashanci gindi a jihar.
Sun zargi 'yan fim da cewa mutane marasa kamala da ke yada batsa.
Sai dai masu shirya fim din sun ce ba haka lamarin ya ke ba, kuma mummunar fahimta ake yi musu.
5. Rahama Sadau ta rungumi Classiq
Batun rungumar mawakin nan, Classiq da Rahama Sadau ta yi shi ne abu na baya-bayan nan da ke jan hankali masu bin al'amuran Kannywood da ma jama'ar gari.
Yayin da wasu ke sukarta kuma kungiyar shirya fina-finan Hausa ta kore ta, Rahama ta nemi gafara tare da kokarin fahimtar da mutane cewa duk abin da ta yi a wakar aikinta ne ya bukaci haka ba son rai ba.

Thursday, 13 April 2017

JARUMI ADAM A ZANGO YA AIKATA WANI ABIN BAZATA

Mutane masu tarin yawa sunyi mamaki akan abinda Adam A Zango ya aikata. Nasan wasu zasu zaci wani abin alkaba’in jarumin ya yi. To ba abin alkaba’i ya yi ba. Abin nan ne da ake cewa anazaton wuta amakera sai kuma akaji doriarta amasaka.
.
Abin ya farune agarin Kaduna State. Abinda ya faru kuwa shine: jarumi Adam A Zango ne ya gina wani katafaren massalachi a Unguwar Zangon kataf. Wanda masallachin samin irinsa sai a birnin Abuja. Wannan abinda Adam ya yi yaba wasu mutanen mamaki, domin su azaton su sai dai ya gyara gidan buga wakoki.
.
Wannan ya nuna afili cewa Adam A Zango mutum ne mai kishin islama. Amma a baya wasu cewa suke baya sallah. Wannan kuma karyane Adam yana sallah yana azumi ya sauke farali. Sannan ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah sannan Annabi Muhd bawan Allah ne kuma manzon Allah ne.

Jarumi Adam A. Zango Ya Gina Katafaren Masallaci.

 Adam A Zango

Jarumi Adam A. Zango Ya Gina Katafaren Masallaci A Garin Su, Zangon Kataf Dake Jahar Kaduna A Nigeria.


DAGA :- Adamu Sani Chirome. 

Jarumi Adam A.Zango Ya Gina Katafaren Masallaci A Mahaifarsa, Ta Zangon Kataf, Dake Jahar Kaduna A Tarayyar Nigeria.

Inda Hakan Yayi Matukar Bawa Jama'a Da Yawa Mamaki Bisa La'akari Da Yadda Jarumin Yayi Kaurin Suna Gami Da Shan Suka Daga Wasu Tsiraru Cikin Al'umma.

Ta Yadda Suke Yada Cewa Jarumi Zango Baya Sallah Kuma Wai Dan Kungiyar Asarine, Wanda Jarumin Yasha Musanta Hakan A Wurare Da Dama Tare Da Kwararan Hujjoji.

To Yanzu Dai Ta Faru Ta Kare Game Da Wannan Zargi Domin Kuwa Yau Gashi Duniya Kanta Ta Shaida Game Da Ire Iren Ayyukan Da Wannan Jarumi Ke Assasawa Game Da Taimakon Al'umma Da Kuma Addininsa A Zahiri.

Domin Kuwa Ko A Kwanakin Baya Sai Da Jarumin Ya Kaddamar Da Gidauniya Ta Musamman Domin Tallawa Al'umma Musamman Marayu da gajiyayyu