Showing posts with label DAKIN GIRKI. Show all posts
Showing posts with label DAKIN GIRKI. Show all posts

Saturday, 5 November 2016

YADDA AKE YIN KOSAN HANTA

KOSAN HANTA
<<<<<<>>>>>>>
Hanta
Kwai
Fulawa
Baking powder
Butter
Mai
Attaruhu,albasa
Maggi,Gishiri,Curry
YADDA AKE YI:-
Zaki dafa hanta da maggi gishiri da curry
idan ta dahu sai ki juyeta ki dakata tayi
laushi sai ki juyeta a kwano me kyau,
sai ki jajjaga attaruhu da albasa ki zuba a
kai ki fasa kwai shima ki zuba akai ki zuba
fulawa da butter ki kwaba su su kwabu
sosai kisa ruwa kadan tare da baking
powder maggi gishiri&curry ki juya sosai ki
dinga diba kina sawa a mai me zafi,idan ya
soyu ki kwashe.

Yanda Ake Hada Alawar Madara

ABIN BUKATA Madara gari gwangwani 3 Sikari
gwangwani 2 Filebo YADDA ZA AYI A zuba ruwa
rabin gwangwani tare da sikarin da filebi zasu
dahu har yayi yauki sai a sauke sannan a zuba
madarar a tuka shi sosai sannan a shafawa leda
dan mai ta baya sannan a juye madarar akai
amma a dora ledar akan tiren don zai fi yankuwa
ta dadi.a yankashi yadda ake so