Showing posts with label ILIMIN KIMIYA DA FASAHA. Show all posts
Showing posts with label ILIMIN KIMIYA DA FASAHA. Show all posts

Wednesday, 11 January 2017

Kun san abin da zai sa tsofaffi su riƙa jin daɗin bacci?

Masana kimiyya sun shawarci mutanen da suka
kai shekara 50 zuwa sama da su kauracewa
shan gahawa ko kofi bayan cin abincin rana idan
dai suna so su yi bacci mai dadi da daddare.
Wani rahoto da kungiyar masana kan lafiyar
kwakwalwa ta charity Age da ke Birtaniya ta fitar
ya ce samun bacci mai dadi yana yi wa tsofaffi
wahala amma samun isasshen hutu zai taimaka
wa kwakwalwarsu ta rika tunani mai kyau.
Rahoton ya bai wa tsofaffi shawara su rika yin
baccin awa bakwai zuwa takwas da daddare,
sannan suka fitar da hanyoyin da suke gani idan
an bi su za a tabbatar da hakan.
Baya ga daina shan gahawa, rahoton ya bukaci
tsofaffi su takaita kalular da suke yi da rana
zuwa kasa da awa daya.
Sauran shawarwarin su ne:
Su rika tashi daga bacci a lokaci daya
kowacce rana
Su rika shan hantsi
Kada su sha giya
Su ci abincin dare awa uku kafin su yi bacci
Kada su rika karatu ta kwamfuta ko wayar
salula ko kwamputar tebur kafin su kwanta
bacci
Su gujewa yin amfani da magungunan da ba
likita ne ya ce a yi amfani da su ba
Su rika sanya safa a kafafunsu kafin su yi
bacci
Kada su yi bacci tare da daddobin gida irin
su kyanwa
Su gujewa yin musu da matarsu ko
mazajensu kafin su kwanta

Tuesday, 27 December 2016

Apple zai fara kera mota mara matuki

Kamfanin Apple ya ce yana shirin soma kera motoci marasa matuka.
A wata wasika da ya aike wa hukumar da ke sanya ido kan sufuri ta Amurka, Apple ya ce yana "matuka murna kan yadda fannin fasaha ke sauyawa ciki har da fannin sufuri".
Ya kara da cewa al'uma za ta mori sauye-sauyen da ake samu a motocin da ake kerawa marasa matuka.
An dade ana rade-radin cewa Apple zai soma kera motoci marasa matuka, amma sai yanzu kamfanin ya tabbatar da batun.

Wednesday, 30 November 2016

An dakatar da karin kudin data a Nigeria

Hukumar da ke sa ido a a kan kamfanonin
sadarwa ta Najeriya, NCC ta dakatar da shirinta
na kara kudin data ga masu amfani da wayar
salula.
Wata sanarwa da mai magana da yawun
hukumar, Tony Ojobo ya aikewa manema labarai,
ya ce sun dauki matakin ne sakamakon sukar da
suke sha daga wurin jama'a.
A cewarsa, hukumar ta umarci kamfanonin
sadarwa su dakatar da kara kudin datar kan
masu amfani da su.
A makon jiya ne hukumar ta bai wa kamfanonin
sanarwar umarnin kara kudin da suke sayar da
data zuwa kwabo 90 kan kowanne mega bite
daga ranar daya ga watan Disamba mai zuwa.
Sai dai 'yan Najeriya sun soki matakin, suna
maus cewa wani yunkuri ne na hana su fadar
albarkacin bakinsu.
Kafin a saoke karin zai shafi manyan kamfanoni
ne irin su MTN da Globacom da Airtell.
Haka kuma an yi niyyar rage farashin datar da
kananan kamfanoni.
A baya dai manyan kamfanonin na sayar da data
a kan: Etisalat N0.94k/MB, Airtel N0.52k/MB,
MTN N0.45k/MB da kuma Globacom N0.21k/MB.
Su kuma kananan kamfanoni na sayar da data a
kan: Smile Communications N0.84k/MB,
Spectranet N0.58k/MB da kuma NATCOMS
(NTEL) N0.72k/MB.

Sunday, 20 November 2016

Hanyoyi 6 da zaku iya gane shinkafar bogi

Rahotannin da ke yawo suna nuna cewar
wasu bata gari daga kasar Sin watau China
sun fara cika kasuwannin kasashen Afrika
ciki kuwa hadda Najeriya da wata samfurin
shinkafar bogi ta roba
– Ita dai kasar ta Sin ta yi kaurin suna
wajen samar da kayayyakin anfani na bogi
ciki kuwa hadda kayayyakin abinci
Shinkafa
Tun farko dai wata jaridar kasar Korea ce ta
fara bankado labarin na wasu yan kasar
China din da ke kera shinkafar roba kuma
tuni har sun fara rarraba ta a kasashen
duniya musamman ma a Afrika.
Ga wasu hanyoyi nan har guda 6 da
amintaccen kamfanin jaridar nan taku na
NAIJ.com ya zakulo maku don anfanin
kawunan mu kan hanyar da za’a bi wajen
gane shinkafar ta boji. Gasu a kasa:
1. Hanyar turmi da tabarya
Idan ku ka samu shinkafar ku sai ku dan
daka ta a cikin turmi da tabarya, idan har ta
dan yi farin gari to tabbas wannan shinkafar
ta kwarai ce mai kyau amma idan kuka ga
wani koriyar kala tana fita daga gare ta to
tabbas shinkafar bogi ce. Sai a kiyaye.
2. Gwaji da wuta
Ai ina fata dai duk munsan yadda kaurin roba
yake idan ana kona ta ko? To hakan ne ma
ake yin wannan kwagin. Idan kuka samu
shinkafar sai a nan kona ta, idan har ta
kama da wuta kuma aka ji kaurin to tabbas
tanan ma za a iya tantancewa.
3. Gwaji a cikin ruwa
Idan muka samu kofi da ruwa a ciki sai a
nan dibi shinkafar da ake kokwanto a zuba a
cikin kofin. Idan har shinkafar ta nutse a
cikin ruwan to tabbas tana da kyau da
inganci, idan kuwa akasin haka ya faru to
tabbas ta bogi ce.
4. Gwajin dambada
Yadda ake wannan gwajin kuma shine a
samu shinkafar da ake kokwanto sai a dan
dafa ta kadan sai a tsameta abarta a wani
wuri mai lema ta kwana kamar 2 zuwa 3.
Idan har tayi hunhuna to tana da kyau
kenan.
5. Ta hanyar tafasawa
Idan ana tafasa shinkafar da ake kokwanton
sai a kula da irin kumfan da ke fita a jikin
tukunyar. Idan har kuka ga kumfan da takeyi
ya wuce misali, to tabbas shinkafar ta bogi
ce.
6. Gwaji ta hanyar tafasashen mai
Sai a samu shinkafar da ake kokwanton
ingancin ta sai a samu tafasasshen mai a
zuba shinkafar a ciki. Idan har ta roba ce to
za kuga ta fara narkewa sannan kuma tana
hadewa da juna.
Idan har hakan ta faru, sai
a kiyaye, shinkafar ta bogi ce.

Tuesday, 15 November 2016

WhatsApp expiration on BB phones shifted to June 2017

The initial date set by WhatsApp for the
expiration of its application on certain
phones like the Blackberry OS at the end of
2016 has been shifted.
Vanguard reports that the new date for the
expiration of the usage of the app has now
been moved to June 2017 as the users of
the phone now have more time to enjoy the
service on their mobile devices.
It was gathered that when this
announcement was made, a lot of people
had started swapping their phones and even
some decided to sell them while the sales of
the phones dropped significantly in the
market.
Observers are now saying this new decision
to extend the expiry date of this application
from the BB OS phones may be as a result
of the latest video calling addition to
WhatsApp announced by mark Zuckerberg,
founder of popular social media site,
Facebook.
Individuals with the phones using the
Operating System now have the privilege of
enjoying the service until the middle of June,
2017.

Monday, 14 November 2016

2016 za ta kasance mafi zafi a tarihi

Shekara ta 2016 za ta kasance shekara mafi
zafi a duniya tun lokacin da aka fara adana
bayanai kan yanayi, kamar yadda hukumar kula
da yanayi ta duniya ta sanar.
Hukumar kula da yanayi ta duniya ce ta ba da
sanarwar a wajen wani taron duniya kan yanayi
da ake yi a Morocco.
Wakilai a wajen taron na duba yadda zaben
Donald Trump a matsayin shugaban Amurka zai
shafi yarjejeniya kan dumamar yanayin duniya da
aka cimma a Paris a bara.
Sai dai kuma wakilin Amurka na musamman a
wajen taron, Jonathan Pershing, ya ce Amurka
za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar Paris din,
duk da sauyin gwamnatin da aka samu.
Mr Trump ya taba bayyana sauyin yanayi a
matsayin wani abu da babu gaskiya a cikinsa,
wanda China ta kirkira domin lalata
masana'antun Amurka.

Tuesday, 8 November 2016

Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (1)

Matashiya
Idan masu karatu ba su manta ba, a baya mun
fara bayani kan tekunan duniya da irin abubuwan
da ke cikinsu (ko karkashinsu), inda muka yi
bayani kan tekun Pacific, wanda shi ne babba,
mafi fadi da girma a duniya. Bayan tekun Pacific
mun fara bayanai kan teku na biyu da ke biye da
shi, wato tekun Atlantika, ko “Tekun Legas,”
kamar yadda muka saba kiransu a Najeriya. A
karkashin wannan gaba dai mun gabatar da
kasidu guda biyu.
Na farko kan asali da samuwar tekun Atlantika,
inda muka duba bangaren tarihi da kuma bagiren
da wannan teku yake a duniya. Sannan a karshe
muka sanar da mai karatu cewa Turawa sun
dade suna gudanar da bincike na kimiyya kan
sha’anin teku a wannan bagire tun sama da
shekaru dari da suka gabata. A kasida ta biyu
kuma mun jero bayanai ne kan tarihin tafiye-
tafiyen bude ido da burgewa da Turawa suka yi
ta yi, har zuwa wannan karni da muke ciki. A
yau cikin yardar Allah, ga shi mun dawo don ci
gaba da bayani kan tekun Atlantika. Za kuma mu
dubi tasirin wannan teku ne wajen ci gaban
tattalin arzikin kasashen duniya da kuma
sadarwa.
Tasiri Wajen Tattalin Arzikin kasa
Kamar yadda bayanai suka gabata, tekun
Atlantika babban teku ne. Shi ne na biyu a
duniya, sannan ya hada alaka tsakanin manyan
nahiyoyin duniya guda uku; nahiyar Amurka
(Kudanci da Yammaci) ta bangaren
yammacinsa. Sai nahiyar Afirka daga bangaren
Arewaci. Nahiyar Afirka na daga cikin nahiyoyin
da suka fi yawan jama’a a duniya. Sai kuma
nahiyar Asiya ta gabashinsa, inda ya jonu da
tekun Indiya (Bahar Maliya) daga gabas, ya
nausa can don hadewa da shi.
Wannan gamayyar manyan nahiyoyin duniya da
tekun Atlantika ya hada ya taimaka wajen
saukake hanyoyin kasuwanci a tsakanin
kasashen duniya. Tekun Atlantika wani babban
titi ne na kasuwanci, inda manyan jiragen ruwa
ke dauko dukiyoyin kasuwanci da hajoji nau’uka
daban-daban daga nahiyar Amurka zuwa Afirka.
Haka ma sukan dauko kayayyaki daga nahiyar
Amurka zuwa nahiyar Asiya, kai tsaye ko ta
hanyar yin Zango a nahiyar Afirka. Bayan
wannan, har wa yau jiragen kasuwanci kan taso
daga nahiyar Amurkan dai zuwa nahiyar Turai;
musamman masu tasowa daga bangaren Latin
Amerika (Kudancin Amurka - South America).
A daya bangaren kuma, jiragen ruwan kasuwanci
kan nausa daga nahiyar Afirka zuwa nahiyar
Asiya, daga can kusa karasa Turai, ta hanyar
maliya da ke sada su da tekun Pacific. A wasu
lokuta kuma akwai masu tashi daga Afirka zuwa
nahiyar Amurka kai tsaye, don kaiwa da daukowa
ko kaiwa da dawowa; ya danganci abin da ya
sawwaka.
Wannan jele da jiragen ruwan kasuwanci ke yi
tsakanin wadannan nahiyoyin duniya ta cikin
tekun Atlantika ya taimaka gaya wajen habaka
dangantakar kasuwanci tsakanin ma’abota
wadannan wurare. Wannan kuma, a Turance, shi
ake kira: “Transatlantic Trade,” a zamanin yau.
Akwai tashoshin jiragen ruwa a dukkan kasashen
da ke gaba da wannan teku a duniya baki daya;
tsakanin Afirka, da Asiya, da kuma nahiyar
Amurka.
A karkashin wannan teku mai albarka, akwai tarin
albarkatun kasa irin su Man Fetur da ke makare
cikin curarrun duwatsun da ke karkashin tekun.
Akwai sinadaran Gas, da duwatsun gini da kuma
duwatsun alfarma a jibge a karkashin wannan
muhalli. Bayan wadannan, an gano tarin
duwatsun zinare a nisan zurfin da bai shige mil
daya ba, a karkashin tekun. Bincike ya nuna
cewa, gano hanyoyin zakulo wadannan duwatsun
zinare a halin yanzu ba abu ba ne mai sauki, idan
an yi la’akari da yanayin muhallin. Sai dai nan
gaba.
Bayan haka, tekun Atlantika ne ke dauke da
albarkatun kifi mafi girma a duniya; fiye da tekun
Pacific ma. Wuraren da suka fi kowane tarin
wannan nau’in albarkar kifaye su ne: bakin
tsibirin Newfoundland da Dogger Bank da ke
kasar Scotland, sai Georges Bank na kasar
Amurka, da kuma tsibirin Bahamas.
Tasiri Wajen Sadarwa
Masu karatu za su yi mamakin jin cewa tekun
Atlantika wata matattara ce da ke dauke da
hanyoyin sadarwa. Kusan dukkan manyan
kamfanonin sadarwa na duniya, da gidajen yanar
sadarwa na duniya, da gwamnatocin kasashe
daban-daban (ta hanyar kamfanoni
hukumominsu), sun binne wayoyin sadarwa
nau’in “Fiber Optics,” wanda hadakar waya ce,
amma a yanayin gilashi, mai daukar siginar
bayanan sadarwa na zamani cikin mafi saurin
yanayi da girma.
A halin yanzu an kiyasta cewa, kashi 95 cikin 100
na a kalla na hanyoyin sadarwa na zamani suna
amfani ne da wayoyin sadarwa na “Fiber Optics”
ta karkashin teku, don aiwatar da sadarwa. A
yayin da ragowar ke amfani da tsarin sadarwa ta
wayar-iska (Wireless). Wannan ya faru ne
saboda ingancinsa da kuma sauri wajen aikawa
da sakonnin bayanai na zamani. A yayin tsarin
hanyar aikawa da sakonni ta wayar-iska ke
daukar mizanin bayanai biliyan daya cikin dakika
guda (1GB per second), tsarin aikawa da sakonni
ta wayar “Fiber Optics” na daukar mizani tiriliyon
daya ne a duk dakika guda (1Terabyte per
second). Wacce alakar ce wannan da tekun
Atlantika?
Alakar ta samo asali ne saboda mahalli. Ma’ana,
kusan dukkan madaukan wadannan bayanai suna
biyowa ta cikin wasu wayoyi na sadarwa da aka
shimfide su a karkashin tekunan duniya, ciki har
da tekun Atlantika. Sai dai ba yau abin ya fara
ba.
Yunkurin farko da aka fara yi wajen shimfide
wayoyin sadarwa a karkashin teku dai ya faro ne
tun cikin shekarar 1850s. Malaman tarihi suka
ce a lokacin ne aka fara shimfida wayoyi masu
dauke da siginar sadarwa don amfani da na’urar
“Telegraph.” Hakan ne ya saukake tare da bayar
da damar karba da iya aika sakonni tsakanin
nahiyoyin duniya masu dauke da wannan na’ura.
Duk da cewa a lokacin kusan kasashen
yammacin duniya ne kadai ke mallakar wannan
na’ura ta “Telegraph,” to amma ganin cewa suna
mulkin mallaka a lokacin, kuma hukumominsu sun
yadu tsakanin tsakiya zuwa gabashin duniya da
kuma nahiyar Afirka, sai suka yi wannan kokari
don samun damar aikawa da sakonni cikin
gaggawa daga kasashensu zuwa inda suke
mulkin mallaka ko akasin hakan.
Sai yunkuri na biyu, wanda ya samu bayan
gushewar na’urar “Telegraph,” sanadiyyar
samuwar na’urar wayar tangaraho. Shi ma ya
haddasa shimfide wayoyin sadarwa masu dauke
da siginar rediyo don daukar murya daga wata
nahiya zuwa wata. Daidai wannan lokaci dai
duniyar ta fara gamewa a fannin sadarwa,
sanadiyyar yaduwar wayoyin tangaraho irin na
zaman baya (Analog).

Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (2)

Marhala ta uku ta samu ne sanadiyyar
bayyana da yaduwar hanyoyi da na’urorin
sadarwa na zamani. Wannan, kamar sauran
dalilan baya, shi ma ya haifar da samuwar
kasashe da manyan kamfanonin sadarwa na
duniya wajen bisne manyan wayoyin sadarwa na
zamani masu suna “Fiber Optics,” don samar da
tsarin sadarwa mai inganci tsakanin nahiyoyin
duniya baki daya.
Wadannan wayoyi, sabanin wadanda suka gabace
su, suna iya taskance rubutattun bayanai ne, da
sauti/murya, da hoto mai motsi, da hoto mara
motsi, tare da bayanansu (Metadata), daga asali
zuwa tikewarsu (daga inda aka aika su zuwa
inda za a karbe su). Dukkan tekunan duniya a
makare suke da ire-iren wadannan nau’ukan
wayoyin sadarwa da ake bisnewa don jona
sauran bangarorin duniya da bayanai.
A bangaren tekun Atlantika ma haka lamarin
yake. Cikin shekarar 1920 aka fara yunkurin
bisne wayoyin sadarwa a karkashin wannan teku,
amma sai abin bai cinma nasara ba. Hakan ya
faru ne sanadiyyar rashin ingantacciyar fasahar
da za ta iya sawwake aikin, da kuma matsalar
tattalin arzikin kasa da duniya ta samu kanta
cikin shekarar 1930, wato: “Great Depression.”
Wannan ya sa sai cikin shekarar 1942 tukun
hakan ya yiwu.
Kamfanin “Siemens Brothers” mai reshe a birnin
Landan, ta hadin gwiwa da hukumar Burtaniya
mai suna: “British National Physical Laboratory,”
suka fara shimfida bututu a karkashin tekun
Atlantika. Sun yi haka ne don samar da bututun
mai na karkashin, wanda shi ne na farko a duniya
baki daya. Hakan ya faru ne a daidai lokacin
Yakin Duniya na II (tsakanin 1940 zuwa 1945
kenan).
Bayan kamfanin “Siemens” sai “Transatlantic-1”,
wanda shi ne kamfanin farko da ya fara bisne
wayoyin sadarwa na tarho a karkashin tekun
Atlantika. Kada a mance, kamfanin “Siemens” ya
bisne bututun mai ne, wanda shi ne na farko a
wannan bangare. Amma a babin sadarwa,
kamfanin “TAT-1” kamar yadda aka saba kiransa
a gajarce, shi ne na farko. Ya yi wannan aiki ne
tsakanin shekarun 1955 zuwa 1956, a daidai
gabar tsibirin Gallanach da ke kasar Scotland, da
gabar tsibirin Clanrebille dake Newfoundland a
kasar Kanada. Wadannan wayoyi na aika
bayanan murya ne da sauti, kuma suna dauke ne
da tashoshin tarho guda 36.
Haka lamarin ya ci gaba har zuwa lokacin da
fasahar Intanet ta bayyana, aka samu ci gaba a
fannin kere-keren lantarki. A daidai wannan
lokaci ne, sanadiyyar habbakar kimiyya da
fasahar sadarwa, bukata ta karu kan ingancin
tsarin sadarwa. Wannan ya samar da nau’ukan
na’urorin safaran bayanai daban-daban, ciki har
da wayoyin kebul nau’in “Fiber Optics.” Idan mai
karatu bai mance ba, a shekarar 2010 ko kasa da
haka kadan ne muka gabatar da kasidu wajen
hudu kan wannan fasaha, masu take: “Fasahar
Fiber Optics.”
Wannan fasaha ta wayoyin sadarwa nau’in waya
ce da aka kera ta daga damammen kunun
gilasai, aka daskarar da ita, sannan aka yanka ta
sille-sille. Babbar manufar hakan kuwa shi ne
don tabbtar da inganci wajen sadarwa da yawa
ko girman mizanin sakonnin da ake son wannan
fasaha ta rika dauka yayin aikawa da sakonni.
Idan mai karatu na son ya gane hakan, ya dauki
gilashi mai dan tsawo, a cikin duhu, ya haska
tocila daga farkonsa zuwa karshe; idan har ya
iya tantance tsawon lokacin da hasken ya dauka
tsakanin lokacin haskawa da isan hasken zuwa
karshen gilashin, to, wannan ita ce tazarar da za
ta dauka idan aka cillo siginar bayanan sadarwa
daga asali zuwa muntaha.
Kusan dukkan kamfanonin sadarwa na zamani
suna da manyan wayoyin sadarwa da suka bisne
a karkashin tekunan duniya, ciki har da tekun
Atlantika. Wannan gasa ce suke yi a tsakaninsu.
Kamfanin Yahoo!, da Microsoft, da Google, da
AT&T, da berizon da sauransu, duk suna da
wannan tsari.
Matsaloli
Babbar matsalar da ire-iren wadannan tsare-tsare
ke fuskanta, duk da ingancinsu wajen sadarwa da
samar da fa’ida ta kasuwanci, shi ne irin
hadarurrukan dake samuwa a tekun; ya Allah a
karkashi ne ko a saman tekun, wanda ke
gangarawa zuwa inda wadannan wayoyi suke.
Wadannan hadarurruka dai sun hada da girgizan
kasa da aman dutse da ake samu a karkashin
teku, wato: “Earthkuarke and bolcanic
Eruption.” Samuwar wannan yanayi na
sanadiyyar konewa ko yayyankewar wadannan
wayoyi. Sai kuma matsalar rubewa da
sanadiyyar tsawon zamani, musamman ga
wadanda aka binne su da jimawa.
Bayan haka, akwai matsalar dabbobin ruwa,
wadanda ke kokarin yagalgala wadannan wayoyi,
ko ta hanyar ci ko sarkafe jikinsu da su. Ba da
dadewa ba kamfanin Google ya sanar da cewa
lallai ya gano cewa manyan kifayen karkashin
teku (Sharks/Whales) na guiguyar wayoyinsa da
ya shimfide a karkashin tekun. Wannan, a
cewarsa, ba karamin hatsari bane ga bayanan da
wadannan wayoyi ke dauke da su. Amma ya
tabbatar da cewa ya samar da wata sabuwar
fasaha ta nau’in waya mai suna: “Kelbar,” wacce
ke da inganci, mai jure matsaloli irin wannan.
Wannan fasaha ta “Kelbar” dai nau’in waya ce
amma mai kama da tayar mota, wato wajen
dabi’a kenan, ba wai siffa ba.
Wannan, a takaice, na cikin gudunmawar tekun
Atlantika ga tattalin arzikin duniya da fannin
sadarwa, musamman nahiyoyin dake
makwabtaka da shi.

Friday, 28 October 2016

Facebook ya bude wani sabon dandali

Kamfanin sadarwa na Facebook ya bude wani
sabon dandali, wanda zai bai wa wasu
kamfanoni damar kafa tasu manhajar, domin
kasuwanci.
Manhajar, wadda ke kama da ta Facebook, na
dauke da na'urorin daukar bidiyo da tura
sakwanni.
Sai dai kuma ba a hade suke wuri guda da
sashen da ke nuna sunan mutum da wasu
abubuwa na kashin kansa ba.
An tsara manhajar ne domin ta maye gurbin
wasu manhajojin da ake amfani wajen kasuwanci
kamar manhajar tura sakwannin email.
Wani mai sharhi dai ya ce wannan sabon dandali
zai fuskanci kalubale daga sauran kamfanoni
irinsa da suke gogayya da shi.
Za a sa manhajar a kasuwa domin gogayya da
wasu manhajojin kamar Yammer ta Microsoft,
masu hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin sada
zumunta.
Da kuma manhajar Slack, wadda ake amfani da
ita wajen tura sakwanni.
Wani jami'i a Lewis Consultancy ya ce "Ba wai
samar da hanyoyin kasuwanci ta sada zumunta
ba ne kadai, zai ba su damar gogawa da wasu
manhajojin kamar Google Cloud."
Ana dai amfani da Google Cloud ne wajen
musaya da gyara bayanai.
Ya kuma kara da cewa, "Zai ratsa wurare da
dama a matsayin abu muhimmi guda daya."

Wednesday, 12 October 2016

YADDA AKE TRANSFER DIN CREADIT NA DUK LAYUKAN NIGERIA

GLO ZUWA GLO kafin kayi transfer din creadit a layinka na glo, to dolene sai kayi activate din tsarin GLO ME2U,Domin wannan tsari na GLO ME2U, kawai aika sako 'ACT' zuwaga 131, in ya tafi bayan wani dan lokaci zasu dawoma da message cewa "create change your password/PIN for securtiy purposes." Yadda ake canza ko kirkiran pin ko pasword, Dial *132*00000*New password*New password# saikayi send. Misali *132*00000*1234 * 1234# saikayi send. 1234, zasu dawoma da sabon pin dinka Amma pin dinka zaikasance guda hudu ne kawai misali 6654, 3534. Yadda ake transfer *131*recipient' s phone number*Amount*p in# send. misali : *132*705635443* 100* 1234# send. Amma dole ne wanda zaka turama ma credit yakasance ya fara da 8, na 080 ko 7, na 070, misali i.e 705876097 ko 805547568. Da zarar ya tafi zasu turoma message kamar haka"To confirm by pressing 1, To proceed press 1, to cancel the transaction press 2. ¤YADDA AKE TRANSFER NA MTN Dafarko dai anaso kayi creating ko changer pin, sudai wadannan pin din guda hudu ne (4) ¤YADDA AKE CHANGER DEFULT PIN Tura sako 0000 1234 1234 zuwa 777, 0000 shine Default Pin 1234 kuma New Pin 1234 shima New Pin ka canza pin kenan. zaka iya canza 1234 ga duk Numban da kakeso, zasu dawoma da message kamarhaka"your pin has been changed successfully." inkuma ta shortcut zakachangers ga yadda zakayi, Dial *601*old/ default PIN*New PIN*New PIN# then press Send/Ok. Misali-: inkana son canza (0000) zuwa 7890,saika danna *601*0000*7890* 1985 # saika danna Send/OK. Inkagama zasuma message kamar haka"successful change." ¤YADDA AKE TRANSFER DIN MTN , Ta SMS. Transfer 081381597 100 1234 saika tura zuwa ga 777. inya tafi zasuma message kamar haka "to confirm your request by replying YES" idan kayi confirnm zasu kasama message kamar haka "your credit will be transferred from your phone to the other subscriber." inkuma ta dialling ne danna *600*Recipient? s phone number*amount in Naira*PIN# saikadanna Send/ Ok. misali *600*0703xxxxxx x* 100* 1234# saika danna Send/OK. Zasuma message kamar haka "successful transfers." AIRTEL ZUWA AIRTEL su airtel kawai zaka tura ta message (2U (space) Recipient's phone number (space) Amount (space) Pin. Zuwaga 432. Misali 2U 0812564539 100 1234 to 432. ¤ETISALAT ZUWA ETISALAT kawai danna *223*Pin*Amount * Phone Number# sent. Amma dole sai kanada naira #10 Tranfer zaitafi .

YADDA AKE GYARA SIM IDAN BAYA TURA SAKO MESSAGE

Wani lokacin zakuga kana bukatar tura message amma da xarar ka rubuta sakon kanaso ka sender saikaga yaki tafiya yacema message not sent kayi kayi amma ka kasa gano wannan matsalar karshe saide ka hakura to Dalilin Dayake Sa Layi Yadaina Tura Message Shine Akwai Wasu Lambobi Wanda Ake Kiran su to wannan numbobin Sune Suke Gogewa dan Haka duk Lokacinda kaga Layinka Yadaina Tura Message to Dinkane ta goge. Ga YADDA ZAKA GYARA MESSAGE CENTER DINKI.. Kawai kashiga Menu na wayarka Saika Shiga <>More>>Message setting>>Text Message>>Message center bayan Ka shiga Nan Zakaga akwati guda biyu 1. Message center name 2.message Center Number To Ga yadda ake saita Nakowane Layi. MTN Message Centre Name (MTN) Message center Number: +234803000000 Etisalat Message Centre Name (ETISALAT) Message Center number: +2348090001518 Airtel Message Centre Name (AIRTEL) Message Center Number: +2348020000009 Glo Message Centre Name (GLO) Message Center Number br /> +2348050001501 Shikkenan Kana sakawa Dakayi Save Ka Magance Matsalarka Ta Message Insha Allah. Allah ya bada sa,a

Friday, 2 September 2016

GOOGLE ALLO SABON CHATTING DA YAFI WATSAPP


dan ba'a manta ba, kamfanin google a kwanakin baya sun fitar da wani application mai suna Google Duo wanda yake zama wata kafa ta sadarwar hoton video (video chat).

Google sun kara fitar da sanarwar cewa sabon chatting app dinsu da suka yiwa lakabi da google allo na nan zuwa nan bada jimawa ba, inda zaizo da sabbin abubuwa da mafi yawa daga cikin chatting apps basu dasu.



Google dai kamar sauran chatting apps yana da features na tura sakon text , hotuna , hotunan yanayi (emojis) , videos , sautin murya da sauran sautuka, files dadai sauran makamantan abubuwan da sauran chatting apps ka iya.

Nasan a haka wasu zasu ce ai babu bambanci tsakaninshi da sauran apps tunda duk a cikin abubuwan da na.zayyano a sama babu wani bakon abu. To kwantar da hankalinka in bayyana maka abinda ya bambance shi daga sauran chatting apps.

Ba kamar sauran apps ba, google allo yana dauke da google search a cikinsa wanda zaka yi ba tare da ka bar cikin app din ba. Sannan kuma akwai search na murya(voice search) a yayin da kake jin gandar yin rubutu. Haka zalika app din na dauke da tsarin auto reply da zai kawo maka reply da yake tsammani a zuciyarka wanda kai kuma zaka bashi damar tunawa in yayi daidai da abinda kake so.

Dadin dadawa, google allo zaizo da tsari da zai baka damar tattaunawa da google bot yayin da kake chat wanda hakan zai kara baka damar more wasu karin abubuwan.

Ya zuwa yanzu dai shi wannan sabon application bai iso ba tukun amma zaka iya zuwa playstore kai search dinshi domin kayi pre-register da zai sanar da kai da zarar an saki wannan application din.

SEPTEMBER 2016: CHEAPEST DATA PLANS FOR ALL NETWORKS

Good day our loyal blog visitors, i will in this post present to you the cheapest data plans, price, validity and subscription code of all or best performing networks as far as internet browsing is concern in Nigeria in this September 2016.



Some might still due to the current economic situation of recession find it not as cheap as they are expecting, but fact to be told, what i am about to state later in this post reflects the cheapest data plans our telecom networks could afford.

MTN 
Despite the rain of complaints about their slow network in some areas, especially the local areas, MTN Nigeria have to be commended for their efforts in providing cheap data packages for their customers. Below are some of the data plans offered by MTN Nigeria:

√ MTN 7.5GB ; 1.5GB week days and the remaining 6GB to work on week ends only. Validity of this package is one month and it costs only N1000. To subscribe dial *131*106#.

√ MTN 17.5GB ; 14GB working on weekends and 3.5GB working on week days. Validity of this pack is 1 month and it costs N2000. To buy this plan simply dial *131*110#.

√ MTN 1GB for N500 (deal zone) for MTN pulse subscribers . you can opt in for this offer by dialing *406# ,you then reply with option 2.

√ MTN 750MB - Send 103 to 131 . It is valid for one month too.

√ MTN 500MB NIGHT PLAN for N25 (for MTN pulse subscribers only) - simply send Night to 131.

• For more MTN data packages dial *131# and follow the instructions on the screen.

• To check your data balance you dial *131# and choose from the menu or you simply send 2 to 131.

AIRTEL 
After MTN data plans, now comes the airtel data packages which are also seen at the forefront in providing cheap and affordable data plans for Nigerians. Airtel were believed to be having a robust and outstanding intetnet network in local areas, that means it is mostly used in rural areas.

√ AIRTEL 1.5GB for N1000 works on all devices and it is valid for 1 month. To subscribe dial *496#.

√ AIRTEL 750MB , it costs N500 and is valid for two weeks time(14 days) unlike that of MTN which has its validity as 1 Month. To subscribe to this data plan, you simply dial *418#

Airtel Night plan packages

- 1 Hour unlimited plan for N100 . Dial *481*1# to opt in 

3 Hours unlimited plan which goes for N300 *481*2# to opt in for this plan

To check your data balance on airtel you dial *123*10# or *140#

ETISALAT 
Etisalat is considered to be the fastest network in the field of internet browsing especially in cities and some other urban areas. See the slots below:

- 200MB for N200 you dial *229*2*10# . It is valid for 1 week(7days).

-1.5GB for N1000, dial *229*2*7# this is valid for one month.

- 3.5GB for N2,000 dial *229*2*8# valid for one month.

- 5GB for N6,500 dial *229*2*3# - 1 month validity.

- 8GB for N8000 dial *229*2*5# 1 month.

- 10GB for N10,000 dial *229*2*5# valid for one month..

• To check your etisalat's data plan you dial *228#.

GLO DATA PLANS
Glo network is considered to be the best interms of bigger data allowance at a very cheap rate. Without long story, below are the slots:

• N1000 = 2GB substantial for 30 days

• N2000 = 6GB substantial for 30 days

•N2500 = 10GB legitimate for 30 days

•N3000 = 12GB legitimate for 30 days

•N4000 = 18GB legitimate for 30 days

•N5000 = 24GB legitimate for 30 days

•N8000 = 48GB legitimate for 30 days

You can easily subscribe to any of the above data plan by dialing *777# and then follow the instructions on that menu.

That's all i can offer about the cheapest and affordable data plans by major telecom networks operating in Nigeria. Share with your friends as this little info might be of service to someone.

Thursday, 11 August 2016

YADDA ZAKA CIRE SECURIYT AWAYAR CHINA KAMARSU JAVA PHONE

Barkan mu da war haka yau nazo mana da wani gajeren bayani akan wayoyin china Idan kana da original tecno java phone kuma ka sa mat security ka manta ga mafita mai sauki. akwai masu amfani da china tecno mobile phone wato (java). Sauda yawa mutun ya kan iya saka security code a wayarsa kuma ya manta da wane irin code yayi amfani ko kuma garen ta6eta6ensa ko yara su saka ma sa security kuma bai san security dinba, to kwantar da hankalinka ga yadda zakayi. Yana da sauki sosai kawai ba ka sani bane!! Amma yau kam zakasan mafita kawai abin da zakayi ka latsa a lamar*#12345#zai nuna maka wani rubutu kamar haka [color- blue]DO YOU WANT TO DELETE ALL DATA[/ color] wani kuma zai baka rubutu makamancin haka. Sannan zai nuna maka alamar YES da NO kawai saika latsa Yes daga nan wayar zai kashe kansa sanna ya bude kansa. Shikenan ka gama komai wayarka zata dawo kamar sabuwa. Allah yasa akiyaye