Showing posts with label LABARAN DUNIYA. Show all posts
Showing posts with label LABARAN DUNIYA. Show all posts

Friday, 17 May 2019

Dalilin Da Ya Sa Muka Ajiye Mukamanmu A Gwamnatin Ganduje, Cewar Su Malam Aminu Daurawa

Wasu manyan malaman addinin musulunci a Kano da suka hada da Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Shaikh Abba Adam Koki, shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano da Dr Muhammad Nazifi Inuwa da kuma Malam Abubakar Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje.
Wata sanarwa da malaman suka sanya wa hannun ta bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda ayyukan da suke gabansu.
Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da shi ta waya, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun fita daga gwannatin ne saboda sun ga ba a bukatar aikinsu.
Shi kuwa a cikin takardar da ya mika ta murabus dinsa Shaikh Abba Adam Koki ya ce ya ajiye aikin ne saboda dalilan rashin lafiya.
Shaikh Daurawa dai shi ne babban kwamandan Hisbah ta jihar Kano, shi kuma Shaikh Abba Koki shi ne shugaban hukumar alhazai ta jihar.
Malam Nazifi Inuwa ya rike mukamin kwamishina na biyu a hukumar Zakka ta jihar Kano, yayin da shi kuma Malam Abubakar Kandahar ya rike mukamin kwamishinan shari'a na daya na jihar ta Kano.
Dangantaka tsakanin gwamnan na Ganduje da wasu daga cikin malaman ta jima da yin da tsami, inda ake zaune ta ciki-na-ciki.
Murabus din malaman na zuwa ne kasa da mako daya bayan gwmanan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai wasu bara-gurbi a hukumar Hisbah.
Yayin da yake jawabi a wajen taron auren zawarawa da aka gudanar a makon farko na wajen Mayu, gwamnan ya ce ana muna-muna da cuwa-cuwa a hukumar Hisbah, abin da ya ce dole ne a tsaftace hukumar.
Dangantakar ta kara yin tsami ana daf da zaben gwamna, bayan da wani bidiyo da aka watsa ta kafofin sada zumunta ya nuna wasu malaman da ke rike da mukamin gwamnati sun kai ziyarar goyon baya ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar PDP.
Kwankwaso shi ne babban abokin hamayyar gwamna Ganduje, duk da cewa ba shi ya nemi takarar gwamnan ba.
Mafi yawan malaman da suka ajiye aikin dai tsohon gwamna Kwankwaso ne ya nada su a mukaman, yayin da shi kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da aiki da su bayan ya zama gwamna a 2015.

Gaskiyar Abun Da Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Ya Fada

Gaskiyar Abun Da Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Ya Fada
Daga Anas Saminu Ja'en
Sheikh Dr. Isa Ali Pantami Malam yana magana ne akan yin imani ga Allah Ta'ala kuma ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake gudanar da Tafsir a ranar 4 ga watan Ramadan a masallacin Annoor Masjeed Wuse ll a Abuja, Malam ya ce hakikanin nagarta shi ne "Man'ama Billahi" wanda yai imani da Allah Ta'ala duk abun da yake daga wajan Allah ka gasgatashi kar ka tsaya kana tinanin ya yi ko bai yi ba.
1- ka yi imani cewa Allah Ta'ala akwai shi.
2- Allah shi ya halitta shi ya mallaka kuma shi yake jijjuyawa.
3- Shi kadai ya dace a bautawa.
4- kai imani da sunayen sa da siffofin sa, ilimin Allah ya fi karfin hankalin ka ya fi karfin hankali na.
Malam ya ce duk abun da Allah ya yi ka yadda akwai hikima a ciki wannan jahilci ne wasu lokacin hatta ga masu mulki ina tuna shekaru kamar bakwai 7 da suka wuce a arewacin kasar nan daga cikin mafi fuskoki da tasiri, akwai wanda ya sha giyar mulki ya ce shi ya rasa me yasa Allah ya halacci Sauro ne.
Har Malam yake cewa wai shi a matsayin sa ba Injiniya ya gama tinanin sa bai sai me yasa Allah ya yi wannan ba, yanzu akwai imani a wannan wajan mutum ya ce wai bai san me yasa Allah ya yi wata halitta ba a cikin halittu wai ya gama tinani, saboda wani lokacin jahilci ba abun da baya sawa. akwai mai mulkin da ya tsaya ya ce Annabi S.W.T akwai wanda ya tsaya ya ce Allah S.A.W akwai wanda ya ce zamanin Annabi Buhari in ba haka ba a ce mutum yana shugabantar al'ummar musulmai ya na Challenging kudira da ikon Allah Ta'ala inda addini da sanin addini wannan ma ai ba mutane bane, wannan bai da ce ko wankin bandakin masallaci a basu ba indai da ilimi ake abu But haka aka tsinci kai a ciki Allah Ta'ala ya karemu daga jahilci Allah ya kare mu daga jahilai da kuma aikin jahilci
Wannan shi ne abun da Malam ya fada Allah ya sakamasa da mafificin alkairi, duk wanda bai yi imani da Allah ba shi ne zai ja da ikon Allah da abun da Allah Ta'ala ya halitta duk musulmin kwarai yasan haka.
Amman saboda kin Allah da siyasar jahilci ta wannan zamani da wasu ke yi suna ta yada cewar Dr. Isa Ali Pantami wai ya zagi Kwankwaso kaf a karatun babu inda ya kama sunan kwankwaso ballantana ya zage sh, idan kuma akwai wanda ya ji ya anbaci sunan sai ya sanar da mu musamman yaran kwankwaso wadanda ba bu mutum mai daraja da kima a idanun su kaf fadin duniya kowa suka ga dama sai su zage shi su ci mutuncin sa wannan kuskure ne babba a rayuwa wallahi, idan kuma shi kwankwaso shi ne ya yi wancan furucin na cewar bai sai me yasa Allah ya yi Sauro ba sai ku fada mana? A cikin masu zagi da cin mutuncin Malam idan kuma akwai wanda yake da ja akan hakan? To ya taimaka ya kawo mana Video ko Audio, dan Allah mu daina yada jita-jita domin ni a yanzu haka ina da Audio din kuma duk wanda ya kawo wallahi wallahi wallahi akwai kyauta mai tsoka.

Thursday, 11 April 2019

ALIKO DANGOTE: 'YADDA ZA KA ZAMA KAMAR NI'

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote ya bai wa matasan nahiyar shawarwari idan suna son zama kamarsa.
Hamshakin attajirin ya bayyana hakan ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da attajirin nan dan kasar Sudan Mo Ibrahim a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa karshen makon jiya.
Wani mahalarcin taron ya tambayi attajirin wadanne bangarori zai fi mayar da hankali idan a ce yana a matsayin dan shekara 21 da haihuwa kuma yana shirin fara kasuwanci.
Dangote ya ce zai fi mayar da hankali ne a harkarkokin sadarwa na zamani da kuma aikin gona.
"Wadannan ne bangarori biyu da za su fi kawo riba," in ji shi.
Sai dai daga nan ya ja kunnen matasa game da dabi'unsu bayan fara kasuwanci musamman 'yan Afirka.
Ya ce muna "kashe ribar da ba ta kai ga zuwa hannunmu ba."
"Da zarar ka fara kasuwanci kuma kasuwancin ya fara samun ci gaba, maimakon ka yi ta kara uwar kudin, sai mutum ya fara kashe kudin da tunanin ribar za ta ci gaba da zuwa," kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa:"Dole ne mutum ya natsu saboda akwai kalubale nan da can."
Attajirin ya ce bai kamata mutum ya fara kashe kudi ba ba-ji-ba-gani ba.
"Saboda idan ka sayi manyan abubuwan more rayuwa (kamar motocin kawa) za su dauke maka hankali daga harkokin kasuwancinka."
Daga nan, ya bayar da misali da kansa, inda ya ce "ba ni da wani gidan shakatawa mallakina a ko ina a fadin duniya."
"Amma akwai wasu daga cikin ma'aikatana da suke da gidan shakatawa a birnin Landan."
'Najeriya za ta zama kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur'
Dangote ya ce aikin gina matatar man da yake yi a jihar Legas a Najeriya zai ci kimanin dala biliyan 12 zuwa 13.
Ya ce idan aka kammala gininta za ta rika samar da gangan mai 650,000 a kowace rana.
Har wa yau, ya ce idan aka kammala aikinta, hakan zai mayar da Najeriya kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur a yankin kudu da saharar Afirka.
"Babban kalubalen da muka fuskanta lokacin fara gina matatar mai shi ne sai da muka gina tashar jirgin ruwa ta musamman saboda babu wata tashar jirgin ruwa a kasar da za mu iya shigo da manyan na'urorinmu ta ita."
A bangaren siminti, Dangote ya ce a bana Najeriya za ta kasance kasar da ta fi kowacce fitar da shi a nahiyar Afirka.
BBChausa.

Wednesday, 19 April 2017

NEWS: KAMFANIN FACEBOOK SUN KULLE SHAFUKAN MUTANE 30,000

A cikin yukurin su na dakile yada labaran karya marasa tushe, kamfanin zumunta na yanar gizo Facebook, sun rufe shafufukan mutane sama da dubu 30,000 a kasar France.
Kamfanin mai mazauni a karamar hukumar Silicon Valley, dake jihar Califonia ta Amurka, suna kokarin ganin sun taimaka wajen ganin an yaki wannan matsalar, duk dai da cewar gwamnatocin kasashen turai na adawa da yunkurin kamfanin.
Mafi akasarin manyan kamfanonin yanar gizo, kamar su Twitter, YouTube, da facebook, suna fuskantar matsanancin bincike a yankin kasashen Turai, don ganin ba’ayi amfani da shafufukan su wajen yada ta’addanci a duniya.
A ‘yan watanni masu zuwa ne, za’a gabatar da zabe a kasashen France da Germany, don haka ana gargadin kamfanonin da su kokarta wajen ganin basu bada wata dama ba, wajen aika sakonnin da basu da asali.
Su bada tasu gudun mawa, wajen ganin ba’a yada duk wani labari da bashi da tushe ba, koda kuwa ya kankantar shi yake, haka duk wani shafi da bashi da kwararan bayanai, to su tabbatar sun kulle shi.
© Dandalinvoa.

Monday, 3 April 2017

Za a fuskanci wahalar man fetur a Nigeria — NUPENG

A ranar Litinin ce direbobin manyan motocin dakon man fetur za su fara yajin aiki a Najeriya.
Kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG, ta ce za tu shiga yajin aikin ne saboda karancin albashi da lalatattun titunan kasar da suke bata musu motoci.
Wani mai magana da yawun kungiyar Cogent Ojobo, ya yi gargadin cewa za a fuskanci wahalar karancin man fetur da dizal da kananzir a kasar, saboda za su dakatar da rarraba su.
Ya kuma ce ba a saka ranar da ake zaton daina yajin aikin ba.
Hakan na nufin tattaunawar da aka yi tsakanin NUPENG da gwamnatin tarayyar Najeriya bai yi tasirin hana kungiyar shiga yajin aikin ba.
Ma'aikatan NNPC sun fara yajin aiki
Nigeria: Litar man fetur ta koma N145
Ma'aikatan mai sun soma yajin-aiki a Nigeria
Wannan ba shi ne karo na farko da kungiyoyin kwadagon ma'aikatan man fetur ke shiga yajin aiki ba a Najeriya, kuma a duk lokacin da suka shiga to ana fuskantar matukar wahalar man a kasar.
Tun a ranar Asabar hankalin 'yan kasar ya fara tashi sakamakon rade-radin yajin aikin da suka ji, inda gidajen mai suka fara cika da motoci.
Mutane sun ta cika tankunan motocinsu da mai, har ma suna saye a jarkoki duk saboda tanadi don tsoron fuskantar wahalar karancin man.

Friday, 10 March 2017

BREAKING: 3 Najeriya bankuna saita zuwa sama a kan Etisalat yau kan N541.8 biliyan bashi

Premium Times aka bayar da rahoton cewa uku Najeriya bankuna suna saita zuwa sama a kan sadarwa m Etisalat yau, Laraba, 8 ga watan Maris, bisa unpaid N541.8billion bashi.



An Etisalat kwarewa cibiyar a Lagos Island, daya daga cikin kamfanin dukiya da cewa a yanzu za a kauracewa da bankuna.

Bisa ga rahoton, da tafi ya bi da gazawar da Najeriya sadarwa Commission (NCC) to kulla zaman lafiya ƙuduri tsakanin Etisalat Nigeria da Kamfanin na bankuna.

The bankuna da hannu ne:

1. Guaranty Trust Bank

2. Access Bank

3. Zenith Bank

Duk da haka, wadannan su ne ba ne kawai bankuna a matsayin akwai kuma wasu kasashen waje bankuna da cewa sun kuma an bayar da rahoton cewa ciwon gudu yaƙi da sadarwa kamfanin kan aro makaman totaling $ 1,72 biliyan (game da N541.8 biliyan) da aka samu a shekarar 2015.

Tuesday, 31 January 2017

Google, Facebook Da Twitter Sun Nuna Rashin Goyon Bayansu Ga Trump

Akalla ma'aikatan Google mutum dubu biyu ne(2000) suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da dokar da shugaban kasar Amurka Donald Trump yasa wacce ta haramtawa wasu kasashen musulmai guda bakwai shigowa kasar. Kasashen da abun, ya shafa sune Syria, Iraq, Iran, Libya, Yemen, Sudan da kasar Somalia.
Shugaban babbar kafar sadarwar zamani ta Facebook Mark Zuckerberg shine wanda ya fara fitowa yayi Allah wadai da wannan mataki na Trump. Mark Zuckerberg har wayau ya kasance shugaban kungiyar masu tarbar yan gudun hijira ta Fwd.us.
Ma'aikatan Google daga sassa daban-daban na fadin kasar ta amurka sun gudanar da jerin gwano don nuna kyamarsu ga wannan hukunci na shugaba Trump. Wasu daga cikin guraren da aka gudanar da wannan zanga-zangar sun hada da New York, San Francisco, Seattle da sauran wasu muhimman gurare.
Daga cikin wadanda suka halarci wannan zanga-zanga akwai CEO na kamfanin Google wato Sundar Pichai tare da daya daga cikin wadanda suka assasa Google wato Sergey Brin. Inda Brin din ya bayyana cewa shima ya shigo America ne a matsayin dan gudun hijira a lokacin da ake tsakiyar rikici a can kasarsu.
Suma anasu bangaren kamfanin Twitter sun nuna rashin goyon bayansu ga wannan mataki na Donald Trump inda suka bayyana cewa gamayyar baki mabanbanta addinai ne suka hadu wajen gina twitter saboda haka basa goyon bayan a kori ko a hana dan wata kasa shigowa Amurka.
Kamfanin Apple, Uber da sauran wasu manyan kamfanonin fasahohin zamani suma sun nuna rashin goyon bayan su ga wannan mataki.
Muma anan arewamobile mun yi Allah wadai da wannan tsatstsauran mataki da Donald Trump ya dauka. Bama kyama ko gudu kowa.

Sunday, 29 January 2017

Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

– Bello Abubakar Masaba, mutumin da ya
auri mata barkatai ya riga mu gidan
gaskiya
– Bello Masaba ya mutu yana da mata
kusan 100
– Masaba yayi wasiyya da a rika aure
Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama
Idan ba a manta ba akwai wani ta’aliki
mai suna Bello Abubakar Masaba, a
Garin Bida ta Jihar Neja mai mata
barkatai. Wannan mutumi dai yanzu
Allah yayi masa cikawa a jiya Asabar
bayan yayi ‘yar gajerar rashin lafiya.
Masaba dai ya yanke jinki ya fadi har
sau biyu, daga karshen yace ga garin ku.
Wata Jarida mai suna The Eagle ta bada
labarin rasuwar wannan mutumi. Alhaji
Mutairu Salahuddeen; wani mai
magana a madadin wannna mutumi ya
tabbatar da haka.
Bello Masaba dai kowa ya san sa da
yawan mata, ace mai mata 97, yayi
mata kusan guda 107, ya kuma rasu ya
bar fiye da 80, bayan ya rabu da wasu
da dama. Ya haifi ‘ya ‘ya sama da 185,
sai dai wasu sun rasu, yanzu ya bar
akalla guda 133.
Bello Masaba dai ya rasu ne jiya da
rana, an kuma shirya jana’izar sa a
Ranar yau da safe. Marigayin yayi
wasiyya da a daina zinace-zinace a
koma auren mata na addini. Masaba ya
mutu yana da shekaru 93.

Saturday, 21 January 2017

Nigeria: Ko Donald Trump zai goyi bayan kafa kasar Biafra?

Tun dai bayan zaben shugaba Muhammadu
Buhari a bara, dangantakar Najeriya da Amurka
ta dan inganta.
Dangantakar dai ta yi tsami ne bayan zargin cin
zarafin bila'dama da ake yiwa sojojin Najeriyar,
musamman ma a yakin da suke yi da mayakan
Boko Haram.
Sojojin Najeriyar suna samun horo da kuma
kayan aiki daga gwamnatin Barack Obama, don
haka za su so Mista Trump ya ci gaba da karfafa
wannan dangantakar.
Najeriya za ta kuma so ta samu kyautatuwar
dangantakar kasuwanci da Amurkar.
Wasu daga cikin manyan kamfanonin Amurka na
cikin gaggan masu zuba jari a bangaren
makamashi a Najeriya, amma kuma gano danyan
man da Amurkar ta yi ya sa yawan man da ta ke
saya daga kasar ya ragu.
Me ya sa shugabannin Afirka ke tsoron
mulkin Trump?
'Katobarar da Donald Trump ya yi'
Su waye na hannun-daman Trump
'Yan aware na Biafra
Me yiwuwa kasashen biyu su samu kan su cikin
yanayin nan da Hausawa ke kira ta ciki-na-ciki,
ko kuma akai ruwa-rana, muddin Mista Trump ya
yanke shawarar amincewa da 'yan awaren
Biafra.
Masu fafitikar ballewa daga Najeriyar sun nuna
goyon bayansu ga dan takarar jam'iyyar
Republican din a lokacin yakin neman zabe, suna
masu fatan cewa zai goyi bayan fafitikar da suke
yi ta samun wannan 'yancin.
Sun ce ya goyi bayan ''Brexit''- matakin Birtaniya
na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai - don
haka suke ganin zai goyi bayan "Biafrexit", koda
yake bai nuna alamun zai yi hakan ba a bainar
jama'a.
An samu hargitsi tsakanin masu fafitikar kafa
kasar Biafra da jami'an tsaro a lokacin da suke
zanga-zangar nuna goyon baya a ranar da aka
rantsar da Shugaba Trump.
Wasu rahotanni sun ce an samu asarar rayuka
amma jami'an 'yan sanda sun ce babu wanda ya
mutu.
Akwai 'yan Najeriya fiye da miliyan daya da ke
zaune a Amurka, kuma wasu na fargabar cewa
manufofin Mista Trump kan harkokin shige-da-
fice ka iya kai wa ga korar dubban su zuwa gida.

Tuesday, 17 January 2017

Jiragen yakin Nigeria sun kashe 'fararen hula 50' bisa kuskure

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta
hallaka tare da jikkata fararen hula bisa kuskure
a kauyen Rann, da ke Kala Balge a jihar Borno.
Kungiyar likitocin sa kai ta MSF ta ce mutane
akalla 50 ne suka mutu, yayin da 100 suka
jikkata.
Ma'aikatan agaji na cikin wadanda suka samu
raunuka - kungiyar bada agaji ta Red Cross ta
tabbatar da mutuwar shida daga cikin
ma'aikatanta.
Harin ya faru ne a kauyen Rann da ke kusa da
kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda sojoji ke
fafatawa da mayakan Boko Haram.
Wani kwamanda a rundunar sojin Najeriya Manjo
Janar Lucky Irabor ya ce matukin jirgin yakin ya
kai hari kan mutanen ne a bisa kuskuren cewa
'yan Boko Haram ne.
Ya ce an bashi umarni ne a bisa bayanan sirri
game da wuraren taruwar mayakan Boko Haram.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike
da sakon nuna takaici da kuma jaje, game da
asarar rayukan da aka yi, ya kuma yi kira da a
kwantar da hankali.
Kakakin fadar shugaban kasar, ya ce gwamnati
za ta tallafawa gwamnatin jihar Borno game da
wannan abin bakin ciki da ya faru.
Kakakin kungiyar MSF Etienne l'Hermitte ya yi
kira ga mahukuntan Najeriya da su taimaka
wajen kwashe mutanen da suka samu raunuka ta
sama da ta kasa.
"Jami'an kiwon lafiyarmu a kasashen Kamaru da
Chadi a shirye suke su duba wadanda suka
jikkata", in ji shi.
MSF ta ce akasarin wadanda harin ya rutsa da
su mutanen da suka gudu daga matsugunansu
ne a yankunan da 'yan Boko Haram ke kai hare-
hare.
Rahotanni sun ce lamarin dai ya rutsa da jami'an
tsaro da dama, inda wasu suka mutu yayin da
wasu kuma suka samu raunuka.
Rundunar sojin ta ce tana amfani da jirage masu
saukar ungulu domin kwashe wadanda suka
jikkata.

Monday, 16 January 2017

Dokar Nigeria ta durkusar da kasuwar motoci a Jamhuriyar Benin

Masu sayarda motoci a Cotonou babban birnin
jamhuriyar Benin, sun koka da rashin cinikin
motoci, tun bayan da gwamnatin Najeriya ta
sanar da hana shigo da motoci na tokumbo daga
iyakokinta na tudu.
Bincike ya nuna cewa sama da kaso casa'in da
biyar na motocin tokumbo da ake sauke su a
gabar tekun jamhuriyar Benin, masayansu na
fitowa daga Nigeria ne mai makwabtaka da
kasar.
Masu sayar da motocin sun ce yanzu kasuwar ta
ja baya kuma farashin motocin ya sauko, saboda
faduwar darajar Naira da kuma rufe iyakokin da
Nigeriar ta yi wadanda suka taimaka wajen
rashin samun cinikin motocin.
A baya dai jiragen ruwa na sauke kwantenoni
ciki da motoci kamar dubu goma a wata,amma
tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da
sabuwar dokar,jirage a gabar tekun Cotonou suka
ja baya inda a sati bai fi a sauke kwantenoni
hamsin ba.
Rasa ayyuka
Karancin masu sayen motocin ya sanya wasu
daga cikin masu wannan harakar rasa
ayyukansu.
Majalisar Dattawan Nigeriar dai ta bukaci
gwamnatin kasar da ta janye wannan matakin da
ta ce ya haddasa dubban 'yan kasar sun rasa
aikin yi.
To sai dai kuma hukumar hana fasakwauri ta
Nigeria ta ce matakin da aka dauka zai taimaka
wajen bunkasa harajin da gwamnati ke samu
tare da samar da aikin yi.

Sunday, 15 January 2017

Cacar-baka tsakanin gwamnati da BBOG kan Sambisa

Gayyatar da gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan
kungiyar da ke fafutikar ganin an ceto 'yan
matan Chibok, wato BBOG, zuwa dajin Sambisa
ta janyo zazzafar muhawara.
Ita dai gwamnatin, a wata takardar gayyata da
Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya aikewa
kungiyar, ta yi kira ga 'yan BBOG su aike mata
da sunayen mambobinsu uku domin a tafi da su
Dajin Sambisa su ga irin fafutukar da ake yi ta
ceto 'yan matan na Chibok.
A cikin sanarwar, ministan ya yaba wa 'yan
kungiyar ta BBOG bisa fafutukar da suke yi, yana
mai cewa, "Domin jinjinawa fafatukar da kuke yi
don ganin an ceto 'yan matan Chibok, muna so
ku ba mu sunayen mambobinku uku domin zuwa
yankin arewa maso gabas ranar Litinin, 16 ga
watan Janairu".
A cewar Minista Lai Mohammed za a yi tafiyar
ne da ministan tsaro, da na watsa labarai, da
wasu 'yan jarida da babban hafsan sojin kasa, da
kuma babban hafsan sojin sama. Da farko
tawagar za ta fara zuwa Yola don ganin yadda
rundunar sojin sama ke farautar 'yan matan na
Chibok, sannan daga bisani su shiga jiragen
saman yakin da ke shawagi a Dajin Sambisa.
'Wasan-ɓuya'
Sai dai a wata wasikar martani da ta aike wa
ministan, kungiyar ta ce mabobinta sun gana sun
kuma yarda da yin amfani da irin wannan dama
don sanin halin da ake ciki a yankin na arewa
maso gabashin Najeriya.
Amma, a cewar wasikar, "Kafin a yi batun
tafiyar, ya kamata mu yi taro da ku domin ku
amsa mana wasu tambayoyi da ke damun mu.
Muna so mai bai wa shugaban kasa shawara a
kan sha'anin tsaro da ministan tsaro da babban
hafsan sojin kasa da kuma babban hafsan sojin
sama su halarci taron".
Kungiyar ta yi korafin cewa kwanaki kadan da
suka gabata wata kungiya da ta rika cin
mutuncin su ta samu tarba ta musamman daga
babban hafsan sojin kasa na Najeriya, lamarin
da, a cewar ta, yake matukar damun ta.
Ta kara da cewa dole ne babban hafsan sojin ya
nemi gafara daga wurinta sannan ya wanke
kansa daga cin zarafin da kungiyar ta yi musu
idan ana so su amsa goron gayyar gwamnati.
Daga bisani kuma daya daga cikin jagororin
kungiyar, Aisha Yesufu, ta wallafa a shafinta na
Twitter cewa tana kalubalantar shugaban kasar,
Muhammadu Buhari, ya jagorance su zuwa dajin
na Sambisa idan da gaske ne yake yaki da
ta'addanci.
Batun dai ya sa wasu na ganin 'yan kungiyar ta
BBOG suna kokarin guje wa gayyatar da aka yi
musu ne kawai, inda wasu ma ke ganin da ma
fafatukarsu ba ta wuce Abuja, fadar gwamnatin
kasar, ba.
Sai dai wasu sun ce ba haka batun yake ba.

Friday, 13 January 2017

MMM Nigeria Ya Dawo Aiki, Ko Menene Shi MMM Din?

Hadaddiyar cibiyar hada-hadar kudade ta MMM Nigeria ta fitar da sanarwar dawowa kan gudanar da harkokin kasuwanci gadan-gadan kamar yadda aka saba a can kwanakin baya.
Sanarwar dai ta fito ne ta shafin kafar na twitter a safiyar yau Juma'a inda suka bukaci jama'a dasu koma cikin harkar ba tare da wata fargaba ba duk da rade-radin da ake na cewar tsarin kasuwancin na iya kasancewa na yan damfara ne wanda ka iya rushewa da dukiyar mutane a kowanne lokaci.
A watan Disamban daya gabata ne dai kafar ta dakatar da duk wata hada-hadar kasuwanci inda aka tsayar da asusun ajiyar duk masu amfani da kafar ta yanda baza a iya tura ko karbar kudi ba har sai zuwa 14 ga watan Janairun 2017. Hakan ya jefa tsoro a zukatan mafi yawa daga cikin masu amfani da kafar duba da irin gargadin da babban bankin tarayya yayi kan cewar MMM yan damfara ne.
Sai dai kuma daga bisani shugaban gudanarwa na MMM Nigeria ya fito karara yayi wa jama'a bayanin cewa su harkarsu ba ta damfara ba ce face dai harka ce ta taimakawa juna.
Menene MMM kuma ya tsarin abun yake?
Na koma hutun semester a makaranta sai wani abokina yake tambayata cewar shin Deendabai kana yin MMM duba da cewar kakan yi kokarin shiga abubuwan da suka shafi hanyar juya kudi ta internet? Amsar da na bashi itace ban yarda da tsarin ba saboda haka bana yi.
MMM gajarcaccen bayanin wasu kalmomi ne na turanci da yake nufinMavrodi Mondial Moneybox, asusu ne na adashin kudi da ya faro daga kasar rasha(Russia), wanda ya kware wajen yin adashe na kudi tare da juyasu ta yanda kowanne member zai rika samun kudin ruwa bayan kwana talatin (30) da zuba kudinsa da karin kaso talatin (30%).
Yadda abun yake shine in ka zuba kudi a matsayinka na sabon mamba to za'a dauki kudinka a ba tsohon mamba da yakai akalla kwana talatin da zuba kudi, haka kaima za'a dauko kudin wasu sabbin mambobin tare da karin kaso 30 a baka bayan cikar kudinka da kwana talatin a gurinsu. Misali ace ka zuba kudi kamar naira dubu dari N100,000, to a tsarin MMM zaka karbi Naira dubu dari da talatin ne bayan kwana 30.
Sai dai kuma tsarin MMM yasha kakkausar suka musamman daga malamai duba da cewar harka ce da ta shafi bayarda kudin ruwa wanda hakan ya sabawa koyarwar addinin musulunci, dadin dadawa kuma akwai alamun cuta ko cutarwa a cikin lamarin bisa la'akari da cewar ba a san kowanne irin kasuwanci akeyi da wadannan kudade ba.
Wannan shine dan takaitaccen bayani dangane da MMM da zaku iya ji daga bakin Deendabai. Fatan zaku tura ma abokanen wannan labari don suma su karu...

Thursday, 12 January 2017

Ba abin da zai hana ni zama shugaban Gambia - Barrow

Wanda ya lashe zaben shugaban kasar Gambia
Adama Barrow ya ce ko ana ha-maza ha-mata
sai ya sha rantsuwar kama aiki a zaman
shugaban kasar Gambia a makon gobe.
A cikin wata hira da BBC Mr. Barrow ya yi kira
ga shugaba mai ci yanzu Yahaya Jammeh da ya
zo su tattauna ido-da-ido domin warware rikicin
siyasar kasarsu gabanin wannan ranar 19 ga
wata Janairu.
Kalaman nasa na zuwa ne sa'o'i gabanin isar
tawagar masu shiga tsakanin ta kungiyar Ecowas
zuwa kasar domin ciwo kan Yahaya Jameh ya
sauka a cikin Lumana.
''Wa'adin mulkinsa zai kare da karfe 12 na dare
na ranar 18 ga wata, don haka a hukumance zan
kasance shugaban kasar ranar 19 ga wata; kuma
ko ana ha-maza ha-mata sai an rantsar da ni'' inji
Barrow.

Tuesday, 10 January 2017

'Yadda fyaɗe ke ƙara ta'azzara a arewacin Najeriya'

Wata kungiya mai zaman kanta da ke ayyukan
kula da mata da kananan yara da marayu a jihar
Kadunan Najeriya, mai suna ARRADA, ta ce,
fyade na karuwa yadda ba a zato, a arewacin
Najeriya.
Hajiya Rabia Ibrahim, shugabar kungiyar ta
ARRADA, ta bayyana wa BBC cewa, an sami
batutuwan yi wa yara maza da mata fyade fiye
da 100 a shekarar 2016.
Sai dai kuma ta ce batutuwan da suka fi zafi da
daukar hankalin mutane sun fi guda 50 wadanda
aka samu a daga watan Agusta zuwa Disambar
2016.
Hajiya Rabia ta zayyana manyan fyaden da aka
samu kamar haka
A Kaduna, wani dagaci mai shekara fiye da
80, ya karbi wata yarinya da ta bata kuma da
shi da dansa da jikansa duka sun kwashe
shekara guda suna yi wa yarinyar fyade.
Yaro dan shekara biyar ya gamu da ajalinsa,
bayan da wani matashi mai shekara 12 ya yi
lalata da shi, a Zariya.
Wata yarin 'yar shekara hudu ta samu
matsalar kasa rike bayan gida sakamakon
fyaden da aka yi mata ta gaba da bayanta.
An kuma sami wani magidancin da yake yi
wa 'ya'yan cikinsa guda uku fyade da suka
hada da mai shekara biyu da hudu da kuma
'yar wata bakwai wadda cikinta ya kumbura
saboda hadiye maniyyin mahaifin nata.
Hajiya Rabia ta kuma koka kan yadda ake samun
jan kafa tsakanin hukumomin 'yan sanda da
bangaren Shari'a wajen hukunta masu aikata irin
wannan laifi.
Ta kara da cewa rashin hukunta wadanda aka
samu da laifin ne yake sanya al'amarin yake kara
ta'azzara.
To amma shugabar kungiyar ta ARRADA, ta
shawarci jama'a musamman iyaye kan yadda ya
kamata su kula da kai komon 'ya'yansu.
Ya kamata iyaye musamman mata su sanya
ido kan masu kula da 'ya'yansu, misali direba
ko kuma mai aiki.
Iyaye su kula sosai da mutanen da 'ya'yan
nasu suke matukar shakuwa da su misali
ankul ko anti da dai sauransu.
Kula da masu yawan yi wa yara wasa ko
kuma ba su kyaututtuka.
Ka da iyaye su rinka korar 'ya'yansu da su je
su yi wasa domin kyale su shakata.
Iyaye mata su rinka duba al'aurar 'ya'yansu
musamman idan suka zo suna kuka tunda
dai ba sa iya magana.
Sharhi, Usman Minjibir
Kusan dai za a iya cewa matsalar fyade a
arewacin Najeriya na daya daga cikin wasu
matsaloli da ake samu amma kuma ba a son
daga maganar.
Masana suna alakanta rashin bunta zancen
fyade ga dalilai na addini da al'ada da kuma
rashin son kunyata a cikin al'umma.
Sau da yawa a kan samu iyaye maza da suke yi
wa 'ya'yansu 'yan mata fyade amma saboda
gudun abin kunya, a kan lullube maganar.
A mafi yawancin lokaci, da zarar an daga irin
wannan maganar, abin da ke biyo baya shi ne
kyama daga wurin al'umma.
A kan samu yanayin ma da yarinya ba za ta
samu manemi ba sakamakon fuskantar matsalar
fyade duk kuwa da cewa ba a son ranta aka yi
mata fyaden ba.
Ana dai ganin cewa da za a rinka kai maganar ga
mahukunta kuma ba tare da wata-wata ba a
hukunta duk wanda aka samu da laifi, to da
al'amarin ya bai kai haka ba.
Arewacin Najeriya dai na daya daga cikin
yankuna masu dimbin al'umma musulmai a
nahiyar Afirka.
Kuma yankin ne yake gaba a yawan musulmai a
Najeriya.
Har ma wasu jihohin yankin na ikrarin kwatanta
zartar da Shari'a bisa doran AlQur'ani.

Nigeria - An cire Ali Ndume daga shugaban masu rinjaye

Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cire
Sanata Mohammed Ali Ndume a matsayin
shugaban masu rinjaye a majalisar. Inda ta
maye gurbinsa da Sanata Ahmed Lawal.
Shugaban majalisar, Bukola Saraki ne ya karanta
wasikar sauya shugaban masu rinjayen a zaman
majalisar a ranar Talata.
Jam'iyya mai mulkin kasar ta APC ce ta nemi a
sauya Ndume da Ahmed Lawal, a lokacin wani
taron 'ya 'yan jam'iyyar da ke majalisar.
Sanata Ahmed Lawal dai ya nemi zama
shugaban majalisar dattawan, amma bai yi
nasara ba.
Lamarin da ya raba kan 'yan jam'iyyar ta APC a
majalisar.
Sanata Ndume ya shaida wa BBC cewa ba a
tuntube shi a kan sauyin ba, kuma babu wanda
ya gayyace shi taron 'yayan jam'iyyar da ke
majalisar.
Babu wasu kwararan dalilai da aka bayyana na
sauyin.

Monday, 9 January 2017

Gambia: Minista ya yi murabus domin kyamar Jammeh

Ministan sadarwa na kasar Gambia, Sheriff
Bojang, ya sanar da yin murabus daga kujerarsa,
a wani mataki na matsa wa Yahya Jammeh
lamba da ya sauka daga shugabancin kasar.
Mista Bojang ya ce ya yi hakan ne domin nuna
kin amincewa da yunkurin shugaba Yahya
Jammeh, na karya dimokradiyyar Gambia.
Sheriff Bojang wanda ya shaida wa kamfanin
dillanci labarai na Reauters hakan, ya kuma ya yi
kira ga sauran masu rike da mukamai irin nasa
da su ma su kwata irin abin da ya yi.
Gidan talbijin mallakar kasar dai ya bayyana
cewa shugaba Jammeh ya yi wa mista Bojang
Korar kare daga aiki ba murabus ya yi ba.
A yau ne dai ake sa ran kotin kolin kasar za ta
fara sauraron karar da shugaba Yahya Jammeh
ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben da
ya ba wa abokin adawarsa, Adama Barrow
nasara, a kansa.
Amma kuma rahotanni na cewa har yanzu
alkalan kotun wadanda ake zargin an yi hayarsu
daga Najeria da Sierra Leone, ba su kai ga isa
Gambiyar ba.
A ranar Litinin ne dai shugabannin wasu kasashe
a Afirka ta Yamma suka yi wani taro a Abuja,
babban birnin Najeriya, kan makomar siyasar
Gambia.
Sun kuma yanke shawarar sake komawa kasar
domin lallashin shugaba Jammeh ya mika mulki
ranar 19 ga watan Janairun nan.
Shugaban Gambia mai ci, Yahya Jammeh dai ya
sauya aniyarsa ta kin amincewa da shan kaye,
kasa da mako daya bayan ya amince da faduwa.
Jammeh ya nemi da a sake zabe, a inda kuma
sojoji suka karbe ragamar iko da hukumar zaben
kasar, bayan da shugaban ya zarge ta da tafka
masa magudi.
yi amai ya lashe
Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben Gambia
Wasu dai na danganta kin amincewa da shan
kayen da Jammeh ya yi da kalaman da
zabbabben shugaba, Adama Barrow ya rinkayi
cewa za su bi doka wajen gurfanar da Yahya
Jammeh.
Kusan za a iya cewa yanzu haka kallo ya koma
kasar Gambia domin sanin abin da zai je ya zo
daga ranar 19 ga Janairu, ranar da ya kamata
Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow.

Sunday, 8 January 2017

Mutane 4 sun mutu a hari da babbar mota a Jerusalem

Wani Bafalasdine ya kashe 'yan kasar Isra'ila
hudu a Jerusalem lokacin da ya danna da
babbar mota cikin wani gungun sojojin, a wani
abu da 'yan sanda suka ce hari ne na ta'addanci.
Wadanda suka mutun sun hada da mata uku da
namiji guda, sannan wasu goma sha uku kuma
sun jikkata.
'Yan sanda sun ce sojojin dake kusa sun harbe
direban har lahira.
A watanni goma sha biyar da suka gabata,
mutane daga Falasdinu sun sha kai hare hare da
wuka da bindiga da kuma motoci akan 'yan
Isra'ila.
Babban jami'in 'yan sandan Isra'ila, Roni Alsheich
ya ce maharin na ranar Lahadin nan, Bafalasdine
ne daga Gabashin Jerusalem.
Bidiyon da kyamarorin gefen hanya suka nada,
ya nuna babbar motar lokacin da take tafiya a
guje inda ta danna cikin sojojin, sannan kuma
direban ya koma da baya inda ya sake bi ta kan
mutanen da ya taka.
Kafin harin na ranar Lahadi, Isra'ilawa talatin da
biyar aka kashe a hare-haren da ake zargin
Falasdinawa ko Larabawan Isra'ila da kai wa tun
daga watan Oktoban 2015.
Isra'ila ta ce Falasdinawa fiye da dari biyu ne,
akasarinsu maharan, aka kashe a lokacin.

Buhari ya sake shan alwashin ceto 'yan matan Chibok

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce
yana fata nan ba da jimawa ba za a ceto sauran
'yan matan Chbok da aka sace kwana 1000 da
suka wuce.
Shugaba Buhari, wanda ya bayyana haka a
shafinsa na Twitter ranar Lahadi, ya kara da
cewa gwamnatinsa tana bakin kokarinta domin
ganin ta ceto 'yan matan da ma sauran mutanen
'yan Boko Haram suka sace.
A cewarsa, " Ina so na jaddada matsayina cewa
kamar yadda a baya na sha alwashin ceto su,
yanzu ma ba za mu karaya ba har sai mun
mayar da sauran 'yan matan hannun iyayensu".
Shugaban na Najeriya ya jinjina wa dakarun sojin
kasar bisa jajircewarsu wajen yaki da Boko
Haram, yana mai yaba wa dukkan mutanen da ke
fafutikar ganin an ceto 'yan matan.
An sake gano wata 'yar Chibok
Ziyarar 'yan matan Chibok ta bar baya da
kura
A ranar Lahadi ne ake cika kwanaki 1000 da
sace 'yan matan na makarantar Chibok 276 da
mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno da
ke arewa maso gabashin Nigeria.
Lamarin dai ya ja hankalin mutane da
gwamnatoci a sassan duniya daban-daban; inda
aka yi ta yin zanga-zangar neman a sako su.
'Sun cika kwana 1000 a tsare'
Fiye da 'yan mata 50 ne suka kubutar da kansu
tun ranar da aka sace sun wato 14 ga watan
Afrilun 2014, yayin da kawo yanzu gwamnati ta
samu kwato wasu kari 23.
A cikin wata sanarwa da ta fitar kan cika
kawanakki dubun da sace su, kungiyar kare
hakkin biladama ta Amnesty International ta yi
kira ga gwamnatin Najeriyar ta kara matsa kaimi
wajen ganin ta kubutar da sauran 'yan matan, da
ma wasu da ke hannun mayakan.Kungiyar ta
Amnesty ta kuma yi kira ga kungiyar Boko
Haram da ta kawo karshen ukubar da ta jefa
'yan matan dama sauran wadanda take rike da
su, don su koma cikin iyalansu.
Amnesty ta ci gaba da cewa, ba wai tana zargin
gwamnati da rashin kokari wajn kubuto da 'yan
matan da ma sauran wadanda aka sace ba ne,
tana so ne a kara himma saboda ba 'yan matan
kadai ne a hannun mayakan ba, har ma da wasu
mutane da suka hada da mata da yara.
Sai dai ta ce tana yaba wa gwamnatin kasar
kwarai da gaske wajen kubutar da sauran.

Friday, 6 January 2017

Nigeria: Tsohuwar ministar mai ta mika dala miliyan 153 ga EFCC

Tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Nigeria
Diezani Alison-Madueke ta mika wa gwamnatin
kasar dalar Amurka miliyan 153 da ake zargin ta
sata daga asusun gwamnati.
Hakan dai ya biyo bayan wani hukunci da wata
kotu ta yanke a birnin Legas ranar Jumu'a cewa
matar ta mika wadannan kudaden ga gwamnatin
har a tabbatar da halaccinsu ko akasin haka.
A cewar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin
kasar zagon kasa ta EFCC - wadda ita ce ta
bukaci kotun da ta umarci tsohuwar ministar ta
mika kudin - an sace kudin ne daga kamfanin mai
na NNPC kana aka boye su a wasu bankuna uku
da ke kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar NAN ya ce
Alkalin kotun Muslim Hassan wanda ya ba da
wannan umarnin; ya bai wa jami'an bankunan
uku wa'adin kwanakki 14 su bayyana gabansa
domin su kawo masa shaidar da ke nuna cewa
kudin ba na sata ba ne.
Ya ce idan suka kasa yin hakan to za a sallama
kudin kacokan ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
'Yadda aka saci kudin'
A cikin bukatar neman mika kudaden wadda
jami'in bincike na hukumar ta EFCC Moses
Awolusi ya gabatar wa kotun, hukumar ta ce a
watan Disamba na shekara ta 2014 ne tsohuwar
ministar ta kira babban manajan daya daga cikin
bankunan a ofishinta suka tsara yadda za a saci
kudaden.
Jami'in hukumar ya yi zargin cewa Mrs Diezani
Alison-Madueke ta bukaci babban manajan
bankin da ya tabbatar da cewa ba a saka kudin a
cikin asusun da aka san da zamansa ba kuma ba
a rubuta shigar da kudin ba cikin kundin da
bankin ke rubuta huldodin da ya yi ba.
Rahoton na kamfanin dillancin labaran Najeriyar
dai bai fadi ko lauyoyin tsohuwar ministar suna a
kotun lokacin wannan zaman ba; balle martanin
da suka mayar ga wadannan zarge-zargen.
Amma dai wannan ba shi ne karon farko da ake
zargin ministar da almundahana ko facaka da
kudaden jama'a ba, amma kuma a kodayaushe
takan musanta.