Shahararre kuma gogarman Kannywood, jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewar fim din kamfanisa, Mansoor da aka kammala dauka kwanan baya za a sake shi a sinumun Nijeriya lokacin bukukuwan karamar Sallah.
Jarumin ya bayyana haka ne yayin tattaunawar musamman da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce duba da yanayin irin aikin da aka yi wa fim din, kamfanin FKD sun yanke shawarar sakinsa a bukukuwan sallah.
“Mansoor fim ne da aka kashe makudan kudade wajen yin sa, saboda haka hanyoyin tallata shi kadai sun bambanta da yadda ake yi wa saura finafinai. Mun zabi lokacin bukukuwan karamar sallah ne domin domin bawa mutane damar kallon sa kasnacewar ana hutu.” A cewar Ali Nuhu.
“Mutane da yawa sun kagu su ga wane sako Mansoor ke dauke da shi, abin da nake so in tabbatar shi ne, fim din ya zo da wani irin salo wanda ba a saba gani ba.
“Duk wanda ya ga yanayin jaruman da aka sanya a cikin fim din, zai ga cewa sabbi ne, watau wadanda ba su taba fitowa a matsayin cikakkun jarumai ba. Da ma shi kamfani FKD ba bako ba ne wajen dauko kananan jarumai ya wanke su, sannan ya saka su a finafinansa.” In ji shi.
Mansoor fim ne da ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Abba El-Mustapha, Tijjani Faraga; sai kuma sabbin jarumai, Umar M Shareef da Maryam Yahaya.
Wannan dai shi ne fim na farko da FKD ta shirya tun bayan fim din da ya tara zaratan jarumai maza zalla watau Ga Mu Nan Dai.
® Leadership Hausa
nice update
ReplyDelete