Showing posts with label SASHEN SIYASA. Show all posts
Showing posts with label SASHEN SIYASA. Show all posts

Friday, 20 January 2017

Gambia: Yahya Jammeh 'ya amince ya bar mulki,' ya kuma fice daga kasar

Zababben shugaban kasar Gambia ya ce Yahya
Jammeh ya amince ya sauka daga kan karagar
mulki, sannan kuma ya fice daga kasar.
Adama Barrow ya bayyana hakan ne a shafinsa
na Twitter bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa
domin shawo kan Mista Jammeh ya amince da
sakamakon zaben.
Tun da farko Shugaban ƙasar Guinea Alpha
Conde da na Mauritania Mohamed Ould Abdel
Aziz sun isa Banjul don ganawa da Yahya
Jammeh.
Shugaban hukumar ECOWAS, Marcel Alain de
Souza ya ce idan tattaunawar ta gaza samun
nasara, sojoji za su ɗauki mataki.
Jawabin kama-aiki
A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba
Adama Barrow ya ce: "Daga yau (Alhamis), Ni ne
shugaban ƙasar Gambia ko ka/kin zaɓe ni ko ba
ka/ki zaɓe ni ba."
Ya ce "Wannan nasara ce ga ƙasar Gambia..
mulki a hannun jama'a yake a Gambia"
A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani
ɗan Gambia da zai taɓa mantawa da ita... karon
farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta
sauya gwamnati ta hanyar ƙuri'a".
Shugaban ƙasa biyu
A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan
mulki ya ƙare, ko da yake majalisar dokokin ƙasar
ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.
'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke
zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka
fice zuwa wasu ƙasashe maƙwabta saboda tsoron
ɓarkewar rikici.
Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da
aka yi cikin watan Disamba.
Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye
sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga
bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba
saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai
a zaben.
Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar
sakamakon zaben.

Wednesday, 11 January 2017

Gambia: Shugaba Jammeh ya sha alwashin ci gaba da mulki

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya sha
alwashin cewa 'zai zauna a kan kujerar mulki har
sai an yanke hukunci a kan sakamakon zaben
shugaban kasar'.
Shugaba Jammeh ya ce ba zai sauka daga
kujerar mulki ba sai bayan Kotun Koli ta yanke
shawara a kan jayayyar da yake yi da sakamakon
zaben, karar da sai a watan Mayu za a saurare
ta.
A wani jawabi da ya yi ta gidan talibijin na kasar,
ya jaddada rashin amincewa da katsalandan din
da kasashen waji ke yi a harkar cikin gida ta
kasar.
Wata tawagar ECOWAS a karkashin jagorancin
shugaban kasar Nijeriya za ta kai ziyara Gambia
ranar Juma'a don kara matsawa Yahya Jammeh
lamba don ya mika mulki ga Adama Barrow
bayan zaben watan Disamban bara.
Shugaba mai jiran gado Adama Barrow ya ce za
a kaddamar da shi a mako mai zuwa.
Mista Jammeh, wanda ya kwashe shekaru yana
mulki, da farko dai ya amince ya mika mulki
bayan an kayar da shi a zaben, sai dai kuma
daga bisani ya ce bai amince da sakamakon ba
saboda wasu kurakurai da aka ce an gano wajen
hada alkaluman.
Amma hukumar zaben ta jaddada cewa kuskuren
bai shafi sakamakon ba kuma Mista Barrow ne
ya lashe zaben.
Tun 1994 Mista Jameh ke mulkin kasar Gambia,
kuma ana zargin shi da tauye 'yancin bil'Adama
duk da cewa yana gudanar da zabe a-kai-a-kai.

Tuesday, 10 January 2017

Labarai Cikin Hotuna: Gwamna Ibrahim Shema A Yayin Daya Isa Kotu Don Amsa Tambayoyi

A dazu kenan da mai girma tsohon gwamnan jihar Katsina barrister Ibrahim Shehu Shema ya bayyana a gaban babbar kotun saurarar kararraki dake jahar katsina don amsa tambayoyi da hukumar yaki da rashawa ta EFCC zasu yi masa.
Shema wanda yake sanye cikin dinkin babbar riga na shadda mai ruwan kasa ya samu rakiyar chairman PDP na jahar katsina, tsohon chairman party Rabiu Gambo Bakori, sakatare, kwamishinoni da sauran magoya bayansa.
Daga cikin mahalarta taron kotun akwai SSG na jahar, Mustapha inuwa da kuma mai ba gwamna shawara akan harkoki na musamman wato Alhaji Tanimu Sada.
Duba hotunan a kasa...

Saturday, 7 January 2017

PDP ta yi Allah wadai da korar 'yan sanda 6 a Najeriya

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta PDP ta yi Allah
wadai da matakin da rundunar 'yan sandan kasar
ta dauka na sallamar jami'anta shida dake aiki
da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada
labaranta na kasa, Prince Dayo Adeyeye ya fitar,
jam'iyyar PDP ta ce shari'ar da aka yi wa 'yan
sandan a asirce, da kuma sallamarsu da aka yi,
abu ne na rashin gaskiya.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa, saurin korar 'yan
sandan da aka yi, wata karin alamace ga
yunkurin yin magudi da halaka gwamna Wike
gabanin zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar
Rivers a watan Disamba.
Jam'iyyar PDP ta ce "gwamnatin APC ta yanke
shawarar hukunta jami'an 'yan sandan ne saboda
sun dage yin aikinsu yadda ya kamata, sun ki
aiwatar da shirin wasu na ganin bayan gwamna
Wike".
Ta kuma kara da cewa zargin saba ka'idojin aiki
da ake wa 'yan sandan, wani abin kunya ne ga
tsarin aikin dan sanda da tafarkin dimukradiyya.
A saboda haka jam'iyyar ta PDP ta yi kiran ganin
an mayar da 'yan sandan bakin aikinsu ba tare da
bata lokaci ba, domin kare martabar aikin, da
gaskiya da adalci.
In za a tuna, rundunar 'yan sandan Najeriya ta
sallami jami'an na ta shida ne wadanda ta ce sun
aikata laifuka daban-daban a lokacin zaben 'yan
majalisu da aka gudanar a jihar Rivers.
Kakin rundunar Don Awunah ya ce bincike ya
nuna cewa jami'an wadanda suka hada da Sufeto
Eyo Victor da Sajen Peter Ekpo da Sajen Ogoni
Goodluck sun yi harbi cikin jama'a ba bisa ka'ida
ba.
Sauran sun hada da Sajen Orji Nwoke da Sajen
Okpe Ezekiel da kuma Sajen Tanko Akor.
Ta kara da cewa sun aikata laifin ne ranar 10 ga
watan Disambar 2016 lokacin da suka bi tawagar
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wajen dirar
mikiya a kan sakatariyar karamar hukumar
Fatakwal.

Friday, 6 January 2017

Bukin rantsarda sabon shugaban Ghana ya kankama

Kasar Ghana ta shirya tsaf domin bukin rantsar
da Nana Akuffo Addo a zaman shugaban kasar
na 12 a tarihi kuma na 5 a jamhuriya ta hudu.
Da misalin karfe 10 na safiyar yau Assabar
agogon kasar ne za a rantsar da sabon shugaban
a yayin wani gagarumin biki a Accra babban
birnin kasar.
Hakan ya biyo bayan da Nana Akuffo Addo -
wani lauya mai fafutukar kare hakkin bil'adama -
ya kayar da shugaba mai-ci John Dramani
Mahama a zaben da aka gudanar a watan jiya.
Shugabannin kasashen Afrika 11 ne ake sa ran
za su halarci bikin ranstuwar, wanda zai gudana
a dandalin Independence Square da ke birnin na
Accra.

Thursday, 5 January 2017

Donald Trump ya sake musanta kutsen da aka zargi Rasha da yi a Zabe

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump
ya sake nuna shakku a kan zargin da ake na
cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben Amurka
da aka yi a shekarar da ta gabata.
Ka Mr Trump ya yi a shafin Twitter sun zo ne
sa'oi kafin jami'an leken asirin Amurka su yi
masa karin haske kan dalilin da ya sa su ka yi
imanin cewa Rasha ta umarci masu kutse a
shafin intanet da su yi wa abokiyar hamayyarsa
ta jam'iyyar democrats Hillary Clinton zagon kasa
a lokacin zaben.
A martanin da ya mayar, mataimakin shugaban
kasar Joe Biden ya ce matukar rashin hankali ne
ga Trump ya ce yana shakku kan wani abu da
jami'an hukumar leken asirin kasar suka fada.
Tuni dai shugana Obama ya karbi rahoton
hukumomin wanda ya ce manyan jami'an
gwamnatin Rasha sun cashe da suka samu
labarin cewa Trump ya samu nasara a zaben.

Ana ci gaba da Ja-in-ja tsakanin Obama da Trump kan Obamacare

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga
'yan majalisar dokokin kasar daga jam'iyyarsa ta
Demokrat da su tashi haikan su kare tsarin
inshorar kiwon lafiyar da gwamnatinsa ta fito da
shi; wanda gwamnatin Trump ta sha alwashin
soke wa.
A cikin wata ganawa ta sa'oi biyu da 'yan
majalisar ranar Laraba, Mr. Obama ya nemi
goyon bayan 'yan jam'iyyar tasa kan su hana 'yan
Refublika kawar da wannan tsarin nasa.
Ganawar ta biyo bayan da mataimakin shugaban
kasar mai jiran gado, Mike Pence, ya je majalisar
inda ya shaida wa 'yan jam'iyyarsu ta Refublika
cewa gwamnatinsu za ta sauya wannan tsarin.
Bayan ziyarar da shugaban barin gado ya kai
harabar majalisar, dan majalisar wakilai na
jam'iyyar Demokrat Elijah Cummings ya shaida
wa manema labarai cewa Mr. Obama ya nemi da
su tashi haikan su kare wannan manufar tasa.
Wadannan kalaman nasa sun zo ne bayan da
'yan jam'iyyar ta Refublika da ke majalisar
dattawa suka dauki matakin farkon na soke
tsarin kiwon lafiyar da aka fi sani da Obamacare.
Sun jefa kuri'a amincewa da wani kuduri a
kasafin kudi da aka tsara da manufar zaftare
kudade ake warewa tsarin.
Wannan tsarin kiwon lafiyar dai ya fadada
hanyoyin samun inshorar kiwon lafiya ga
Amurkawa Miliyan 20 wadanda ba su iya
samunsa in ba don tsarin ba.
Amma tsarin - wanda aka fito da shi tun a
shekara ta 2010 - ya gamu da cikas na karuwar
tsadar kudaden da ake biya da kuma janyewar
manyan kamfanonin da ke bayar inshorar ta
lafiya, abin da ya bar Amurkawan da zabi maras
yawa kan kiwon lafiya.

Wednesday, 4 January 2017

'Yar Somalia ta zama 'yar majalisa a Amurka

Ilhan Omar ta kafa tarihi bayan da ta zamo 'yar
Somalia ta farko da aka zaba a matsayin 'yar
majalisar dokoki a Amurka.
Ms Omar, wacce aka haifa a Somalia, ta je
Amurka ne a matsayin 'yar gudun hijira.
An zabe ta a majalisar wakilai ta jihar Minnesota
a wani zabe mai zafi da aka fafata bara.
Zaben Ms Omar, wacce Musulma ce, ya zo
kwanaki kadan bayan da zababben Shugaban
Amurka Donald Trump ya zargi 'yan gudun hijirar
Somalia a Minnesota da "yada tsattsauran
ra'ayi".
Akwai al'ummar Somalia da dama da ke zaune a
Amurka, musamman a jihar Minnesota.
Kuma ana yi wa zaben Ms Omar wani kallon abin
da ka iya kara fito da kimar 'yan kasar da ke
zaune a jihar da ma Amurka baki daya.

Friday, 16 December 2016

Kotu ta yi watsi da bukatar Nyako kan komawa mulki

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako kan ta mayar da shi kan kujerarsa domin ya karasa wa'adin mulkisa.
Majalisar dokin jihar Adamawa ce dai ta cire Nyako daga kan mulki a watan Yulin shekarar 2014 wata goma kafin ya kammala wa'adinsa.
'Yan majalisar sun tsige shi ne bisa abin da suka ce saba ka'idar aiki da almubazzaranci da dukiyar al'umma.
Da suka yin watsi da bukatar tasa, alkalai bakwai na kotun kolin karkashin jagorancin mai sharia Tanko Muhammad sun amince da hukuncin kotun daukaka kara wanda ya ce tsigewar da aka yi wa Nyako bai dace ba, amma ba za ta mayar da shi kan mulki ba saboda yadda karamar kotu ta tafiyar da lamarin.
Sun kara da cewa lauyan Murtala Nyako ya yi kasassaba kan karar da ya shigar a kotun daukaka kara saboda bukatar da ya shigar a gabanta domin ya janye batun sake mayar da tsohon gwamnan kan kujerarsa.

Thursday, 15 December 2016

Sanatoci sun yi watsi da naɗin Ibrahim Magu


'Yan majalisar dattawan Najeriya sun ki amincewa su tabbatar da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattali arzikin kasa ta'annati.
'Yan majalisar sun ce sun dauki matakin ne bayan wani rahoto ya nuna cewa shugaban na EFCC na da hannun a taken hakkin dan adam.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa da safiyar Alhamis ne 'yan majalisar suka gayyaci Mr Magu zauren majalisar inda suka yi ganawar sirri da shi, kuma a lokacin ganawar ne suka shaida masa cewa hukumar tsaron kasar ta mika musu wani rahoto da ke zarginsa da hannu wajen take hakkin dan adam.
A cewar majiyar, bayan haka ne shugaban riko na EFCC din ya yi musu bayani kan rahoton, amma ba su gamsu da bayanansa ba.
Daga bisani ne suka yi watsi da tabbatar da nadinsa a matsayin shugaban dindindin na hukumar.
Da ma dai an dade ana kai ruwa rana game da batun tabbatarwa da Mr Magu mukamin nasa, inda wasu ke zargin 'yan majalisar na jan kafa kan batun saboda shari'ar da ake yi wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki bisa zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa, zargin da ya sha musantawa.

Saturday, 10 December 2016

Sabuwar dambarwar siyasa a Gambia

adamabarrow.jpgGambia ta shiga cikin wata dambarwar siyasa, bayan shugaban kasar Yahya Jammeh ya janyen sanarwar da ya bayar a makon jiya, cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar.
Shugaba Jammeh ya ce ya na so a sake gudanar da zaben, duk da kiraye-kiraye da Tarayyar Afirka ta yi na ganin ya mika mulki cikin kwanciyar hankali.
Adama Barrow dai ya dage kan cewa shi ne ya yi nasara a zaben, sannan ya bukaci jama'ar Gambia da su yi zanga-zanga.
Duk da wannan dambarwa dai, babu wata hatsaniya a cikin unguwanni a Banjul, babban birnin Gambia.
Akasarin mutane sun yanke shawarar zama a cikin gidajensu, saboda fargabar yiwuwar barkewar tashin hankali.
An ga sojoji dauke da manyan bindigogi a muhimman wurare a babban birnin kasar.
Sabon zababben shugaban kasar, Adama Barrow ya yi watsi da batun sake gudanar da sabon zabe, sannan ya yi kira ga Shugaba Jammeh da ya amince da kayen da ya sha.
Ya ce ina sanar da ku cewa, shugaba bai barin gado bai da wani iko bisa doka na yayi watsi da sakamakon zaben, da yin kiran a sake gudanar da wani. Hukumar zabe ce kadai ke da ikon shirya zabe da sanar da wanda ya yi nasara. Haka kuma akayi, ni kuma na zama zababben shugaban kasa.
Tarayyar Afirka ma ta bayyana kin amincewa da sakamakon zaben da shugaba Jammeh ya yi yanzu a matsayin abin da ba zai yiwuwa.
Ministan harkokin wajen Senegal ma ya gargadi shugaba Jammeh da kada ya yi yunkurin tauye wa jama'ar kasar 'yancin su.
'Yan kasar ta Gambia dai yanzu, sun zura ido ne suna jiran ganin abin da zai faru.

Thursday, 8 December 2016

Fargaba kan jinkirin sakamakon zabe a Ghana

Majalisar tabbatar da zaman lafiya ta Ghana ta
yi kira ga hukumar zaben kasar EC da ta
gaggauta sanar da sakamakon zaben shugaban
kasar da aka yi a ranar Laraba.
Shugaban Majalisar Farfesa Emmanual Asante
ne ya yi kiran a wajen wani taron manema
labarai.
Farfesa Asante ya ce jinkiri wajen bayyana
sakamakon ya na haifar da fargaba, da rashin
tabbas, da kuma yada jita-jita mara amfani.
Ya kuma yi kira ga jam'iyyun siyasa da jama'ar
kasar su kwantar da hankula, su kuma jira
hukumar zaben kasar ta bayyana sakamako.
A nata bangaren, hokum zaben kasar ta ce
jinkirin na da nasaba da matsalolin da aka samu
a wurin yin zaben fiye da kima.
Hukumar ta ce don haka sai ta sake tantanace
duka sakamakon da aka kawo mata, kafin ta kai
ga bayyana wa.
Ita kuwa gamayyar kungiyoyin fararen ta cikin
gida da ta saka ido kan zaben, CODEO, ta ce
zaben yana da inganci.
CODEO ta kuma yi Allah-wadai da yadda
jam'iyyun siyasa ke bayyana sakamakon zabe,
gabanin hukumar zabe.
A wani labarin, bayanai sun ce jakadan Amurka a
Ghana ya kai ziyara ga dan takarar jam'iyyar
hamayya Nana Akuffo Ado a gidansa da safiyar
ranar Alhamis.
Gidan talabijin na Joy News mai zaman kansa ya
rawaito cewa mutanen biyu sun gana a asirce,
kuma babu wanda ya san abin da suka tattauna.

Tuesday, 6 December 2016

2016: Ana zaben kasar Ghana

A ranar laraba ne ake zaben shugaban kasa da
na 'yan majalisar dokokin kasar Ghana.
Shekaru 25 kenan da kasar Ghana ta koma
turbar mulkin Dimukradiyya, kuma wannan shi ne
karo na bakwai da al'umar kasar za su kada
kuri'ar zaben shugaban kasa.
A wannan zaben dai ana ganin fafatawar za ta fi
zafi tsakanin shugaba mai ci John Dramani
Mahama na jam'iyyar NDC da Nana Akufo-Addo
na jam'iyyar NPP.
Akwai kuma wasu 'yan takarar da za su wakilci
jam'iyyu hudu, da kuma indifanda.
Ba dai wannan ne karo na farko da Nana Akufo-
Addo mai shekara 72 ke tsayawa takarar
shugabancin kasar, karo na uku kenan da yake
neman kujerar.
Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin cewa
idan har ya sha kaye a wannan karo, to hakan
zai kawo karshen damawa da ake yi da shi a
siyasar kasar saboda shekarunsa.
A bangare guda kuma idan har Shugaba Mahama
ya fadi zaben, to shi ne zai zamo shugaban
Ghana na farko da ya yi wa'adin mulki sau daya
a tarihin dimukradiyyar kasar.
Idan kuma ya yi nasara, zai kafa tarihin zama
shugaba na farko farar hula da ya dade ya na
mulki a kasar tun bayan da Ghana ta zamo mai
jam'iyyun siyasa daban-daban.
Saboda shi ne ya karashe sauran wa'adin mulkin
marigayi John Atta Mills da ya rasu a shekarar
2012.

Friday, 2 December 2016

Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben Gambia

Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya sha kaye a
zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar
Alhamis.
Shugaban hukumar zaben Alieu Momar Njie ya
bayyana dan takarar 'yan adawa Adama Barrow a
matsayin wanda ya lashe zaben.
Mista Jammeh, wanda ya hau mulki a 1994, ya
amince da shan kaye, a cewar shugaban
hukumar zaben.
Ba a taba mika mulki a cikin ruwan sanyi a
Gambia ba tun bayan da kasar ta samu 'yancin
kai a 1965.
Mista Njie ya ce Mista Barrow ya lashe zaben na
ranar Alhamis da tazarar fiye da kuri'u 50,000.
Mista Jammeh, wanda ke ikirarin bin tafarkin
addini sau-da-kafa ya ce "zai shafe shekara
biliyan guda yana mulki idan Allah ya so".
Ya dai shafe shekara 22 a kan karagar mulkin
kasar, wacce ta dogara da 'yan yawon bude ido
wurin samun kudaden shiga.
Wakilin BBC a Gambia Umaru Fofana ya ce
Adama Barrow yana da farin jini matuka a wurin
matasa.
Wanene Adama Barrow?
An haifi Adama Barrow ne a shekarar 1965 a
wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin
nan na Basse a gabashin Gambia.
Ya koma birnin London a shekarun 2000,
kuma wasu rahotanni sun ce ya taba yin aiki
a matsayin jami'in da ke tsaron babban
kantin nan na sayar da kaya, Argos a
arewacin London a lokacin da yake karatu a
can.
Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda
ya koma kasuwanci a fanni gine-ginen
gidaje.
Jam'iyyun hamayyar da suka yi hadin gwiwa
ne suka tsayar da Barrow, mai shekara 51, a
matsayin mutumin da zai fafata da Shugaba
Jammeh.
Ya sha sukar rashin sanya wa'adi biyu na
kujerar shugaban kasar sannan ya soki
daurin da aka yi wa 'yan jam'iyyun hamayya.
Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari'a
ya samu 'yanci sannan 'yan jarida da kuma
kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin
albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka
ba.
Ya ce zai kafa gwamnatin gwamnatin hadaka
ta shekara uku wacce za ta kunshi jam'iyyun
hamayya idan ya ci zaben.

Wanene sabon shugaban Gambia, Adama Barrow?

An haifi Adama Barrow ne a shekarar 1965 a
wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin nan
na Basse a gabashin Gambia.
Ya koma birnin London a shekarun 2000, kuma
wasu rahotanni sun ce ya taba yin aiki a
matsayin jami'in da ke tsaron babban kantin nan
na sayar da kaya, Argos a arewacin London a
lokacin da yake karatu a can.
Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda ya
koma kasuwanci a fanni gine-ginen gidaje.
Jam'iyyun hamayyar da suka yi hadin gwiwa ne
suka tsayar da Barrow, mai shekara 51, a
matsayin mutumin da zai fafata da Shugaba
Jammeh.
Ya sha sukar rashin sanya wa'adi biyu na kujerar
shugaban kasar sannan ya soki daurin da aka yi
wa 'yan jam'iyyun hamayya.
Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari'a ya
samu 'yanci sannan 'yan jarida da kuma
kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin
albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka ba.
Ya ce zai kafa gwamnatin gwamnatin hadaka ta
shekara uku wacce za ta kunshi jam'iyyun
hamayya idan ya ci zaben.

Thursday, 1 December 2016

Dole mu hana Larabawa kwarara cikin Amurka —Trump

Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump
ya lashi takobin yin duk abin da zai iya yi wajen
kankare 'yan ta'adda daga Amurka.
Ya kara da cewa "wasu mutane da ba mu san
asalinsu ba suna kwararowa daga gabas ta
tsakiya, saboda haka dole ne mu dakatar da su."
Mista Trump ya sake nanata batun da ya rinka yi
a lokacin yakin neman zabe wato "america ce
gaba da komai."
Sai dai kuma mista Trump ya yi hani dangane da
kin jinin wani mutum saboda abin da ya yi imani
da shi da kuma amfani da mummunan furuci ga
mutane.

Tuesday, 29 November 2016

BH: Ina da ja kan yawan mutanen da suka mutu — Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce,
ko kadan ba dai-dai ba ne ace mutanen da suka
mutu a shiyyar Arewa maso gabashin kasar
sakamakon ayyukan Boko Haram, daga shekarar
2009 kawo lokacin da aka bayar da kididdigar,
dubu 10 ne.
A watan maris din da ya gabata ne dai shugaba
Muhammadu Buhari, ya ce 'yan kasar kimanin
dubu 10 ne suka rasu sakamakon rikicin na 'yan
kungiyar Boko Haram, tun daga shekara ta 2009.
Gwamna Kashim Shettima, wanda ya bayyana
hakan ga manema labarai a birnin Abuja, ya
kuma ce an yi hasarar kadarori a yankin na
kusan dala biliyan tara.
"A jihar Borno kadai an kona azuzuwa dubu
5335, an kona makarantun sakandare guda 38
sannan gidajen mutane dubu 956,453 aka kona."
In ji Shettima.
Sai dai kuma gwamnan ya ce, yanzu ba lokacin
ja-in-ja ba ne kan adadin mutanen da suka mutu.
Ya kara da cewa abin da ya kamata a mayar da
hankali a kai, shi ne, yadda za a tallafawa
mutanen da rikicin ya dai-daita.
Kashim Shettima ya kuma bayyana irin karfin
gwaiwar da yake da shi wajen samun tallafin
musamman a karkashin jagorancin shugaba
Muhammadu Buhari.
Sharhi, Usman Minjibir
Kusan za a iya cewa har kawo yanzu babu wata
kididdiga da wani zai iya bugar kirji ya ce ita ce
sahihiya kan adadin mutanen da suka mutu
sanadiyyar rikicin Boko Haram.
Ko da Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama sun sha
samun karo wajen fitar da alkaluma tsakaninsu
da bangarorin gwamnati musamman ma jami'an
tsaro.
A shekarar 2014, sai da Kungiyar Kare Hakkin
Bil'adama ta Amnesty International ta yi zargin
cewa an kashe mutane sau fiye da biyar din
kididdigar da gwamnatin shugaba Goodluck
Jonathan ta bayar a shekarar.
A lokacin dai gwamnatin shugaba Jonathan ta ce
mutane fiye da dubu 11 ne suka mutu tun daga
2009 lokacin da hare-haren kungiyar ya fara
ta'azzara.
Sai dai kuma mafi yawancin lokaci, a kan kasa
tantance mutanen da 'ya'yan kungiyar Boko
Haram suka kashe da kuma wadanda ake zargin
jami'an tsaron kasar da kisa.

Tinubu gagarabadan jam'iyar APC ne - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi
watsi da jita-jitar cewa shi da wasu shugabannin
jam'iyar APC suna takun saka da daya daga
cikin kusoshin jam'iyar Asiwaju Bola Tinubu.
Shugaba Buharin ya bayyana cewa irin wannan
jita-jita ba ta da tushe ballantana makama.
Babban mai bai wa shugaban kasar shawara kan
harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya ce
shugaban kasar ya nuna matukar bacin ransa
game da batun.
Ya ce shugaba Buhari ya sha tattaunawa da Bola
Tinubu tun kafin lokacin zaben gwamnan jihar
Ondo da kuma bayan zaben.
Tun bayan sabanin da aka samu a zaben fitar da
gwani na jam'iyyar a jihar Ondo, rashin jituwa
take kara fitowa fili a jam'iyyar.
Hakan ne ya sa wasu ke zargin cewa magoya
bayan Buhari na kokarin ganin bayan Tinubu,
wanda shi ne ya jagoranci kafa jam'iyyar.
Malam Garba Shehun ya kara da cewa duk wani
shaci-fadin da ake yi cewa shugaban kasa da
'ya'yan jam'iyyar na yunkurin ganin bayan Tinubu,
ba shi da tushe.
Ya kara da cewa shugaba Buhari ya dauki Tinubu
a matsayin wani gagarabadan dan siyasa, wanda
kowa ya san irin gagarumar gudummawar da
yake bayar wa wajen cigaban jam'iyya mai
mulki.
Malam Garba Shehu ya shawarci masu jita-jita
da su daina kokarin ganin kawo cikas tsakanin
shugaban kasa da Tinubu ko kuma jam'iyya.
Ya ce shugaba Buhari na alfahari da
''Jagaba'' (Tinubu) da kuma rawar da yake
takawa a cikin jam'iyyar.

Saturday, 26 November 2016

Fidel Castro ya fi kowa taka rawa a 'yancin Afirka— Jega

Shugabannin kasashen duniya da dama na ci
gaba da jimamin mutuwar tsohon shugaban
kasar Cuba, wanda ya kangare wa Amurka a
lokacin yakin cacar baka, Fidel Castro.
Shugaban China Xi Jinping ya ce 'yan kasar
China sun yi rashin babban aboki, yayin da
shugaba Putin na Rasha ya bayyana shi a
matsayin tauraron wani zamani.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ma ya ce
ya yi bakin ciki da jin labarin mutuwar tsohon
shugaban, dan juyin juya-hali, wanda yafi
kowanne dadewa yana shugabancin Cuba.
Cikin wata sanarwa, shugaba Buhari ya bayyana
Fidel Castro a matsayin zakakurin shugaba
wanda ya bunkasa fannonin ilimi da kiwon lafiya
da wasanni, da har wasu kasashen duniya ke cin
moriyarsu.
Ya kuma bayyana shi a matsayin babban abokin
nahiyar Afirka, wanda ya bayar da gagarumar
gudun muwa wajen neman 'yan cin kasashen
nahiyar.
A wata hira da BBC, fitaccen mai sharhi kan
harkokin yau da kullun a Najeriya, Mahmud Jega,
ya ce marigayi Fidel Castro ne mutumin da ya fi
kowanne bai wa nahiyar Afirka taimako na
samun 'yanci:
Shi ma Paparoma Francis ya bayyana mutuwar
Fidel Castro a matsayin wani abin bakin ciki,
sannan ya yi mushi addu'o'i.
Shugaba Jocob Zuma na Afirka ta Kudu ma ya
bayyana marigayin a matsayin mutumin da ya yi
tsayuwar daka don tabbatar da 'yan cin wadanda
ake dannewa a fadin duniya.
Sai yayin da wasu shugabannin ke yabawa Fidel
Castro, sabon zababben shugaban Amurka
Donald Trump ya bayyana shi ne a matsayin mai
kama karya da ya kuntata wa mutanen kasar shi.
A cikin wata sanarwa, Mista Trump ya ce abin
da za a rika tuna Fidel Castro da shi, shi ne
kuntatawa da tauye wa mutane hakkokinsu.

Thursday, 24 November 2016

Obasanjo na yi wa Buhari zagon-kasa - 'Yan majalisa

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ce tsohon
Shugaban kasar Olusegun Obasanjo na yi wa
gwamnatin Buhari zagon-kasa, bayan da ya
zarge su cin hanci da rashawa.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta bayyana
Obasanjo a matsayin "mutumin da ya fi kowa cin
hanci a tarihin kasar".
Mai magana da yawun majalisar Hon Abdulrazak
Namdas ya ce "Abin takaici ne ya fara nuna
halayyarsa ta kawar da gwamnati da aka sanshi
da ita tun shekara 1979".
Ya kara da cewa "Ya yi hakan ga tsofaffin
Shagabanni da suka hada da Shehu Shagari,
Janar Buhari, Janar Babangida, da kuma Janar
Abacha kafin ya daure shi a kurkuku".
Olusegun Obasanjo, ya furta wadansu kalamai a
ranar Laraba a Lagos, inda ya soki gwamnatin
Buhari saboda yadda take yi wa gwamnatoci
ukun da suka gabata, ciki har da ta sa, kudin
goro wajen zargin rashin iya jagoranci.
Ya kuma bai wa Buhari shawara da ya daina
korafi kan abin da ya wuce, inda ya ce tun da an
zabe shi ne domin ya gyara Nigeria, ya kamata
ya mayar da hankali kan gyara barnar da ya
tarar.
Sannan ya nemi ya taka wa 'yan majalisun kasar
birki, yana mai cewa majalisar ce dandalin cin
hanci da satar kudin al'umma.
Sai dai Namdas ya ce a lokacin Obasanjo ne aka
baje kudi a majalissar tarayya domin bayar da
cin hanci, saboda a sauke Kakakin Majalisar na
wancan lokaci Ghali Umar Na Abba.
Ya kuma tambayi 'yan Nigeria cewar "Shin har
kun manta lokacin da Obasanjo ya yi amfani da
karfin ikonsa, inda ya dunga karbar kudade daga
wajen 'yan kasuwa da 'yan kwangila domin gina
katafaren dakin karatunsa?
Ya kuma ce Obasanjo ya taimakawa Buhari a
lokacin yakin zabe, amma tun lokacin da ya
fahimci cewar gwamnati mai ci tana fama da
tattalin arziki, sai ya juya da nufin yi mata zagon
kasa.
Kawo yanzu Mista Obasanjo bai ce komai game
da kalaman na 'yan majalisar ba.