Friday, 20 January 2017

Home Gambia: Yahya Jammeh 'ya amince ya bar mulki,' ya kuma fice daga kasar

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


Zababben shugaban kasar Gambia ya ce Yahya
Jammeh ya amince ya sauka daga kan karagar
mulki, sannan kuma ya fice daga kasar.
Adama Barrow ya bayyana hakan ne a shafinsa
na Twitter bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa
domin shawo kan Mista Jammeh ya amince da
sakamakon zaben.
Tun da farko Shugaban Ζ™asar Guinea Alpha
Conde da na Mauritania Mohamed Ould Abdel
Aziz sun isa Banjul don ganawa da Yahya
Jammeh.
Shugaban hukumar ECOWAS, Marcel Alain de
Souza ya ce idan tattaunawar ta gaza samun
nasara, sojoji za su Ι—auki mataki.
Jawabin kama-aiki
A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba
Adama Barrow ya ce: "Daga yau (Alhamis), Ni ne
shugaban Ζ™asar Gambia ko ka/kin zaΙ“e ni ko ba
ka/ki zaΙ“e ni ba."
Ya ce "Wannan nasara ce ga Ζ™asar Gambia..
mulki a hannun jama'a yake a Gambia"
A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani
Ι—an Gambia da zai taΙ“a mantawa da ita... karon
farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta
sauya gwamnati ta hanyar Ζ™uri'a".
Shugaban Ζ™asa biyu
A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan
mulki ya Ζ™are, ko da yake majalisar dokokin Ζ™asar
ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.
'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke
zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka
fice zuwa wasu Ζ™asashe maΖ™wabta saboda tsoron
Ι“arkewar rikici.
Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da
aka yi cikin watan Disamba.
Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye
sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga
bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba
saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai
a zaben.
Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar
sakamakon zaben.

No comments:
Write Comments