Friday 2 December 2016

Home Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben Gambia

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya sha kaye a
zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar
Alhamis.
Shugaban hukumar zaben Alieu Momar Njie ya
bayyana dan takarar 'yan adawa Adama Barrow a
matsayin wanda ya lashe zaben.
Mista Jammeh, wanda ya hau mulki a 1994, ya
amince da shan kaye, a cewar shugaban
hukumar zaben.
Ba a taba mika mulki a cikin ruwan sanyi a
Gambia ba tun bayan da kasar ta samu 'yancin
kai a 1965.
Mista Njie ya ce Mista Barrow ya lashe zaben na
ranar Alhamis da tazarar fiye da kuri'u 50,000.
Mista Jammeh, wanda ke ikirarin bin tafarkin
addini sau-da-kafa ya ce "zai shafe shekara
biliyan guda yana mulki idan Allah ya so".
Ya dai shafe shekara 22 a kan karagar mulkin
kasar, wacce ta dogara da 'yan yawon bude ido
wurin samun kudaden shiga.
Wakilin BBC a Gambia Umaru Fofana ya ce
Adama Barrow yana da farin jini matuka a wurin
matasa.
Wanene Adama Barrow?
An haifi Adama Barrow ne a shekarar 1965 a
wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin
nan na Basse a gabashin Gambia.
Ya koma birnin London a shekarun 2000,
kuma wasu rahotanni sun ce ya taba yin aiki
a matsayin jami'in da ke tsaron babban
kantin nan na sayar da kaya, Argos a
arewacin London a lokacin da yake karatu a
can.
Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda
ya koma kasuwanci a fanni gine-ginen
gidaje.
Jam'iyyun hamayyar da suka yi hadin gwiwa
ne suka tsayar da Barrow, mai shekara 51, a
matsayin mutumin da zai fafata da Shugaba
Jammeh.
Ya sha sukar rashin sanya wa'adi biyu na
kujerar shugaban kasar sannan ya soki
daurin da aka yi wa 'yan jam'iyyun hamayya.
Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari'a
ya samu 'yanci sannan 'yan jarida da kuma
kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin
albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka
ba.
Ya ce zai kafa gwamnatin gwamnatin hadaka
ta shekara uku wacce za ta kunshi jam'iyyun
hamayya idan ya ci zaben.

No comments:
Write Comments