Kamar yadda muka fada a baya, wannan zubin jadawali ya yi nazari ne na musamman ta hanyar duba da rawar da kowace jarumi ya taka a finafinan da suka fito a 2016, ya’alla bangaren fada, jarumta, barkwanci da sauran fannoni.
.
1- Hadiza Aliyu (Gabon):
.
Fim din BASAJA GIDAN YARI kadai ya isa dora shahararriyar harumar a matakin na farko. Ba tantama wannan jaruma ta nuna kanta a cikin shirin. Babu wani abu da za a iya cewa game da ita sai sambarka. Hakika babbar nasara ce a wajen jarumar da ta zamo cikin jerin wadanda suka taka rawa a cikin fim din Basaja. Ta shiga tarihin da ba za a manta da ita ba, domin kusan kowa ya fi ganin ta fiye da sauran jaruman.
.
Yanayin yadda Zee take wasa kwakwalwarta a duk lokacin da take kokarin gano halin da Jabir yake ciki akwai mamaki matuka. Domin idonta, bakinta, kunnenta da duk ilahirin jikinta yana nunawa dan kallo cewar lallai abinda take fada haka yake. Hadiza Gabon ba daga nan ba, hakika ta ciri tutar da za ta iya lashe kowace irin kyauta ta girmamawa.
.
Jarumar haifaffiyar kasar Gabon, ta shigo masana’antar finafinai da kafar dama, domin kuwa ta samu nasarar bankwarawa tare hawa bigiren da dukkan wani shahararre yake buri.
.
Sai dai ba wai daukakar da Allah ya yi wa jarumar ko kuma kwarewa da ta yi a harkar fim bane ya fi ja hankalin mutane ba, sai don wasu kyawawan dabi’u da Allah ya azurta jarumar da su, wadanda da yawan al’umma ba su da su, ba ma kawai abokan sana’arta na fim ba. Domin Hadiza ta kasance mai tausayi da jin kan al’umma domin abin hannunta bai dame ta ba.
.
Ta taba fadin: “Na samu nasarori da kyaututtuka da dama, ciki har da kyautar tauraruwar taurari mata da kuma kyautar da gwamnan Kano ya bani har ma kuma da kyautar da na samu a da fim din Ali ya ga Ali,” in ji Hadiza Gabon.
.
Fitacciyar jarumar ta lashe kyautar ‘yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim, a wani bikin bayar da kyaututuka ta Africa Films Awards na shekarar 2016 wanda jaridar Africa Boice take gudanarwa a kasar Ingila.
.
2- Hafsat Idris:
.
A rana irin ta yau, watau 16 ga watan Dismabar 2015, jarumar ta fara daukar kyamara a farfajiyar shirya finafinan Hausa, inda ta fito a cikin fim din BARAUNIYA. Duk da cewa shi ne fim din na farko, amma tun kafin ya fita kasuwa jarumar ta fara samun yabo daga masana harkokin finafinan Hausa.
.
Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da sakon ake labarinta. Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka dora ta.
.
Da farko an yi tsammanin Hafsat Idris za ta rika fitowa ne a matar aure kawai, amma daga bisani sai kwarewarta ta fito fili ta yadda take iya fitowa a finafinai kala-kala.
.
Masana’antar Kannywood ta dade ba ta samu jaruma da cikin lokacin kankani ta shige sahun takwarorinta ba, domin an saba ganin yadda wasu jaruman ke daukar shekaru kafin ‘yan kallo su gamsu cewar kwararru ne.
.
Babban abin da ya fi jan hankalin makallata finafinan Hausa game da jarumar shi ne, irin salon kifta idonta a lokacin da take magana. Wasu na ganin jarumar ta fito da nata irin salon ne domin ta kwashi magoya baya, wanda yanzu haka take samunsu a kullu yaumin.
.
Finafinan da suka sanya jarumar ta haye sahu na biyu a wannan jadawali sun hada da; Furuci, Dan Kurma, Maya, ‘Yar Fim, Wazeer da sauran su.
.
3- Rahma Sadau:
.
Duk ba dakalar korar jarumar da ta kunno kai a karshen shekarar nan, hakan bai hana Rahma samun kanta a jerin jarumai mata da suka haska a 2016 ba, domin za a iya cewa jarumar ta samu nasarar tsallake Arewacin kasar zuwa Kudancin Nijeriya, Afrika da ma kasashen duniya.
.
Ta wata fuskar, za a iya cewa korar Rahma daga masana’antar Kannywood gobar titi ce a Jos, domin yanzu ba jarumar Hausa ba ce, tuni ta fara mafarkin fitowa a finafinan industirin da babu kamarta watau Hollywood.
.
Tun kusan farkon shekarar nan, jarumar ta fara fuskantar kalubale daga masu ruwa da tsaki a farfajiyar Kannywood, sakamakon wani fim da ta fito a ciki mai suna ANA WATA GA WATA, inda ta yi wani kalami da ake ganin bai dace ba, an so dakatar da fitar fim din, amma daga bisani aka sake shi kasuwa, duk da an samu matsaloli da dama da suka hada da kame jigajigan da suka hadu wajen samar da shirin.
.
Rawar da jaruma Rahma Sadau ta taka a fim din Ana Wata Ga Wata ta fita daban, domin ta janyo mata suna da shahara a fadin Nijeriya.
.
Bullar labarin korar ta kuwa, shi ne labari na farko na wani jarumin Kannywood da ya zagaya duniya.
.
Jim kadan bayan balahirar, Rahma ta samu gayyata daga shahararren mawaki Akon zuwa kasar Amurka, inda ta shafe tsawon kwana 10 tana warkajami a tsakiyar turawa.
.
Hakika shekarar 2016 ta zowa jarumar da abu biyu; farko kalubalen kora daga abokan aikinta na asali watau Kannywood, da kuma nasarar samun gayyata zuwa Hollywood. Yanzu haka akwai fim dinta na Turanci mai suna SONS OF THE CALIPHATE da ake haskawa a gidan talabijin na Ebony Libe.
.
4- Nafisa Abdullahi:
.
GUGUWAR SO, fim ne da ya yi masifar kyau, musamman da ya kasance labarin soyayya. Hakika jarumar ta tuna da irin rawar da ta taka a fim din da ya zama silar zamowarta shahararriya a duniya finafinai watau, Sai Wata Rana.
.
Jarumar ta haskaka sosai a wannan shekara, sunan ta bai boyu ba sam, musamman bayan ta kaddamar da gidauniyar tallafawa gajiyyayu kwanan baya.
.
Nafisa jaruma ce da ta kware wajen iya salon aktin na soyayya ko kuma salihanci. Tana yin kyau kwarai idan ta fito a matsayin wadda ake zalunta. A shekarar nan ta fito a shirin fim mai dogon zango wanda Darakta Malam Aminu Saira ya bada umarni, watau LABARINA. Tallar shirin kawai aka gani, amma tuni mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu game da rawar da Nafisa ta taka.
.
Game da gidauniyar da ta bude kuwa, Nafisa ta ce dalilin da ya sa ta kaddamar da wannan Gidauniya ta kuma fara da taimakon talakawa shi ne, bisa rahoto da ta samu na irin matsaloli da al’umma ke fuskanta musamman na rashin dan abin da za a kai bakin salati. A cewarta, lokaci ya yi da ya kamata mutane irinsu su fara taimakawa jama’a ta hanyoyin da suke ganin za su iya.
.
“A duk lokacin da mutum ya kai matsayin da jama’a suke kaunarsa, musamman dan fim da yake alfahari da jama’a, kasancewar su ne ke siyan finafinan da yake fitowa a ciki. Ya dace ya dauki matakin bin hanyoyin da zai tallafa masu, ko ya samu lada a wajen ubangiji.” In ji Nafisa.

5- Jamila Umar (Nagudu):
.
Gwana ta gwanaye, wadda aka hakikance tana hawa kowane irin rol, kuma ta aiwatar da shi yadda yake a rubuce, ko ma fiye da haka. An ga haka finafinai sama da 100 da jarumar ta fito ciki a tsawon shekarun da ta yi a Kannywood.
.
Nagudu ta kware sosai a fagen nishandatar da mutane, musamman a finafinai masu ma’ana da suke dauke da sako. Babu shakka jarumar tana ci gaba da rike kambinta na jarumar da masana’antar ke alfahari da ita.
.
A shekarar 2016, jarumar ta haska sosai finafinai masu matukar kyau, kadan daga akwai INDON BIRNI, wanda ci gaba ne na Indon Kauye, shiri ne ba barkwanci da ya nishadantar da ‘yan kallo matuka.
.
Rawar da Nagudu ta taka na ‘yar kauye maras wayo, uwar shiririta da shirme ta kayatar matuka, domin idan mutum yana kallo ita kawai yake so a hasko.
.
Har ila yau fim din Zinaru, wanda shi ma jarumar ta fito a matsayin kwadayayyiyar kaza, Jamila ta taka rawa kwarai da gaske, domin ‘yan kallo sun kara tabbatar da cewa Nagudu ba daga nan ba wajen aktin.
.
6- Fatima Abdullahi (Washa):
.
Jaruma mai tashe, wadda cikin kankanin lokaci ta shiga sahun manyan jaruman da ake labarinsu game da kwerawa da suke da ita a wajen amfani da kwalkwalwa a farfajiyar shirya finafinai.
.
Fim din GIDAN ABINCI, wanda Kamal S. Alkali ya bada umarni, a shi jaruma ta kara rikita tunanin mutane game da basirar da take da ita. Shirin na barkwanci ne, inda Washa ta fito a matsayin ‘yar sandar boge. Ta yi matukar kyau sanye da kayan jami’an ‘yan sanda tamkar ta gaske. Ta nishadantar da al’umma ta cikin wani shiri da ya hada jarumai irin su; Nuhu Abdullahi, Sulaiman Bosho da Rabi’u Daushe.
.
An ga yadda jarumar ta baje kolin basirarsa a fim din BASAJA GIDAN YARI. Darakta Falalu ya nuna cewar shi kwararre ne da ya iya jan zarensa a fannin bada umarni. Ya wahalar da mutane matuka kafin ya bayyana wace ce asalin Washa a labarin. A bangaren Fati kuwa, kusan gaba daya za a iya cewa fim din nata ne, domin tana bayyana kwata-kwata hankulan mutane ya karkata zuwa gare ta.
.
Da ma Fati Washa ba daga nan ba, sai kuma ga shi ta shiga tsakiyar tsararrakinta, inda ta baje kolin tata basirar, ta kuma samu shiga wannan jerin na matan da suka fi haskawa a shekarar 2016.
.
7- Maryam Gidado:
.
TALAKA BAWAN ALLAH, fim ne da Babban Darakta Sunusi Oscar 442 ya bada umarni. Labarinsa ya nuna yadda wani attajiri ke wadaka da dukiya shi da ‘ya’yansa, ba tare da ya san cewar dukiyar ba tasa ba ce.
.
Gidado da ta saba fitowa a matsayin jarumar da take shan wahala a hannun mugaye, wannan karo ta fito a rol din da ita ce ta uzzarawa wata saboda wanda take so yana nuna ba ya son ta, waccan yake so.
.
An ga yadda take nuna salon fitsara da rashin kunya, zobaro baki da yin daurin dankwalin ture ka ga tsiya. Har ila yau, akwai tallan wani fim mai suna Nana Habiba, wanda shi ma a ciki jarumar ta yi bajinta sosai, musamman da yake ta fito a matsayin wadda aka sace ake kuma kokairn yanka ta.
.
Babu shakka wannan jarumar har yanzu tana jan zarenta yadda ya kamata, sam ta ki yarda ya tsinke.
.
8- Aisha Aliyu (Tsamiya):
.
Duk da cewar jarumar ba kowane rol take karba ba, tana tsayawa ta zaba tare darjewa, ta yi finafinai masu ma’ana wadanda suka birge ‘yan kallo.
.
Wasu finafinan ta fito ita kadai, yayin da wasu kuma suka fito da yawa. Misali MIJIN BIZA na kamfanin Abnur, wanda Abdul Amart mai kwashewa ya shirya, Falalu A. Dorayi ya bada umarni akwai ‘yan wasa da yawa. Duk da ta fito a tsakiyar jarumai mata da yawa, hakan bai hana ta daga yatsa tare da nuna tata bajintar ba.
.
Har ila yau fim din ‘Yar Amana wanda suka fito tare da jarumi Adam A. Zango da Isah Adam (Feroz Khan), an ga yadda a cikin wannan shiri jarumar ta kara bayyana kanta a matsayin kwararriyar da duniyar finafinai ke alfahari da ita
.
9- Sadiya Adam:
.
Farin jinin da ta samu cikin kankanin lokaci ya yi matukar bawa masu kallon finafinan Hausa mamaki. Jarumar haifaffiyar garin Maiduguri a jihar Borno, ta shigo masana’antar fim da kafar dama, domin sunanta ya fara amo a bakuna makallata finafinan Hausa.
.
Shekarar 2016 abin alfahari ce ga Sadiya Adam, domin ta fito a cikin finafinan masu kyau, wadanda suka zamo mata wani mataki na darewa duniyar shahara, tuni ta fara samun tallace-tallace daga kamfononi a nan gida Nijeriya.
.
Finafinan da fito a wannan shekara sun hada da; Bani Ba Aure, Hali Daya, Auren Manufa, Hasashe, Gwarzon Shekara da Wutar Gaba.
.
Zuwa yanzu an zuba ido domin ganin yadda za ta kaya a finafinan da jarumar ta saka Jammu za ta yi a sabuwar shekara mai kamawa.
.
10- Hannatu Bashir:
.
Mutane da yawa sun yi mamakin ganin yadda jarumar ta lashe kyautar gwarzuwar mai taimakawa jarumar a gasar da Mujallar City People ke gabatarwa duk shekara a Legas.
.
Hannu ta lashe wannan kambi na 2016 sakamakon irin rawar da ta taka a finafinan Hausa masu kyan gaske.
.
Hakika wannan jaruma ba za ta man da shekarar 2016, domin a cikinta ne ta samu damar tattaki har zuwa birnin Ikko ta karbo kambi da kowace jaruma ke mafarkin samu.a samu damar tattaki har zuwa birnin Ikko ta karbo kambi da kowace jaruma ke mafarkin samu.
.
Ita ma an zuba ido domin ganin wace gudunmawa za ta bayar finafinanta na nan gaba.
.
Source By Leadership

No comments:
Write Comments