Sunday 13 November 2016

Home Muna bayan Atiku Abubakar - Mutanen Adamawa

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Mutanen Adamawa na kokarin tunzura
Alhaji Atiku Abubakar ya tsaya takarar
shugaban kasa
– Mutanen jihar Adamawa sun ce suna
bayan Atiku Abubakar
– Magoya bayan Atiku Abubakar sun ce ya
taka rawar gani lokacin yana Mataimakin
Shugaban Kasa
Atiku Abubakar da Jibrilla Bindow
Mutanen Adamawa sun ce su fa suna bayan
Alhaji Atiku Abubakar idan zai tsaya takarar
Shugaban Kasar nan. Gwamnatin Jihar tace
tana bayan Atiku Abubakar dari-bisa-dari
wajen ganin ya zama Shugaban Kasar
Najeriya.
Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin
Jihar Adamawa, Abba Jimetea ya bayyana
hakan kwanan nan a wajen buda wata
sabuwar hanya da Gwamnatin ta gina daga
Girei-Wuro-Bokki. Abba Jimeta yace
daukacin Mutanen Adamawa sun ce sai
Atiku Abubakar.
Abba Jimeta, wanda Shugaban Ma’aikatan
Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa, yace da
zaran Alhaji Atiku Abubakar yace zai tsaya
takarar Shugaban Kasa, to kowa a Jihar zai
tashi tsaye wajen ganin an cika wannan buri.
Abba Jimeta yace kaf Gwamnatin Adamawa
tana bayan Atiku Abubakar.
Alhaji Atiku Abubakar, Turakin Adamawa ya
rike Mataimakin Shugaban Kasar nan na
shekaru takwas, lokacin Shugaba Obasanji.
Mutanen Adamawa sukace yayi abin a-zo-a-
gani musamman a bangaren Tattalin arziki,
Don haka suna bayan sa idan zai tsaya
takara. Atiku Abubakar yana Garin Benin,
wajen nadin sabon Gwamna, ba a sani ba ko
zai tsaya takara ko ba zai tsaya ba v  

No comments:
Write Comments