Thursday, 11 April 2019

ALIKO DANGOTE: 'YADDA ZA KA ZAMA KAMAR NI'

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote ya bai wa matasan nahiyar shawarwari idan suna son zama kamarsa.
Hamshakin attajirin ya bayyana hakan ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da attajirin nan dan kasar Sudan Mo Ibrahim a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa karshen makon jiya.
Wani mahalarcin taron ya tambayi attajirin wadanne bangarori zai fi mayar da hankali idan a ce yana a matsayin dan shekara 21 da haihuwa kuma yana shirin fara kasuwanci.
Dangote ya ce zai fi mayar da hankali ne a harkarkokin sadarwa na zamani da kuma aikin gona.
"Wadannan ne bangarori biyu da za su fi kawo riba," in ji shi.
Sai dai daga nan ya ja kunnen matasa game da dabi'unsu bayan fara kasuwanci musamman 'yan Afirka.
Ya ce muna "kashe ribar da ba ta kai ga zuwa hannunmu ba."
"Da zarar ka fara kasuwanci kuma kasuwancin ya fara samun ci gaba, maimakon ka yi ta kara uwar kudin, sai mutum ya fara kashe kudin da tunanin ribar za ta ci gaba da zuwa," kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa:"Dole ne mutum ya natsu saboda akwai kalubale nan da can."
Attajirin ya ce bai kamata mutum ya fara kashe kudi ba ba-ji-ba-gani ba.
"Saboda idan ka sayi manyan abubuwan more rayuwa (kamar motocin kawa) za su dauke maka hankali daga harkokin kasuwancinka."
Daga nan, ya bayar da misali da kansa, inda ya ce "ba ni da wani gidan shakatawa mallakina a ko ina a fadin duniya."
"Amma akwai wasu daga cikin ma'aikatana da suke da gidan shakatawa a birnin Landan."
'Najeriya za ta zama kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur'
Dangote ya ce aikin gina matatar man da yake yi a jihar Legas a Najeriya zai ci kimanin dala biliyan 12 zuwa 13.
Ya ce idan aka kammala gininta za ta rika samar da gangan mai 650,000 a kowace rana.
Har wa yau, ya ce idan aka kammala aikinta, hakan zai mayar da Najeriya kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur a yankin kudu da saharar Afirka.
"Babban kalubalen da muka fuskanta lokacin fara gina matatar mai shi ne sai da muka gina tashar jirgin ruwa ta musamman saboda babu wata tashar jirgin ruwa a kasar da za mu iya shigo da manyan na'urorinmu ta ita."
A bangaren siminti, Dangote ya ce a bana Najeriya za ta kasance kasar da ta fi kowacce fitar da shi a nahiyar Afirka.
BBChausa.

WANI MATASHI YA SHA ALWASHIN KARBAR BASHIN BANKI DAN ZUWA GURIN NAFISA ABDULLAHI SU YI WANI ABU

Soyayya takan sa mutum yayi abinda shi kanshi zai baiwa kanshi mamaki, musamman idan ya kamu sosai, kusan hakannne ke shirin faruwa da wani matashi da yace jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi na birgeshi.
A sakon daya aika mata ta Twitter,yace ana girma ana rage kyau amma Nafisa kullun kara kyau kike, sai na amshi bashin banki dan inzo in ganki mu dauki hoto.
Ban taba ganin mace me kyanki ba.
Nafisar dai tace ba fashin baki, hoto kawai.


JARUMI ALI NUHU YA MAKA ADAM A ZANGO KOTU

A yaune dai shahararren jarumi kuma mai fada aji a masana’antar kannywood wato jarumi Ali Nuhu ya maka fitaccen jarumi Adam A Zango a kotu bisa abinda ya kira bata suna da cin mutunci da Zango yayi masa.
A takardar sammaci da kotun ta aikewa da jarumi Adam zango a yau alhamis, kotun ta bukaci da ya bayyana a gabanta a ranar litinin mai zuwa (15/04/2019) don amsa ko kare kansa bisa wannan tuhuma da jarumin yake masa.
A yayin da jarumi Adam A Zango ya karbi wannan sammaci, sai ya maida martani kamar haka:
Idan baku manta ba a cikin yan kwanakin nan ne dai aka samu rashin jituwa tsakanin manyan jaruman guda biyu inda har ta kaiga jarumin Adam Zango ya rinka zagin Ali Nuhu.
Ko kuna ganin wannan mataki da jarumi Ali Nuhu ya dauka yayi daidai duba da yadda wasu jaruman ke daukar doka da hannunsu idan aka yi musu ba daidai ba?

Wednesday, 10 April 2019

KARSHEN TIKATIKA TIK WANNAN SHINE VIDEO CHATTING DIN AMINA AMAL DA HADIZA GABON DAGA FARKO HAR KARSHE

Idan baku manta ba kwanan nan anata samu rigingimu tsakanin jaruman kannywood wanda yakai ga Amina Amal da hadiza gabon suma suka samu sabani wanda Amina Amal ta wallafa a shafinta na instagram akan hadiza gabon yar madigo ce
Hakan yasa hadiza gabon tasa aka dauko mata Amina inda ta tursasa ta saita bayyanawa duniya gaskiyar lamarin
Saidai wassu mutane suna cewa tsorone yasa Amina ta taki fadan gaskiyar lamarin a video domain hadiza Gabon har dukan ta take
To yau muna tafe muku da video chatting nasu daga farko har karshe dan gane waye ke da gaskiya a cikin su

Downlord