Shahararren kamfanin shirya finafinan Hausa, Sarai Mobies, ya fara shirya wani kayataccen fim wanda a tarihin masana’antar za a iya cewa ba a taba yin irinsa ba, domin ana sa ran za a dauki kusan wata shida kafin a kammala shutin dinsa gaba daya.
Shi dai wannan sabon shirin mai suna Labarina, ya samo asali ne daga kiraye-kirayen da manyan masana harkar fim na duniya ke yi na ganin Kannywood ta fara shirya finafinai masu dogon zango watau siris (Series), ta yadda za a rika goyayya da sauran masana’antun duniya.
Finafinan Siris, wanda a yanzu suke tashe a kasuwar fim ta duniya, ba a saba yin su bisa tsari na yadda za su dace a manyan finafinan kasashen duniya a masana’antar Hausa ba, shi ya sa ake ganin wannan shi ne karo na farko da wani darakta ya bugi kirji tare da kaddamar da shirin fim wanda mai kallo zai shafe kusan awa 24 yana kallo bai kare ba.
Da yake bayani game da makasudin yin fim din, kwararren darakta Malam Aminu Saira, ya ce ya yi wannan tunani ne bisa irin kiraye-kirayen da masana da kuma ‘yan kallo ke yi na son a yi fim mai dogon zango, inda ya ce, “duniya yanzu ta ci gaba, harkar fim gudun yada kanin wani ake yi, shi ya sa muka yi babban shiri ta hanyar bullo da irin wannan salo da zai canja tafiyar Kannywood.”
“Finafinan Siris suna samun karbuwa a duniya, tuni sauran masana’antu sun yi nisa da wannan tsarin tun shekrau aru-aru. Duk da cewa a baya an yi, amma wannan karo ba irin wanda aka saba gani ba ne.” In ji shi.
Har ila yau ya kara da cewa, fim din Labarina, ya samu kayatacce labari, wanda wata matashiyar budurwa ke bayar da labarin irin tashin hankali, matsaloli da kalubalen da ta fuskanta a rayuwarta.
Ya ce, “jaruman fim din suna da yawan gaske, lokaci ne zai bai wa ‘yan kallo damar ganin su daya bayan daya. Kasanewar labarin yana da tsayi, dole ne a ga jarumai kala-kala, da wadanda ake damawa da su a Kannywood da kuma sabbin fuska.
Haka zalika ya ce daga cikin manufar shirya irin wannan katafaren fim akwai batun bunkasa harkokin tattalin arzikin Kannywood. A cewarsa, fim irin wannan mai tsayi, da yake bukatar mutane da yawa, dole ne zai taimaka wajen samawa dimbin matasa ayyukan yi, tun da ba fim ne da za a yi shi na awa biyu ko uku ba.
“Yawan mutane shi ne kasuwa, kuma daga cikin burinmu akwai batun kara bunkasa tattalin arziki da kasuwancin fim. Saboda haka Labarina zai tattara mutane masu yawan gaske, wanda hakan zai kara janyo wasu sabbin mutane cikin masana’antar domin sama musu ayyukan yi.
Da yake amsa tambaya kan ko wata kwangila kamfanin nasa ya samu domin shirya shirin, Saira ya ce, sam abin ba haka ba ne, inda ya jaddada cewa fim din hadin guiwa da Saira Mobies da kuma Rainbow, watau kamfanin da zai yi dillanci da kasuwancin fim din.
Sai dai kamar yadda ya shaida mana, tuni wasu gidajen talabijin sun fara kai wa shirin farmaki ta hanyar bayyana sha’warsu na sanya hannun jari, amma Malam Saira ya shaida musu aikin gama ya gama, sai dai su tari gaba, domin wannan shiri kamfanin Rainbow ne zai yi kasuwancinsa.
No comments:
Write Comments