Saturday, 3 December 2016

Home Super Falcons ta lashe kofin Afirka na bana a Kamaru

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super
Falcons, ta lashe kofin nahiyar Afirka, bayan da
ta doke ta Kamaru da ci 1-0 a karawar da suka
yi a ranar Asabar a Kamaru.
Da wannan sakamakon Nigeria wadda ke rike da
kofin, ta lashe karo na 10 jumulla a tarihi, inda ta
fara daukar kofin farko a shekarar 1991.
Wannan ne karo na hudu da Nigeria ke cin
Kamaru a wasan karshe a gasar kofin nahiyar
Afirka ta Mata.
Nigeria ta fara cin kamaru a wasan karshe 2-0 a
gasar farko a shekarar 1991 a Legas, sannan ta
doke Kamaru 4-0 a wasa na biyu a shekarar a
Yaounde.
Super Falcons ta kara doke Kamaru da ci 5-0 a
wasan karshe a shekarar 2004, sannan ta kara
samun nasara da ci 2-0 a wasan karshe a gasar
da aka yi a 2014.
Nigeria ta dauki kofin a shekarar 1991, 1995,
1998, 2000, 2002, 2004, 2006, 2010 da kuma
2014, inda Equotorial Guine ta dauka sau biyu a
shekarar 2008 da kuma 2012.
Za a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta mata a
shekarar 2018 a Ghana.

No comments:
Write Comments