Thursday, 10 November 2016

Home 'Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya'

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya
tsallake kuri'ar yanke kauna da 'yan Majalisar
dokoki suka kada a kansa.
Babbar jami'yyar adawa ta Democratic Alliance
ita ce ta gabatar da kudurin kan abin da ta kira
sakacin da yake yi a shugabancin kasar.
Jamiyya mai mulki ta ANC da ke da rinjaye a
Majalisar ta goyi bayan shugaba Zuma.
Wakiliyar BBC ta ce wannan shi ne karo na uku a
wannan shekarar da aka kada kuri'ar yanke
kauna akan shugaba Zuma kuma jamiyyar ANC
mai mulki dake da rinjaye a majalisar dokoki ta
shawo kansu ba tare da wata matsala ba.

No comments:
Write Comments