Thursday, 3 November 2016

Home Nigeria: Sayen kayan daki ya gagari wasu iyaye a Kano

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Wasu iyaye a Nigeria sun ce sun kasa saya wa
'ya'yensu mata kayan daki saboda tsadar
rayuwar da ake fama da ita.
A kasar Hausa iyayen budurwa ne kan saya wa
'yarsu kayan daki da suka hada da gado da
kujeru kafin tarewa a gidan aurenta.
Sai dai, a baya-bayan nan, matsin tattalin arziki
da ake fuskanta a Najeriya ya janyo hauhawar
farashi da raguwar harkokin saye da sayarwa.
Su ma kafintoci na kokawa kan karancin kasuwar
da suke fuskanta saboda yawan daga bukukuwan
aure, sakamakon rashin halin sayen kayan daki.
Za ku iya sauraron rahoton da wakilinmu
Mukhtar Adamu Bawa ya hada mana a farkon
wannan labarin.

No comments:
Write Comments