Monday, 31 October 2016

Fifa ta kirkiro kyautar karrama 'yan kwallo

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta kirkiro
sabuwar kyautar karrama 'yan wasan kwallon
kafa da suka yi fice, bayan da ta raba gari da
masu shirya kyautar Ballon d'Or.
Hukumar za ta sanar da wadanda za su lashe
kyautuka takwas da ta ware tsakanin maza da
mata masu taka leda da wadanda suke bayar da
gudunmawa a fagen tamaula a ranar 9 ga watan
Janairu a Zurich.
Fifa ta fara karrama 'yan wasa da jami'ai da
suka taka rawar gani a fagen tamaula a shekarar
1991 zuwa 2009 daga nan ne ta hada gwiwa da
mujallar Faransa mai gudanar da kyautar Ballon
d'Or.
A karkashin wannan sabon tsarin za a fitar da
zakarun bana ta hanyoyi biyu.
Hanyar farko kashi 50 cikin 100 zai kunshi
kuri'un kyaftin da kociyoyin tawagar kwallon kafa
da suke mambobi a hukumar kwallon kafa ta
duniya Fifa.
Haka kuma za a bai wa jama'a damar yin zabe
ta intanet da kuma manyan 'yan jarida 200 da
suke fadin duniyar nan.
A ranar Juma'a Fifa za ta bayyana 'yan wasa 23
da suke kan gaba a murza-leda, sannan ta ware
guda uku a ranar 2 ga watan Disamba, wadanda
daga cikinsu za a zabi zakaran bana.
Ga jerin kyautukan da za a lashe a shekarar
2016:
1. Dan wasan da ya fi yin fice
2. 'Yar wasan da ta fi yin fice
3. Mai horarwa da ya fi kowa iyawa
4. Wadda ta fi iya jan ragamar kwallon kafa ta
mata
5. Kwallon da aka ci mafi kayatarwa
6. Kyautar wasa ba da gaba ba
7. Kyautar magoya baya da suka fi da'a
8. 'Yan wasa 11 da babu kamarsu a cikin fili

Nigeria: Satar Mutane ta yi kamarin da ba a zato

Wani dan majalisar wakilan Najeriya ya ce
matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa
a wasu jihohin kasar ta yi kamari fiye da yadda
kowa ke tsammani.
Hon. Abdulmalik Zubairu daga jihar Zamfara -
daya daga cikin jihohin da ke fama da wannan
matsalar- ya ce a mazabar da yake wakilta kadai
an sace mutane kusan bakwai a cikin makonni
biyu kawai.
Ya ce yanzu masu garkuwa da mutanen kan bi
mutane har gidaje ko gonakkinsu su sace su.
Shi ma da yake zantawa da BBC bayan yin gyara
da dokar hukunta masu satar mutane domin ta
hada da hukuncin kisa, Kakakin Majalisar
Dokokin jihar Kano Honourable Kabiru Alhassan
ya ce ko a kudancin jihar ma ana bin mutane har
gona ana garkuwa da su.
Wakilin BBC a jihar ta Kano ya ce wannan
matsalar na sa har mazauna wannan yankin na
kauracewa gidajensu.

Pepe na Real Madrid zai yi jinya

Mai tsaron baya na Real Madri, Pepe, zai yi
jinyar makonni, wanda hakan zai sa ba zai buga
karawar da kungiyar za ta yi da Atletico Madrid
da Barcelona ba.
Pepe mai shekara 33, dan kwallon tawagar
Portugal, ya yi rauni ne a wasan da Madrid ta ci
Alaves 4-1 tun kafin a je hutun rabin lokaci a
ranar Asabar.
Shi ma dan wasan Real Madrid mai tsaron baya,
Sergio Ramos, na yin jinyar ciwon baya da yake
fama da shi.
Wasu daga cikin jaridun Turai sun wallafa cewar
Pepe zai yi jinyar makonni hudu zuwa shida.
Madrid za ta kara da Atletico Madrid a gasar La
Liga a ranar 19 ga watan Nuwamba, sannan ta
fafata da Barcelona a farkon makon Disamba.

Schweinsteiger ya fara atisaye a Man United


Dan kwallon tawagar Jamus, Bastian
Schweinsteiger, ya fara yin atisaye da manyan
'yan wasan Manchester United.
Tun lokacin da Mourinho ya zama kociyan
United, Schweinsteiger ke yin atisaye shi kadai
ko kuma tare da matasan kungiyar 'yan kasa da
shekara 23.
Rabon da Schweinsteiger tsohon kyaftin din
tawagar kwallon kafa ta Jamus ya buga wa
United wasa tun a watan Maris karkashin Louis
van Gaal.
Schweinsteiger ya yi wa United wasanni 31, tun
lokacin da ya koma Old Trafford da murza-leda
daga Bayern Munich kan kudi sama da fam
miliyan 14 a Yulin 2015.

Manchester City za ta karbi bakuncin Barcelona

Manchester City za ta karbi bakuncin Barcelona
a gasar cin Kofin Zakarun Turai wasa na biyu da
za su fafata a Ettihad a ranar Talata.
A wasan farko da suka yi a Camp Nou,
Barcelona ce ta shararawa City kwallaye 4-0,
kuma Messi ne ya ci uku a karawar, Neymar ya
ci guda daya.
Barcelona ce ke mataki na daya a kan teburin
rukuni na uku da maki tara, sai Man City ta biyu
da maki hudu, sannan Borussia
Monchengladbach da maki uku, Celtic da maki
daya.
Haka kuma a ranar ta Talata Borussia
Monchengladbach za ta karbi bakuncin Celtic a
Jamus.

Kocin Jamus Low ya tsawaita yarjejeniyarsa

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Jamus,
Joachim Low, ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba
da jan ragamar kasar har zuwa karshen gasar
kofin nahiyar Turai ta 2020.
Kwantiragin Low, mai shekara 56, da Jamus za
ta kare ne, bayan kammala gasar cin kofin
duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Low ya dade yana jan ragamar tawagar Jamus,
wanda ya yi wa Jurgen Klismann mataimaki na
shekara biyu, kafin ya karbi aikin horar da kasar.
Kociyan ya lashe kofin duniya da aka yi a Brazil a
shekarar 2014, a kuma shekara biyar ya kai
kasar wasannin daf da karshe.
A gasar cin kofin ahiyar Turai da aka yi a
shekarar 2016, mai masaukin baki Faransa ce ta
fitar da Jamus a wasan kusa da na karshe a
gasar.

India: Bukukuwan Diwali sun bar baya da kura

Mazauna birnin Delhi na kasar India da suka
fusata, na ta musayar hotunan hazon da ya
turnuke birnin, kwana guda bayan bukukuwan
Diwali inda aka yi gagarumin wasan wuta.
Hazon wanda kurar launikan da aka rika watsawa
sama ta haifar, ya gurbata iskar da ke da
mummnar illa ga jama'a.
Mahukunta sun yi gargadin cewa birnin Delhi za
su fuskanci gurbatacciyar iska saboda yanayin
zafi da kuma iska mai sauri da ke kadawa.
Dawali wani muhimmin lokacin bukukuwa ne na
Hindu a arewacin India, inda ake murnar nasarar
da aka samu kan aikata laifuka.
Ana kuma wasan wuta ne a lokacin irin
wadannan bukukuwa, amma kuma hakan na
gurbata iska mai kyau.
A makon jiya ne hukumomi a birnin na Delhi
suka sanar da cewa za su kakkafa wasu
na'urorin tace gurbatacciyar iska a bakin hanyoyi
don rage gurbatarta.

Shugaban jam'iyyar Democrat ya ce 'FBI da karya doka'

Shugaban jam'iiyar Democrat a majalisar
dattawan Amurka ya ce hukumar bincike ta FBI
ta karya doka, kan binciken da take yi game da
sakonnin E-mail da ke da alaka da 'yar takarar
shugabancin kasar Hillary Clinton.
Harry Reid ya zargi daraktan hukumar ta FBI
James Comey da sabawa dokar da ta hana
jami'anta yin katsalandan a harkar zabe.
Rahotanni game da binciken hukumar ta FBI na
zuwa ne makonni biyu kafin zaben da za a
gudanar a Amurka.
Hukumar ta samu takardar izinin binciken tarin
sakonnin E-mail din mataimakiyar Mrs Clinton
Huma Abedin, da aka gano a cikin na'urar
komfiyutar maigidanta.
Sakonnin E-mail kimanin 650,000 ne za a
gudanar da bincike a kan su, da ake ganin zai yi
wuya masu binciken su fitar da sakamako a kan
su kafin ranar zabe.
Hukumar ta FBI ta ce tana da yakinin cewa
sakonnin E-mail din za su iya kasancewa suna
da alaka da binciken da gudanar a baya kan
Misis Clinton.
Ita dai Clinton ta yi amfani da yanar gizo ta
musamman a lokacin da take rike da mukamin
sakatariyar harkokin wajen Amurka a gwamnatin
Shugaba Barack Obama.

An hako manya-manyan tukwanen kasa a Kano

An hako wasu manyan tukwanen kasa a unguwar
Zangon Bare-bari a karamar hukumar Nassarawa
dake tsakiyar birnin Kano.
Masu hasashe dai na cewa tukwanen ka iya kai
wa shekaru 500 a duniya, ko da yake gwajin
kimiyya ne kadai zai iya tabbatar da haka.
Tun bayan gano tukwanen ne a wani gida da ake
sabunta ginawa, wasu da ba a san ko su wane
ne ba suka haura da tsakar dare suka fasa daya
daga cikin tukwanen da nufin kwashe abin da ke
ciki.
Mai unguwar Zangon Bare-bari Malam Auwalu
Rabi'u inda aka gano tukwanen, ya shaida wa
BBC cewa tukwanen guda uku da ke cikin wani
katon rami, manya-manya ne kamar girman
mutum.
Ya ce bayan da aka gano su ne a ranar Alhamis
aka shaida masa, inda shi kuma ya sanar da
hukuma.
A makonnin baya ma, an gano irin wadannan
tukwane a yankin Rangaza a karamar hukumar
Nassarawa a birnin na Kano.
A shekara biyar zuwa shida da suka gabata ma a
unguwar Agadasawa da ke birnin Kanon an taba
samun tukunya daya , amma ba ta kai girman
wadannan ba.

Nigeria: Za a yi bincike kan lalata da 'yan gudun hijira

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya umarci
a gudanar da binciki kan zargin yin lalata da
'yan gudun hijirar Boko Haram da kungiyar
Human Rights Watch (HRW) ta yi.
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce
shugaban ya kadu da jin wannan labari.
Sannan ya ce "kyautata jin dadin rayuwar
wadannan mutane da ke fuskantar barazana abu
ne mai muhimmanci ga gwamnatinsa".
Sanarwar wacce mai magana da yawun
shugaban, Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta
ce 'yan Najeriya dama kasashen duniya su san
cewa gwamnati ba za ta dau zargin na kungiyar
ta HRW da wasa ba.
Shugaba Buhari ya bai wa babban Sipeton 'yan
sandan kasar da gwannonin jihohin da lamarin ya
shafa umarnin su gaggauta gudanar da bincike
game da batun.
Binciken na su shi zai nuna mataki na gaba da
gwamnatin za ta dauka, a cewar sanarwar.
A ranar Litinin ne kungiyar HRW ta zargi wasu
jami'an gwamnatin Nigeria da yin lalata da 'yan
matan da rikicin Boko Haram ya raba da
muhallansu, ta hanyar yi musu fyade da
yaudararsu don yin lalata da su.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin da rashin yin
abin da ya kamata wajen kare irin wadannan
matan.
Ta kara da cewa ta samu bayanin yin lalata da
kuma fyade kan mata da 'yan mata 43 da ke
zaune a sansanonin gudun hijira bakwai da ke
Maiduguri, a jihar Borno.
Sama da mutane miliyan biyu ne suka bar
gidajensu sakamakon rikicin na kungiyar Boko
Haram.

Matar farko da aka yi wa dashen fuska a duniya ta rasu

Matar da aka fara yi wa dashen fuska a duniya,
Isabelle Dinoire ta rasu, kamar yadda likitoci a
kasar Faransa suka bayyana shekaranjiya Laraba.
Sanawar da asibitin Amiens Hospital, wurin da
aka yi mata aikin dashen fuskar a watan
Nuwamban shekarar 2005, ya fitar, ta ce Isabelle
ta rasu ne ranar 22 ga watan Afrilun da ya
gabata, bayan doguwar jinya. Ta rasu tana da
shekara 49 a duniya, kamar yadda kafar labarai
ta CNN ta bayyana. Asibitin ya ce dalilin bayyana
labarin rasuwarta a makare, ya samo asali ne
daga wasiyyar da marigayiyar ta bari, wadda ta
bukaci kada a bayyana labarin rasuwarta ga
manema labarai.
Sai dai asibitin bai bayyana ciwon da ya yi
ajalinta ba. Kodayake, kafafen labaran kasar
Faransa sun ruwaito cewa rashin lafiyar da ya yi
ajalinta yana da nasaba da aikin dashen fuskar
da aka yi mata a baya.
An yi wa marigayiyar aikin dashen fuskar ne
lokacin da take da shekara 38 da haihuwa, bayan
karyarta ta cije ta a fuska. An dasa wa
marigayiyar wani bangare na fuskar wata mace
da ta kashe kanta ne.
Kuma shekara guda bayan aikin ne, Dinoire ta
ce: “Fuskar nan ba tawa ba ce, amma duk
lokacin da na dubi madubi, kaina nake gani.”
Aikin da aka yi wa marigayiyar a kasar Faransa
ya bude hanyar fara yin dashen wasu sassan
fuskar dan Adam a wasu kasashe shida, ciki har
da kasar Amurka.

Karya ta jira uwardakinta tsawon kwana 6 a asibiti

A farkon makon nan ne aka sada wata karya da
uwardakinta bayan ta shafe tsawon kwana shida
tana zaune a kofar dakin da aka kwatar da ita a
wani asibiti da ke kasar Spain.
Karyar mai suna Maya, wadda take da shekara
biyu a duniya, ta zauna a kofar dakin da aka
kwantar da uwardakinta mai suna Sandra Iniesta,
’yar kimanin shekara 22 a duniya, har sai bayan
da aka sallame ta daga asibitin mai suna Elda.
Sandra ta yi fama ne da ciwon ciki yayin da suke
tafiya da mahaifinta da kuma karyar a kan
hanyarsu ta zuwa birnin Barcelona.
Daga nan ne suka garzaya asibitin Elda, aka
kwantar da Sandra na tsawon kwana shida, inda
aka yi mata aiki, kamar yadda jaridar The
Independent ta bayyana.
A wannan lokaci ne mahaifin Sandra ya yi
yunkurin komawa da karyar cikin mota don su
koma masaukinsu, amma sai ta yi kememe ta ki
barin kofar dakin da aka kwantar da Sandra.
Wadansu daga cikin ma’aikatan asibitin da suka
fahimci halin da ake ciki, sai suka fara yada
hotun Maya ta shafin sada zumunta na
Facebook. Bayan haka ne, sai jama’a suka fara
tururuwar ziyartar asibitin don yin ido hudu da
Maya, inda wadansu daga cikinsu har da ba ta
kyauta.
Yayin da aka sallami Sandra, manema labarai sun
ji ta bakinta kan al’amarin, inda ta ce hakan ba
wani bakon abu ba ne a gare ta. “Maya ta saba
jira na duk lokacin da na shiga daki, ko
makewayi. Ba ta barin wurin har sai bayan na
fito,”inji ta.

Ba’amurken kasar Sin ya kera jirgin da ke sauka a garejin gidansa

A Jihar Chicago ta kasar Amurka an samu
jama’a da injiniyoyi da suka mayar da bayan
gidansu filin jiragen sama, har ma suna ajiye
kananan jirage a garejinsu. Daga cikin wadannan
injiniyoyi akwai wani mutumin kasar Sin
zaunannen Amurka, mai suna Dabid Hu, wanda
injiniya ne da ke aiki a kamfanin kayan lantarki
na Nokia.
Wannan Ba’amurken dan kasar Sin ya fara kera
karamin jirgin sama ne tun a shekarar 2006.
Wato shekara 10 ke nan da ya fara wannan aiki
daga zane-zane a kwali, har ya fara sayen
sassan jirgin inda ya rika harhadawa. Dabid dai
ya hada jirginsa shi kadai, inda ya yi amfani da
lokutan da ba ya yin aikin komai.
Jirgin Dabid Hu yana da nauyin kilo 590, sannan
yana gudun kilomita 290 a kowace sa’a. Don
haka yana iya karade nisan kilomita 644 zuwa
724 a lokaci kankane.
Bayan da hukumar kula da jiragen sama ta
Amurka ta tantance ingancin jirgin, sai ya fara
tashi a cikin watan Yunin bana.
“Na sha tuka jiragen sama a tsawon rayuwata,
amma wannan shi ne karamin jirgi mafi inganci
da na taba tukawa. A tsarin sarrafa injinsa yana
da matukar nagarta ga dadin sauti,” a cewar
Musgrabe, wani jami’in bayar da horo a kamfanin
hada-hadar jiragen sama na Blue Sky Aero Inc.,
kamar yadda ya sanar da kamfanin Dillancin
Labarai na dinhua.
Ya ce karamin jirgin yana da “cikakkiyar kariya,”
inda ya kara da cewa, “komai a cikin jirgin yana
da cikakkiyar shaidar amincewata.”
Tun a watan Yunin bana aka fara hada-hadar
tashi da wannan jirgin saman, inda a halin yanzu
ya yi tafiye-tafiye na wata biyu, kuma ya shafe
sa’o’i 32, ta yadda aka kiyasta a kowane mako
yana cin dogon zango da yakan shafe akalla
sa’o’i biyu zuwa uku. Kuma babu wata matsala
da ta auku a gare shi.
“Wannan aiki ne da aka shafe shekara 10 ana
gudanar da shi. Iyalina sun fuskanci dimbin
kalubale wajen tallafa mini, inda suka fuskanci
damuwa da matsin rayuwa da rashin kudi.
Tamkar dai kowane gagarumin aiki, amma dai
farin cikina mun kai ga gaci,” a cewar Hu, bayan
da ya tashi da jirginsa a filin jirgin saman Morris
da ke bayan gidansa a ranar Lahadin da ta wuce.
“Na dai tashi sama a wannan jirgin. Don haka na
bude babin sabuwar rayuwa, inda kuma nake
hangen tunkarar wani al’amari nan gaba,” inji shi.

Manoma sun samu garabasar Naira miliyan 34 saboda dashen itatuwa a Sin

Manoman karkara a kasar Sin sun samu
garabasar Yuan miliyan biyar da dubu 600,
kimanin Dala dubu 850, wato daidai da Naira
miliyan 34, saboda kokarinsu wajen dashen
itatuwa a kauyen Lintao da ke Arewa maso
Yammacin kasar Sin a Lardin Ganasu, kamar
yadda kafar yada labarai ta Chinnanews.com ta
ruwaito.
Manoman karkarar da suka samu garabasar kudi,
yawansu ya kai magidanta 80 Zhang Zinhai, wani
da ya samu kaso mafi tsoka na Yuan dubu 100.
Ya ci burin dasa dimbin itatuwa a shirin dashen
badi.
Ya samu hanyar samun kudi mafi sauki fiye da
sauran al’umma, saboda a cewarsa: “Babu
bukatar kashe kudi a wannan aikin.”
A shekarar 2013, wani kamfani a kasar ya samar
da irin dashe na tsirran itatutuwa dubu 400 ga
daukacin magidantan da ke zaune a yankin.
Bayan shekara uku an yanke cewa manoman za
su mayar da yawan irin tsirran da aka ba su daga
kamfnain, inda aka tsara biyansu kudi. Shi kuma
kamfani zai sayar da wadannan bishiyoyi a
Artewacin kasar Sin, wato yankin Mongolia da
Shandi, ta yadda za su dasa korayen furanni a
yankunansu.

Tsohon duniya mai shekara 145 na neman mutuwa

Wani mutumin kasar Indonesiya da ya fi kowa
tsufa a duniya, bisa la’akari da yawan shekarunsa
da suka kai 145, ya bayyana cewa, a shirye yake
ya mutu.
A kundin bayanai da jami’an kasar Indonesiya
suka tattara, an yi nuni da cewa Mba Gotho yana
da shekara 145, kuma an haife shi a ranar 31 ga
Disambar 1870. Ya ce bai yi mamakin ganin
daukacin ’yan uwansa na haihuwa su 10 duk sun
mutu, har ma da matansa hudu, in data
karshensu ta mutu cikin shekarar 1988
daukacin ’ya’yansa duk sun mutu,. Kuma yana
zaune ne tare da jikokinsa da tattaba kunnensa
da ’ya’yan tattaba kunnen.
Matukar aka tantance hakikanin gaskiyar wannan
lamari, to tabbas ya fi kowa tsufa a duniya, tunda
yanzu kambin nisan shekaru da tsufa na hannun
wata ‘’yar kasar Faransa, mai Suna Jeanne
Calment mai shekara 122. Wannan tsoho tukuf-
tukuf ya fito daga ga Sragten da ke tsakiyar
yankin Jaba, kuma gidan talabijin na Lipitan 6 ya
tattauna das hi.
Ya ce ya dade yana raye a haka, shi yasa ba zai
damu ba, idan mutuwa ta riske shi. Bukatata
kawai in mutu, tunda daukacin jikokina suna iya
kula da kansu ne, kamar yadda ya bayyana wa
tashar talabijin ta Liputan 6 a Talatar makon jiya.
Suryanto, jikan Mbah Gotho ya ce kakansa ya
dade da shirya wa mutuwa, tun yana da shekara
122, amma har yanzu al’amarin bai auku ba.
Acewarsa: “an haka masa kabari tun a shekarar
1992, yau shekara 24 ke nan.” Baya ga haka,
Suryanto ya ce iyalan Mbah tuni suka ware masa
wurin da za a yi masa kabari kusa da kaburburan
’ya’yansa. Wani jami’in sashen tattara bayanai a
kasar Indonesiya ya tabbatar da ranar haihuwar
Mbah Gotho, kamar yadda take a rubuce jikin
katinsa, wato 31` ga Disambar 1870.
Ko an ki ko an so dole a sanya shi a jerin
mutanen da suka fi tsufa da nisan shekaru a
wannan duniyar, duk da cewa masu bincike na
daban ba su tantance hakikanin lamarin ba.
A cewar jikokinsa, ’yan kwanakin nan ya fi
sauraren rediyo, domin idanunsa ba su da kwarin
kallon talabijin. Kimanin shekaru uku ken an da
suka gabata aka fara dura masa abinci, tare da yi
masa wanka, saboda rashin kwarin jikinsa.
Da aka tuntubi Mbah Gotho kan ko mene ne
sirrin tsawon rayuwarsa, sai ya bayar da amsar
cewa: Sirrin dai hakuri ne kawai.’

Ta yi bikin bankwana kafin ta halaka kanta a Kalifoniya ta Amurka

Wata mai cutar ajali, mai suna Betsy Dabis ’yar
shekara 41 ta yi bikin bankwana da duniya kafin
ta halaka kanta. Wannan mata mai fama da
matsanaciyar cutar jijiyoyin da ke sakonni a
sassan jiki ta “ALS,” ta gayyato ’yan uwa da
abokan arziki don bikin bankwana sa duniya.
A labarin da jaridar Daily mail ta ruwaito, ta ce
wannan mata ita ce ta farko a cikin al’ummar
Jihar Kalifoniya da ta sha kwayoyin halaka kanta,
a karkashin kulawar likita.
A watan Yulin da ya wuce, ta aike da gayyata ga
abokai, inda ta ce: “Yanayin wanna biki ya saba
wa wanda kuka saba halarta a baya, don haka
akwai bukatar jimami da tunkarar al’amura tare
da bayyana al’amura karara.
A cewarta, ‘Doka daya ce tak: Kada a yi kuka a
gabana.’
daya daga cikin wadanda aka gayyata, mai suna
Niels Alpert, mai shirin sinima a birnin New York,
ya bayyana wa Dailymail cewa, “Ni da sauran
wadanda aka gayyata mun fuskanci kalubale,
amma babu wani abin tambaya kan cewa, mun
halarci taron ne don nuna kulak an halin da take
ciki.
Dabis ta bayyana yadda kakrshenta zai kasance
a cikin takardar gayyata, inda ta bayyana cewa,
za ta farad a suma ne. Mutanen da suka halarci
wannan biki dai sun haura 30, inda suka tattaru a
wani gari Ojai da ke Kudancin Jihar Kalifoniya.
Da karshen wannan mata ya karato, sai abokanta
suka suka rika yi mata sumbatar bankwana. Sai
aka dauke Dabis zuwa wata rumfa da aka
kwantar da ita a gado, inda ta sha sinadaran
magungunan Morphine da Pentobarbital da
chloral hydrate da likita ya ba ta.
Ita kuwa ’yar uwar Dabis Kelly ta bayyana wa
wata jaridar intanet ta muryar mutanen San
Diego (boice of San Diego) cewa:
“A gaskiya al’amarin yana da wuya a gareni.
Lamarin ya yi mini nauyi. Abu mafi tsanani shi ne
yadda mutum zai bar wannan dakin nan da nan,
saboda zan kasance cikin damuwa. Sai mutane
sun gano dalili. Sun fahimci irin tsananin wahalar
da ta yi fama da ita, shi yasa matakin da ta
dauka ya dacer. Sun amince da hakan. Sun san
cewa tana son kasancewa cikin jin dadi.”
Wannan al’amari dai ya auku ne bayan wata guda
da dokar Kalifoniya ta amince da bai wa mai
cutar ajali zabin daukar rayuwarsa/ta.

Kwararrun masana a Saudiyya sun kafa kungiyar auren zawarawa

Wasu kwararrun masana a kasar Saudiyya da
suka hada da likitoci da Injiniyoyi da malaman
addini da Farfesoshin jami’a, sun kafa kungiyar
auren zawarawa da matan da mazansu suka
mutu, ta hanyar bin ka’idar auren mace fiye da
daya a dokar shari’ar Musulunci da ta amince a
auri hudu.
Kafafen yada labaran Saudiya sun ruwaito cewa,
akwai matan da ba su da aure da suka kai
miliyan biyu, wadanda suka hada da matan da
mazajensu suka mutu da wadanda aka sake su
da ma wadandfa ba su taba yin aure ba. A
karkashin dokar Saudiyya irin wadannan matan
an yarda su sake yin aure, amma ba a cika
aiwatar da dokar ba.
“Za mu yada manufar auren mace fiye da guda,
kuma ya kamata mata su amince da ita, don
bayar da dama ga wadanda ba su da aure su
samu mazan aure,” a cewar jigon da ya kafa
kungiyar, Ataallah Al Abar.
Abar ya ce ya mika wa hukumomi takardun
bayanai da ke nuni da tsarin kafa kungiyar.
Sannan kungiyar za ta samar da shafin
sadarwarta, wanda za baje tsarin auratayya
tsakanin maza da mata.
Auren mace fiye da daya, al’amari ne da aka
saba da shi tunda addini ya amince a auri mata
hudu a lokaci guda.

Dan kasar Sin ya tuka keke zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya

Wani Musulmin kasar Sin ya tuko keke zuwa
kasar Saudiyya don yin aikin hajjin bana, inda ya
samu kyakkyawar tarba a birnin Taif da ke
Yammacin kasar. kungiyar ’yan tseren keke sun
yi marhabin da wannan bawan Allah.
Mahayin keken ya ce ya taso daga gidanshi da
ke birnin dianjiang da ke Arewa maso Yammacin
kasar Sin, inda ya shafe tafiyar kilomita dubu
takwas da 150 kagfin isowarsa Yammacin
Saudiyya a birnin Taif.
Bayan da ya huta a wannan birni, sai ’yan
kungiyar tseren kekuna suka yi wa bakonsu
Muhammad dan Sin rakiya zuwa birnin Makkah,
kamar yadda shafin sadarwa na Sabk.com ya
ruwaito.
“Mu ne kungiyar tseren kekenuna a Saudiyya da
muka fara tarbar mahayin keke dan kasar Sin,
muna kuma fatan ganin ya samu irin wannan
tarbar daga kungiyoyi irin namu, don haka muke
gabatar da shi a sauran birane,” a cewar Nayef
Al Rawas shugaban kungiyar tseren kekuna ta
Taif.
A ranar Asabart din makon jiya ne Hukumar Kula
da Harkokin Addini ta kasar Sin (SARA) ta ce,
kimanin mutum dubu 15 da 500 ne Musulmin Sin
da za su yi aikin hajjin bana. Kuma tuna Juma’ar
makon jiya aka tura jira 37 su dauki alhazan Sin
dubu 11, wadanda suka tuni suka isa birnin
Makka a kasar Saudiyya, kamar yadda Kamfanin
Dillancin Labarai na dinhua.
Wannan lamari na tukin keke zuwa birnin Makkah
mutanen nahiyar Asiya sun saba da shi, don yi
hajji ko umra.
A watan Mayun shekarar 2014 wani gungun
mutanen Malesiya sun taso daga birnin Kuala
Lumpur zuwa birnin Madina. Mutanen su 12, sun
hawo kekuna takwas da wata karamar mota biye
da su, inda suka keta birane 53.
Mutanen sun shafe kwana 60 suna tafiya, don yin
umrah a birnin Makkah, kamara yadda jagoransu
ya bayyana.

Likita ya tara haqoran da ya cire wa marasa lafiya dubu 10 a Abu Dhabi

Wani Likita a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar
Daular Larabawa, mai suna Dokta Nizar
AbdurRahman ya tara hakoran marasa lafiya
dubu 10.
“Wasu marasa lafiya na adana hakoran da aka
cire musu saboda dalilai na addini,” a cewar
likitan, wanda ya shafe shekara 15 yana aiki a
Abu Dhabi.
“Na shafe shekara 13 ina aiki a Cibiyal kula da
Lafiya ta Baniyas Ahalia, sannan na yi shekara
biyu a asibitin Al Ain,” inji shi.
“Ina burin samun lambar yabon kundin tattara
shahararrun al’amura na Limca da ke kasar Inda,
da kuma na duniya, wato Guiness world Record,
bisa la’akari da abin da na tara.”
Ya tara daukacin hakoran da aka cire a asibitin,
inda yake tsoma su a ruwan sinadarin Hydrogen
Perodide.
“Nakan wanke su da maganin kariya daga
kwayoyin cuta.Kuma akwai hakoran manyan
mutane a cikin tarina,” a cewarsa.
“Kodayaushe nikan bai wa majinyata shawar su
ci gaba da kula da hakoransu, har ta kai ga in
babu yadda za a yi sai a cire,” inji Likita.
Yana taimaka wa dalibai wajen aikin gwaji.
“dalibai kan untube ni in suna bukatar hakora.
Don su yi amfani da su a jarabawar gwaji, ko
cike gurbin hakorin da ya fadi,” inji shi.
dabi’un masu ciwon hakori da na gano Likita
Nizar a fahimci dabi’un masu fama da ciwo daga
sassan duniya daban-daban a tsawon shekara 15
da ya shafe yana aiki.
“Mutanen da suka fito daga Indiya, musamman
na birnin Kerala ba su cika zuwa asibiti ba, har
sai ciwo ya matsa musu. Sukan yi amfani da duk
maganingida da zai taimaka musu, sai lamarin ya
ci tura sannan su je asibiti. Mutane bas u fahimci
cewa zuwa asibiti da wuri zai ceci hakoransu.
Domin ba a zaune nike don cire musu hakori
kawai ba,” inji shi.
“su kuwa al’ummar Pakistan, musamman
wadanda ke makale da biro a aljihu, za su yi
kokarin bayyana maka yadda suke so a yi musu
aiki. Ba za ma su saurareka ba. Idan ka biye
musu, kana iya cire hakorin da ba shi ne mai
ciwon ba, inda a karshe sai an dawo an yi abin
da ya dace,” acewarsa.
Su kuwa mutane Bangladash, y ace, masu
tababa ne. “Kimanin kasha 90 cikin 100 na
wadannan mutanen suna tunanin idan an cire
musu hakori za su rasa ido. Don haka nike yi
musu alkawarin idona, ta haka nike jan ra’ayinsu
su amince a yi musu aiki.
Mutanen Afirka kuwa hakoransu na da kwari.
Nizar ya ce gogewarsa ta kai ga zai iya bayyana
maka sana’ar mutum idan ya dubi hakoran
marasa lafiya. “Zan iya tantance tela da mai
aikin lantarki. Suna da ramuka hadaddu a
hakoransu,”
“Na sha ganin marasa lafiyar da suka shafe
shekara 15 zuwa 20 ba su goge bakinsi ba,
amma suna son fara’arsu ta fito da hakora masu
haske kamar jaruman Hollywood. Irin wadannan
matsalolin suna da wuyar sha’ani.”
Abinci na da tasirin inganta kwarin hakori, don
haka sai a rika taunawa da kyau, kamara yadda
likitan hakori kan bayar da dabarun inganta
hakori. Ruiwan lemu mai dauke da iskar gas na
matukar cutar da hakora. Hatta shayi da gahawa
na cutar da su.
“Yawan tauna abinci na kara karfin hakori,” inji
shi.
A cewar Dokta Nizar samun managartan hakoran
ba abu ne mai wahala ba. Shawarar da ya fi bai
wa mutane wajen goge hakori, ita ce: “A goge
baki da buroshi mai laushi kuma a hankali. Domin
goge hakori ba kokowa ba ce.”
“akwai bukatar mutum ya goge hakorinsa sau
biyu a rana, kuma ya kuskure da sinadarin kariya
daga cuta. Sannan, mutum ya rika zuwa ana
duba hakoransa bayan wata shida. Kuma rika
zuwa gurje hakora a asibiti.
Matar wannan likita, mai suna Simi Nizara, ita
ma likitar hakora ce, ta kuma fara tara hakoran
da ta cire daga bakin marasa lafiya.
“Ba ni da tarin hakora masu yawa,” a cewar
wannan Ba’Indiya ’yar asalin Punalur da ta fito
daga gundumar Kollam, ta kuma shafe shekara
hudu tana aiki da asibitin Al Salama da ke
Baniyas, a birnin Abu Dhabi.
Wannan likita a kullum yana ganin marasa lafiya
10 zuwa 12, sannan yana cire hakora biyar zuwa
bakwai a kowace rana. “Na fara tara wadannan
hakora ne don bayar da tabbbaci, amma yanzu
abin ya zame mini sha’awa. Shekara biyu da
suka gabatar tarin hakoran da nike da shi ba su
wuce dubu takwas ba. Yanzu kuwa tabbbas sun
wuce dubu 10.
Mai rike da kambin tarin hakora a likitocin Indiya,
shi ne Dokta Jibreel Oysul, wanda ya fito daga
yankin Tamil Nadu a kasar Indiya, inda a Kundin
shahararrun abubuwa na Limca, aka tabbatar da
cewa ya tara hakoran majinyata dubu 10, tun a
shekarar 2011.

An dakatar da mata masu shirin talabijin a Masar saboda teva

Hukumomin talabijin a kasar Masar sun sallami
mata takwas masu gabatar da shirye-shirye
saboda teba, wai saboda manufar kafofin yada
labarai na kasar na kokarin kambama kimarta a
idon al’umma.
Wannan umarni dai an bayar da shi ne a makon
da ya gabata, inda aka bai wa matan wata guda
cur su yi kokarin rage teba kafin a kyale su su
dawo bakin aiki, kamara yadda kafofin yada
labaran kasar suka bayar da rahoto.
kungiyoyin fafutikar kare hakkin al’umma sun soki
lamirin korar mata takwas din, kuma mutane da
dama sun bijiro da tambaya kan cewa, ‘me ya sa
mata kawai aka kakaba wa dokar?’ Har yanzu dai
ba a tabbatar da cewa, ‘ko dokar za ta yi aiki a
kan mazan da ke gabatar da shirye-shirye a
gidajen talabijin ba, ko a’a.
Khadija Khatab, daya daga cikin mata masu
gabatar da shirye-shirye da aka sallama, ta yi tur
da wannan tsari. “Wannan kaskanci ne da abin
kunya,” kamara yadda ta bayyana wa jaridar Al
Watan.
“Wani yunkuri ne na korar masu gabatar da
shirye-shirye da suka goge da aiki, kuma a kyale
da za su ci gaba da aikin gabatarwar, alhalin ba
su da wasu managartan tsare-tsare,” a cewarta.
“kimanta nagartan aikin mutum bisa la’akari da
kiba ba ma’auni ne mai kyauta,” a cewar Eman
Beibers, shugabar kungiyar Bunkasa Harkokin
Mata ta birnin Alkahira. “Matsalarmu ita ce muna
auna kimar jiki a zahiri, maimakon aikin da
mutum ke yi. A gaskiya zan yi matukar
amincewa da dakatar da masu gabatarwar in da
a ce an yi la’akari ne da rashin ingancin aikinsu
ko suna caba kwalliya. Bai kamata a dubi kimar
mutum ko rashin kaurinsa, matukar ba ta/ya
furta munanan kalamai a lokacin da ya/take
bakin aiki, kuma ya/ta san yadda za a tarairayi
bakin da ake gudanar shirin da su,” kamar yadda
Beibers ta bayyana wa jaridar Gulf News.

An kashe dalibi yana kokarin sulhunta rikicin Naira 500

A ranar Litinin da misalin karfe 10 na dare ne
wani dalibi mai suna Aminu Badamasi da aka fi
sani da Justice mai kimanin shekara 28 da ke
sashin Ilimin Zamantakewa na Jami’ar Ahmadu
Bello da ke Zariya, ya rasa ransa a bayan da
wani matashi mai suna Yusuf Abdullahi da aka fi
sani da Mutuwa mai shekara 24 ya burma masa
wuka a ciki lokacin da yake kokarin sulhunta
wadansu kan bashin Naira 500.
Marigayin da wanda ake zargi da kashe shi suna
zaune ne a Layin Sule Ajasko da ke Jushi kusa
da Kwanar Maishanu a hanyar Jos a karamar
Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Yayan marigayin Balarabe Badamasi ya shaida
wa wakilinmu cewa, “Da misalin karfe 10 na dare
a ranar Litinin na fita domin in sa waya a caji sai
na ga marigayi kanena da abokansa su uku suna
hira sai muka gaisa na wuce. Na shiga shago ke
nan sai na ji hayaniya ina fita aka ce ai an kashe
Aminu kuma na hangi Yusuf Mutuwa rike da
wuka an rasa mai zuwa. A haka na yi kunar
bakin wake na fada masa na buge shi ya fadi
jama’a suka zo suka kama shi. Bayan tabbatar
da rasuwar kanina, sai matasa suka yi yunkurin
kashe Yusuf Mutuwa amma muka hana su har
’yan sanda su zo su kama shi, mu kuma muka
dauki gawar kanena muka kai gida shi ne aka yi
jana’izarsa.”
Mahaifiyar marigayin Malama Zainab Mohammed
cikin kuka ta ce danta ya samu kyakyawar
shaida domi a kan kokarin da yake yi wajen
sulhuntawa ne ake yi masa lakabi da Adalci
kuma a kan haka Allah Ya karbi rayuwarsa.
daya daga cikin abokan marigayin wanda abin ya
faru a idanunsa da ya nemi a sakaye sunansa, ya
ce, “Muna zaune sai muka ji ana jayayya
tsakanin Aminu Mai Indomi a kan raguwar bashin
kudin kwai Naira dari biyar da ya karba a hannun
Dini Abdullahi tun cikin azumi bai biya ba. Shi ne
shi marigayi Aminu ya taso domin ya sulhunta su
kuma ya cire Naira 500 ya biya Dini, sannan ya
yi musu nasiha. Shi Yusuf da ya yi kisa ba da shi
ake yi ba, kuma ba abin da ya shafe shi a
maganar. Kawai sai muka ga ya burma wa
marigayi Aminu wuka a ciki ya kuma yiwo kan
mutane.”
Wakilinmu ya ce bayan kammala jana’izar
marigayin matasa daga makabarta dauke da
makara sun wuce ofishin ’yan sanda suna cewa
sai ’yan sanda sun ba su Yusuf Mutuwa su
kashe shi tunda ya saba raunata mutane kuma
ya taba kashe wani a Abuja ya gudo ga shi
yanzu ya kara kisan kai, don haka a ba su shi su
kashe shi su huta. Sai da ’yan sanda suka yi
amfani da barkonon tsohuwa kafin su tarwatsa
matasan.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna,
ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar lamarin
inda ya yi kira ga jama’a su kwantar da
hankalinsu bayan sun kammala bincike za su
gabatar da wanda ake zargi a gaban shari’a
domin ya fuskanci hukunci.

An kaddamar da littafi kan rayuwar Shugaban kasa Buhari a Abuja

A ranar Litinin da ta gabata ce aka kaddamar da
littafi a kan rayuwar Shugaban kasar
Muhammadu Buhari mai taken ‘Muhammadu
Buhari: The Challenges of Leadership in Nageria’
a zauren taro na Cibiyar ’Yar’aduwa da ke Abuja.
Tsohon Shugaban kasa, Yakubu Gowon ne ya
jagoranci bikin kaddamarwar, kuma ya bayyana
cewa Shugaba Muhammadu Buhari mayaki ne,
wanda ke aiki tukuru domin ganin ya farfado da
tattalin arzikin Najeriya, duk kuwa da irin manyan
kalubalen da kasar ke fuskanta.
Littafin, wanda shahararren malamin jami’a,
Farfesa John N. Paden ya rubuta, ya kunshi
bayanai ne a kan rayuwar Shugaba Buhari da
kuma gwagwarmayarsa tun daga shigarsa siyasa
zuwa yau. Marubucin, wanda shi ne ya rubuta
littafin tarihin marigayi Sardauna Ahmadu Bello,
ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari da
cewa mutum ne jajirtacce, mai kishin kasa,
wanda ke kokarin yin duk wani abu da zai
taimaki kasarsa. Ya kara da cewa, ya rubuta
littafin ne domin ya bayyana wa duniya ko wane
ne Shugaba Muhammadu Buhari.
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya
yaba wa marubucin littafin, wanda ya ce ya
rubuta littafin da inganci. A cewarsa, duk wanda
ke son sanin Najeriya da shugabanninta, to ya
nemi littafin.
Shugabannin kasashen Chadi da Benin da Nijar
da ke makwabtaka da Najeriya sun halarci taron
kaddamar da littafin.
Sauran manyan mutanen da suka halarci
kaddamarwar sun hada da Mataimakin Shugaban
kasa, Yemi Osinbajo da Jagoran Jam’iyyar APC
na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da Shugaban
Jam’iyyar APC na kasa, Cif Odigie Oyegun da
Alhaji Isma’ila Isa Funtuwa da Farfesa Ibrahim
Gambari da tsohon Jakadan Amurka a Najeriya,
John Campbel

Sunday, 30 October 2016

Sojojin Najeriya sun harbe wani dan kunar bakin wake

Rahotanni daga garin Maiduguri sun nuna
cewa dakarun sojojin Nijeriya sun bindige
wani dan kunar bakin wake dake dauke da
bama-bamai har guda biyu a jikin sa,
 a
lokacin da ya yi yunkurin shiga sansanin
‘yan gudun hijira na Bakassi dake garin
Maiduguri a safiyar yau.
Idan ba a manta ba, a sanyin safiyar jiya
Asabar ma an samu tashin tagwayen bama-
bamai a wannan yankin, inda kimanin
mutane tara suka rasa ransu yayin da
mutane da dama suka ji rauni.
A wani labarin mai kama da wannan kuma a
jiya ne dai A Najeriya, mutane tara ne aka
tabbatar da sun mutu lokacin da wasu da
ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka
kaddamar da harin bama-bamai a Maiduguri,
babban birnin jihar Borno.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan kunar bakin
wake ne suka tayar da bama bamai guda
biyu, daya a kusa da kofar shiga sansanin
‘yan gudun hijira na Bakassi, sannan dayan a
wani gidan man NNPC.
Hukumar bayar da agajin gaggawa a kasar,
NEMA, ta ce wasu mutane 24 sun samu
raunuka.
Birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-
haren ‘yan kungiyar ta Boko Haram,
kodayake yanzu ba safai ake kai masa hare-
hare ba.
Dakarun sojin Najeriya na cewa suna bakin
kokarinsu na kawar da kungiyar ta Boko
Haram, suna masu kira ga mutane cewa su
rika kai rahoton duk wani motsi da ba su
amince da shi ba.

Abba Kyari yana nan, ba a dakatar da shi ba

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin
tarayyar Najeriya, Abba Kyari ya dawo aiki a
karshen makon nan
– A da ana ta rade-radin cewa Shugaba
Buhari ya dakatar da shi daga aiki
– Sai dai Abba Kyari yace yana nan,
shugaban kasa bai dakatar da shi

Malam Abba Kyari
Shugaban ma’aikatar fadan gwamnatin
tarayya watau Abba Kyari ya dawo Ofis a
ranar Juma’ar nan. Wannan dai ya biyo
bayan rade-radin da aka yi ta yadawa na
cewa shugaban kasa ya dakatar da shi Abba
Kyari daga aiki.
Abba Kyari wanda shine shugaban
ma’aikatan gidan gwamnatin yace karya ce
kurum ake yi, yana nan babu wanda ya kore
sa, ko ya dakatar shi. Abba Kyari yace ya
dai je hutu ne na kwana biyu, kuma har ya
kamala, ya dawo bakin aiki.
A wancan makon ne dai ‘yan jarida suka rika
yada labarin cewa Shugaban Kasa ya
dakatar da Abba Kyari daga aiki, da ya dawo
wannan karo sai yake tambayar ‘Yan jaridun
ko za su fadawa duniya cewa Abba Kyari ya
dawo, ta shafin Twitter? Abba Kyari dai bai
ce da ‘yan jarida uffan ba, yace aikin sa ba
ya barin yayi magana da ‘yan jaridu.
Ana dai zargin cewa Abba Kyari yana cikin
wadanda suke rike madafan iko a cikin
wannan gwamnati. Ana zargin sa da cewa ya
karbi cin hanci na miliyan N500 daga
kamfanin MTN. Sai dai shugaban kasa
Buhari yace duk rade-radin banza ne, shine
kadai ke rike da madafan iko a gwamnatin
na sa.

Abin da ya sa ba zan taba Kwankwaso ba-Gwamna Ganduje

Gwamna Gaduje yace ba zai tsaya
binciken Gwamnatin Kwankwaso ba
– Gwamna Ganduje yace zai maida hankali
ne wajen yin ayyuka a jihar Kano
– Ganduje ne mataimakin Rabi’u
Kwankwaso lokacin yana gwamna
Gwamna Ganduje na jihar Kano yace ba zai
tsaya bata lokacin sa ba wajen binciken
gwamnatin Injiniya Rabi’u Kwankwaso.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a
Ranar Asabar dinnan, bayan taron Jam’iyyar
APC na bangaren Kano da aka yi a Garin
Sokoto.
Gwamna Ganduje yace duk da cewa mafi
yawan Jihohi suna ta binciken abin da ya
faru a Gwamnatocin baya, shi ba zai tsaya
yin wannan ba. Gwamna Ganduje ne dai
mataimakin Kwankwaso a lokacin yana
Gwamnan Jihar Kano har sau biyu; a
shekarar 1999-2003 da kuma 2011-2015.
Gwamna Ganduje yace abin da zai karkata
gare shi, shine ayyuka da tsare-tsaren da duk
za su kawo cigaba a Jihar Kano. Gwamna
Ganduje yace gwamnatin sa za tayi kokari
karasa duk ayyukan kwarai da ta gada daga
duk gwamnatocin baya wadanda za su kawo
cigaba ga Jihar Kano.
Ana ta rikici tsakanin magoya Kwankwaso da
shi Gwamna Ganduje, Gwamna Ganduje yayi
tir da abin da ke faruwa, yace wasu ne kawai
ke yada karya domin su ga bayan sa da
gwamnatin sa. Gwamna Ganduje yace
wannan abin Allah-wadai ne daga manyan
‘yan Kwankwasiyyan.

Chelsea ta doke Southampton da ci 2-0

Southampton ta yi rashin nasara a gida a hannun
Chelsea da ci 2-0 a gasar Premier da suka fafata
a ranar Lahadi a filin wasa na St Mary.
Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Eden
Hazard a minti na shida da fara wasan, sannan
ta ci ta biyu minti 10 da dawowa daga hutu ta
hannun Diego Costa.
Da wannan sakamakon Chelsea ta koma mataki
na hudu a kan teburin Premier da maki 22, yayin
da Southampton tana matsayi na 10 da maki 12.
Chelsea za ta karbi bakuncin Everton a wasannin
mako na 11 a gasar ta Premier a ranar Asabar,
inda Southampton za ta ziyarci Hull City a ranar
Lahadi.

Bale ya tsawaita zamansa a Real Madrid

Gareth Bale ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da
murza-leda a Real Madrid har zuwa shekarar
2022.
Bale mai shekara 27, ya koma Madrid da taka
leda daga Tottenham kan kwantiragin shekara
shida a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 85, a
matsayin wanda aka saya mafi tsada a tarihin
tamaula.
A cikin watan Oktoba su ma abokan taka-ledar
Bale a Real Madrid Luka Modric da Toni Kross
suka tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a
kungiyar.
Real Madrid ta sanar da cewar a ranar Litinin,
Bale, zai tattauna da 'yan jarida kan batun
yarjejeniyar da suka sake kullawa.

Baba Ganaru ya zama kociyan Wikki Tourists

Wikki Tourists ta garin Bauchin Nigeria ta nada
Baba Ganaru a matsayin sabon kociyanta.
Kungiyar wadda ta kare a mataki na uku a gasar
Firimiyar Nigeria da aka kammala, ta saka hannu
a kan yarjejeniya aiki da kociyan na tsawon
shekara daya.
Wikki wadda za ta wakilci Nigeria a gasar
Zakarun Afirka ta Confederation ta rasa mai
horar da 'yan wasanta Abdu Mai Kaba wanda ya
koma Akwa United.
Baba Ganaru tsohon kociyan Nasarawa United
ya bar aikin jan ragamar Kano Pillars a karshen
gasar Firimiyar Nigeria da aka yi, bayan da
kungiyar ta kare a mataki na bakwai a gasar.

Super Eagles ta gayyaci 'yan wasa 24

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Gernot
Rohr, ya gayyaci 'yan wasa 24 da za su kara da
Algeria a wasan nema shiga gasar kofin duniya
a Uyo.
Cikin 'yan wasan da ya bai wa goron gayyata,
uku daga cikinsu masu tsaron raga ne, sai masu
tsaran baya tara da 'yan wasan tsakiya biyar da
kuma masu cin kwallaye su bakwai.
Mai tsaron raga Ikechukwu Ezenwa na
IfeanyiUbah, shi ne dan kwallon da yake taka-
leda a gasar Firimiyar Nigeria wadda aka
kammala.
Nigeria wadda ta lashe kofin Afirka sau uku tana
mataki na daya a kan teburin rukuni na biyu,
bayan da ta ci Zambia 2-1 a wasan farko da suka
yi.
Ga jerin 'yan wasan da aka gayyata Super
Eagles:
Masu tsaron raga: Carl Ikeme (Wolverhampton
Wanderers, England); Ikechukwu Ezenwa (FC
IfeanyiUbah); Dele Alampasu (FC Cesarense,
Portugal)
Masu tsaron baya: Leon Balogun (FSV Mainz 05,
Germany); William Troost-Ekong (Haugesund FC,
Norway); Kenneth Omeruo (Alanyaspor FC,
Turkey); Uche Henry Agbo (Granada FC, Spain);
Tyronne Ebuehi (ADO Den Haag, The
Netherlands); Abdullahi Shehu (Anorthosis
Famagusta, Cyprus); Musa Muhammed (Istanbul
Basaksehir, Turkey); Elderson Echiejile (Standard
Liege, Belgium), Kingsley Madu (SV Zulte
Waregem, Belgium)
Masu wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea
FC, England); Ogenyi Onazi (Trabzonspor FC,
Turkey); Wilfred Ndidi (KRC Genk, Belgium);
Oghenekaro Etebo (CD Feirense, Portugal); John
Ogu (Hapoel Be'er Sheva, Israel)
Masu cin kwallaye: Ahmed Musa (Leicester City,
England); Kelechi Iheanacho (Manchester City,
England); Moses Simon (KAA Gent, Belgium);
Victor Moses (Chelsea FC, England); Odion
Ighalo (Watford FC, England); Brown Ideye
(Olympiacos FC, Greece); Alex Iwobi (Arsenal
FC, England)

An hana Mourinho zuwa filin wasa

An kori kocin Manchester United Jose Mourinho
zuwa wurin da 'yan kwallo ke zama a wasan da
suka tashi 0-0 da Burnley na gasar Premier
ranar Asabar.
Mourinho ya fito bayan an dawo daga hutun
rabin lokaci sannan aka raka shi wajen tsayawar
'yan kwallo a Old Trafford a wasan da ya sa
United koma ta takwas a tebirin gasar Premier.
Daga nan ne kuma dan kasar ta Portugal mai
shekara 53 ya tafi wurin da shugabanni ke zama.
Alkalin wasa Mark Clattenburg ya yi watsi da
kiran da United ta yi a ba su bugun fenareti.
Wani mai sharhi kan wasanni Danny Murphy ya
bayyana cewa kashin da aka rika bai wa United a
'yan kwanakin nan ne ya gigita Mourinho.
Mourinho bai yi magana da 'yan jarida ba bayan
wasan, wanda United ta mamaye,inda ta yi
yunkurin cin kwallo sau 37.

Na yi shakku kan 'yan wasana - Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya amince
cewa ya nuna shakku kan 'yan wasansa ba wai
kan tsarinsa na buga wasa ba bayan sun doke
West Brom, lamarin da ya sa suka zo karshen
wasanni shida basu ci kwallo ba.
City ba ta yi nasara a wasa ba tun ranar 24 ga
watan Satumba, sai dai ta doke West Brom da ci
4-0 inda ta hau kan tebirin gasar Premier.
Guardiola ya shaida wa BBC Sport cewa "Sau
shida muka yi wasa ba mu ci ba, kuma hakan
lokaci ne mai tsawon gaske. Duk lokacin da
muka sha kashi sai na yi shakkar 'yan wasana.
Haka kuma idan muka dawo daga hutun rabin
lokaci bamu ci wasa ba sai na yi shakku kan su."
Guardiola ya kara da cewa bai taba yin shakka
kan tsarin wasansa ba, yana mai cewa "sake yin
nasara yana da matukar muhimmanci a gare
mu."
Sergio Aguero ya zura kwallaye biyu a wasan,
yayin da Ilkay Gundogan ya kara kwallaye biyu.

An yi kunnen doki tsakanin Kudu da Arewa a dambe

Kimanin wasannin takwas aka dambata da
safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke
Dei-Dei a Abuja, Nigeria, sai dai karawa biyu ce
aka yi kisa.
Bangaren Kudawa ne suka fara yin nasara, inda
a turmin farko Autan Faya daga Kudu ya buge
Shagon Dogon Dan Jamilu daga Arewa.
Ana gama zagayawa da Autan Faya ne sai
Arewa suka dauki fansa, inda Shagon Buzu daga
Arewa ya buge Shagon Shagon Babangida daga
Kudu a turmin farko.
Ga jerin wasannin da aka yi babu kisa:
Shagon Shagon Dan Kanawa daga Kudu da
Lawwalin Gusau daga Arewa
Shagon Bahagon 'Yan Sanda daga Arewa da
Ali Shagon Bata isarka daga Kudu
Shagon Mahaukaci Teacher daga Arewa da
Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu
Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Nuran
Dogon Sani daga Arewa
Autan Fafa daga Arewa da Bahagon Sisko
daga Kudu
Dogon Na Gobira daga Arewa da Bahagon
Dan Kanawa daga Kudu.

Cibulkova ta lashe gasar tennis ta Singapore

Dominika Cibulkova ce ta lashe gasar kwallon
tennis ta kwararru ta mata da aka kammala a
Singapoe a ranar Lahadi.
Cibulkova 'yar kasar Slovakia, ta lashe kofin ne,
bayan da ta doke wadda take a matsayi na daya
a jerin iya wasan a duniya Angelique Kerber da ci
6-3 da 6-4.
'Yar wasan mai shekara 27, ta ce rana irin ta
Lahadi ba za ta taba mancewa da nasarar da ta
yi ba.
Cibulkova ta kai wasan karshe ne a ranar
Asabar, bayan da ta ci Svetlana Kuznetsova a
dukkan fafatawa ukun da suka yi.

Yanda Zaka Mayar Da Wayarka Kamar Android 7 Ba Tare Da Upgrade Ba

Barkanku da warhaka maziyarta shafinmu mai albarka, shafin da a koda yaushe yake kokarin kawo muku bayanai kan abubuwa da suka shafi wayoyin hannu inda a wasu lokutan mukan dan taba fannin na'urar kwamfuta da sauran ababe da suka shafi fasahohin zamani.
A yau cikin ikon Allah zamu kawo muku bayanai akan matakan da zaku bi don ku mayar da wayoyinku na android zuwa tsarin android 7 ko wanda aka fi sani da Nougat wacce take a mazaunin manhaja mafi girma a kira android.
Android Nougat (Android 7) itace sabuwar manhaja kuma babba a tsarin zubi(version) na wayoyin android. Akwai wasu zube-zube na wayar da dama; kama daga kitkat 4.2.2 , lollipop 5.0.1 , marsmallow 6. , ya zuwa kan android 7 (Nougat).
Ba dole bane sai mutum ya kasance yana siyan duk irin wayoyin dake dauke da wadannan zube-zuben bane zai iya samun damar more su ba. Mutum zai iya more su ta hanyar bunkasa (update) wayar tashi zuwa duk irin sabuwar manhaja wacce ke dauke da zubin da yake so muddun kamfanin wayar tashi ya bashi damar yin hakan ko kuma ta hanyar yin amfani da kwanfuta. Sai dai ba kowacce waya bace ke samun wannan dama inda a dalilin hakane na yanke shawarar yin rubutu kan yadda zaka mayar da wayarka zuwa kamannin android Nougat din.
Matakan Da Za a bi
Ba tare da wani dogon surutu ba, wasu apps ne kawai zaka dauko sannan kayi install dinsu akan wayarka. Ga applications/softwares da ake bukata:
- Nougat Launcher :- Launcher ce da zata mayar da hotuna da kuma icons na apps din wayarka su koma kamar na android.
- N Dialer+Calci :- Application ne da zai mayar da dialpad din kira da na calculator din wayarka zuwa irin na Nougat.
Ragowar apps din ake bukata sune: Android N-ify the status bar , Twilight , Xposed Installer da sauransu..
Ina fata da wannan dan rubutu nawa wasu zasu amfana wajen kawata wayoyinsu don jin dadin amfani dasu. Ba daidai bane ka yiwa wani ko wata karyar cewa wayarka version 7 ce, alhalin kana rike da kitkat ne.....
Tura wa abokai...

Sojoji sun dakile yunkurin sabon hari a Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun
dakile wani yunkuri na kai harin kunar bakin
wake a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi
dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An yi yunkurin kai harin ne kwana daya, bayan
wasu 'yan kunar bakin wake da ake zargi 'yan
kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare a
birnin, ciki har da kofar shiga sansanin na
Bakassi.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa
ta Najeriyar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce
dakarun rundunar Operation Lafiya Dole dake
Maiduguri sun harbe wani dan kunar bakin wake
da safiyar Lahadi, yayin da yake kokarin kutsawa
cikin sansanin 'yan gudun hijiran na Bakassi.
Kanar Kukasheka ya ce bayan an harbe dan
kunar bakin waken, jami'ai tsaro masu kwance
bom sun lalata bom din dake jikinsa kafin ya kai
ga tashi.
Hare-haren kunar bakin wake na neman dawowa
a birnin na Maiduguri, bayan an samu saukin
hare-haren na lokaci mai tsawo.

Nigeria: An maido da abincin 'yan gudun hijira da aka sace

Jami'ai a jihar Borno ta Nigeria sun ce an
hannunta musu abincin da gwamnatin tarayyar
kasar ta aike wa 'yan gudun hijirar rikicin Boko
Haram da shi amma sai aka karkata akalar wasu
daga cikin motocin da ke dauke da kayan
abincin.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta
jihar Alhaji Ahmed Satomi ya tabbatar wa BBC
da cewa sun karbi motoci 79 na kayan abinci
daga cikin 113 da gwamnatin tarayyar ta turo;
kuma nan ba da dadewa ba za su karbi sauran.
'' Ministan da aka wakilta ya kawo kayan abincin
ne ya zo ya kawo wannan abincin da ake tunanin
an so a bi wata hanya da shi, amma
alhamdulillahi yanzu an gano shi har an
hannunta shi ga gwamnatin jihar Borno.'' In ji
Alhaji Satomi.
Zargin karkata akalar kayan abincin na 'yan
gudun hijra dai ya fusata mutane da dama a
kasar tun ma ba 'yan gudun hijiran ba wadanda
suka yi zanga-zanga a sansanoni daban-daban

Ivory Coast: Za a gudanar da kuri'ar raba gardama kan kundun tsarin mulki

Ivory Coast zata gudanar da kuri'ar raba
gardama a yau akan sabon kundun tsarin mulkin
kasar wanda shugaba Alassane Ouattara ya ce
zai taimakawa kasar wajen samun cigaba bayan
shekarun da aka shafe ana fama da rikici.
Tuni dai jam'iyyun adawar kasar suka yi kiran da
a kauracewa wannan yunkuri, suna masu cewa
anyi saurin yiwa kundun tsarin mulkin gyare-
gyare kuma zai bawa shugaban kasar karfin ikon
da ya wuce kima.
Wani babban abu a cikin gyare-gyaren da ake
son yi a cikin kundun tsarin mulkin shi ne
saukaka ka'idojin zama dan kasa ga 'yan takarar
shugaban kasa, wani batu da ya rura wutar yakin
basasa har sau biyu a kasar tun shekarar 2002.
Sannnan kuma zai samar da majalisar dattawa a
kasar wadda kaso uku na adadinsu shugaban
kasa ne zai nada su.

Saturday, 29 October 2016

Tsagerun Neja-Delta: Najeriya tayi asarar fiye da Tiriliyan 2

Kamfanin man Najeriya na NNPC tace
Najeriya ta tafka makudan asara daga
farkon shekarar nan zuwa yanzu
– NNPC tace Najeriya ta rasa akalla Biliyan
$7 watau fiye da Naira Tiriliyan 2 saboda
Tsagerun Neja-Delta
– Tsagerun Neja-Delta suna ta fasa butatan
man Kasar da yankin

NNPC GMD Baru
Kamfanin man Najeriya watau NNPC ta
bayyana cewa Kasar Najeriya tayi uban
asarar fiye da Naira Tiriliyan biyu daga
farkon shekarar nan zuwa yanzu. NNPC tace
daga Junairun shekarar nan, kawo yanzu
Kasar Najeriya ta rasa N2. NNPC tace daga
Junairun shekarar nan, kawo yanzu Kasar
Najeriya ta rasa Tiriliyan N2.1
Shugaban Kamfanin na NNPC, Maikanti Baru
yayi wannan bayani a Garin Abuja, wajen
gabatar da wata takarda game da farashin
man fetur da kuma tsageranci ‘yan yankin
Neja-Delta. Baru ya gabatar da wannan
takarda ne domin nuna alakar tsagerancin da
ake yi a Yankin da kuma abin da ake samu
daga man fetur din.
Najeriya ta rasa ganguna fiye da 7000
wannan shekarar, idan kowane ganga na kan
$45, Najeriya ta tafka asarar kusan Biliyan
$7 kenan watau fiye da Naira Tiriliyan biyu.
Kuma dai mafi yawan man da aka rasa na
gangar Gwamnatin Tarayya ne.
Shugaban APC Cif Oyegun yace an kauda
Boko Haram, kuma Gwamnatin Shugaba
Buhari na kokarin kawo karshen rikicin Neja-
Delta. John Oyegun yace Shugaba Buhari na
kokarin gyara, musamman ga abubuwa uku
kamar yadda ya dauki alkawari; tsaro, cin
hanci da kuma tattalin arziki.

Man City ta dare kan teburin Premier

Manchester City ta hau kan teburin Premier,
bayan da ta ci West Brom 4-0 a wasan mako na
10 da suka fafata a ranar Asabar.
Sergio Aguero ne ya ci wa City kwallaye biyu
kafin a je hutun rabin lokaci a karawar da suka yi
a filin wasan West Brom.
Bayan da aka dawo ne daga hutu shi ma Ilkay
Gundogan ya zura guda biyu a raga.
Da wannan sakamakon City ta koma ta daya a
kan teburin Premier da maki 23 a wasanni 10 da
ta yi a gasar.

Liverpool ta samu maki uku a kan Crystal Palace

Crystal Palace ta yi rashin nasara a gida a
hannun Liverpool da ci 4-2 a gasar Premier
wasan mako na 10 da suka kara a ranar Asabar.
Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Emre
Can minti 16 da fara wasa, minti biyu tsakani
Crystal Palace ta farke ta hannun James
McArthur.
Kafin a je hutu Liverpool ta kara ta biyu ta
hannun Dejan Lovren, Crystal Palace ta sake
farkewa ta hannun James McArthur.
Liverpool ta ci kwallo na uku daf da za a tafi
hutun rabin lokaci ta hannun Joel Matip, kuma
saura minti 18 a tashi daga wasan Roberto
Firmino ya ci na hudu.
Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 23
a wasanni 10 da ta buga a gasar ta Premier.

Arsenal ta doke Sunderland 4-1

Sunderland ta yi rashin nasara a gida a hannun
Arsenal da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako
na 10 da suka fafata a ranar Asabar.
Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Alexis
Sanchez a minti na 19 da fara tamaula, bayan da
aka dawo ne daga hutu Sunderland ta farke ta
hannun Jermain Defoe.
Arsenal ta kara cin kwallaye ta hannun Olivier
Giroud a minti na 71 da kuma 76, sannan Alexis
Sanchez ya ci ta hudu kuma ta biyu da ya ci a
wasan.
Arsenal ta hada maki 23 a wasanni 10 da ta yi a
gasar Premier ta bana.

Mutane 9 ne suka mutu a harin Maiduguri

A Najeriya, mutane tara ne aka tabbatar da sun
mutu lokacin da wasu da ake zargi 'yan kungiyar
Boko Haram ne suka kaddamar da harin bama-
bamai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Rahotanni sun ce wasu 'yan kunar bakin wake ne
suka tayar da bama bamai guda biyu, daya a
kusa da kofar shiga sansanin 'yan gudun hijira na
Bakassi, sannan dayan a wani gidan man NNPC.
Hukumar bayar da agajin gaggawa a kasar,
NEMA, ta ce wasu mutane 24 sun samu raunuka.
Birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-
haren 'yan kungiyar ta Boko Haram, kodayake
yanzu ba safai ake kai masa hare-hare ba.
Dakarun sojin Najeriya na cewa suna bakin
kokarinsu na kawar da kungiyar ta Boko Haram,
suna masu kira ga mutane cewa su rika kai
rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi
ba.
A ranar Asabar za a ci gaba da buga gasar La
Liga wasannin mako na 10. Sai dai Cristiano
Ronaldo na fama da rashin cin kwallaye a gasar
bana.
Dan wasan ya gamu da koma-baya ta fuskar cin
kwallaye tun lokacin da ya koma Madrid a
shekarar 2009, wanda ya ci guda hudu a bana
biyu a gasar La Liga
A tawagar kwallon kafa ta Portugal kuwa,
kwallaye biyar Ronaldo ya ci, hudu a karawa da
Andorra da daya a fafatawar da suka yi da
tsibirin Faroe a wasan neman shiga gasar cin
kofin duniya.
A kakar wasannin bara da aka kammala Luis
Suarez ne ya lashe kyautar wanda ya fi yawan
cin kwallye a gasar La Liga, inda ya ci 40; guda
30 Ronaldo ya ci a matsayi na biyu.
A kakar wasannin kwallon kafa ta bana Messi na
Barcelona ya zura kwallaye 14 a raga a wasanni
11 da ya yi.

Kyawawan halayen Hadiza Gabon

Hadiza ko kuma Dijatou Aliyu wadda aka fi
sani da Hadiza Gabon, tana daya daga cikin
jarumai mata da suka shahara a farfajiyar
finafinan Hausa. Hadiza ta yi matukar
kwarewa a duk wani matsayin da za a ba ta
a fim, wanda hakan ya sa har yau ake
damawa da ita a masana’antar, domin ba
kowace jaruma ba ce za ta iya hawa irin
matsayin da jarumar ke hawa a finafinai.
Fitacciyyar Jarumar Kannyywood, Hadiza
Gabon
Kyakkyawar jarumar ta kuma kasance mai
yawan masoya daga cikin jaruman fim, har
ta kai ga ta samu daukakar da ita kanta ba
ta taba zaton samu ba.
Allah ya azurta jarumar da kyawawan dabi’u
na taimako, tausayi da jin kan mutane,
musamman gajiyayyu, marasa karfi da kuma
marayu.
Akwai lokacin da labarin wata nakasashiyar
yarinya mai suna Rahama Karuna wacce ake
dauka a cikin roba ana bara da ita a jihar
Kano, lokacin da Hadiza ta ji labarin wannan
yarinya sai ta tausaya sosai harma ta ziyarci
yarinyar inda ta tallafa mata da kudade da
kayayyakin abinci.
Sannan kwanakin baya Hadiza ta ziyarci
sansanin yan gudun hijira inda su ma tayi
masu alkhairi mara misali, domin ta tallafa
masu da kayan abinci, kamar yadda muka
sani cewa yan gudun hijira sunyi fama da
lalurar yunwa.
Hadiza Gabon a lokacin da ta kai ziyara
sansanin yan gudun hijira
Bayan nan kuma a lokacin da jaruma Hadiza
za ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta,
maimakon ta tara jama’ar da ba su dace ba
a yi ta sharholiya, sai ta tattara kayayyakin
bikin nata ta je gidan marayu, inda ta dauke
su a matsayin wadanda za su taya ta bikin.
Hadiza ta yanka kek din bikin ranar
haihuwarta ta tare da marayun kuma ta ci ta
sha tare da marayun, domin a cewarta yin
hakan wata hanya ce ta farantawa marayun
rai, tare kuma da debe musu kewa, wanda
bai kamata a ce ana mayar da su saniyar
ware ba a al’amuran farin ciki dake gudana a
kasar nan.

Hadiza Gabon tare da wasu yara
Wannan ba shi ne karo na farko da Hadiza ta
kai ziyara gidan marayu ba, domin aikinta ne
ziyara gidan marayun inda take raba musu
kayan abinci da kayan sawa.
Munayi wa wannan jaruma fatan alkhairi da
kuma ci gaba a rayuwarta ta duniya da
lahira.

Darajar farashin Naira ta tashi

Darajar farashin Naira ta daga a
Bankunan Najeriya
– Naira ta daga da kusan Kobo 50 a Bankin
canji na Kasar
– A yanzu haka, Dalar Amurka tana kan
N305
Darajar farashin Naira ta samu yunkurawa
sama a Bankin canjin kudi na Najeriya. Kudin
Naira na Najeriya ya samu dagawa da abin
da ya kusa kai N1 a banki, sai dai kuma
Naira ya sauka a kasuwar canji, Inji Hukumar
Dillacin labarai na Kasa watau NAN
Darajar farashin Naira ta samu dagawa daga
N304.5 zuwa N305 a kan kowace Dalar
Amurka guda, ma’ana dai Naira ta kara
daraja da Kobo 50 watau Rabin kwandala.
A kasuwar canji kuma, watau Bureau De
Change, ana canjin dalar Amurka ne da Naira
N385, yayin da kuma ake sayar da kudin
Pound Sterling na Ingila a kan N560, ana
kuma canjin Kudin EURO na Turai a kan
N503 kan kowane guda.
Ma’ana dai Naira ta kuma fadi a kasuwar
‘Yan canji da ake kira Bureau De Change da
har kusan N5 duk da cewa farashin Naira ya
daga a Bankunan Kasar. Shugaban ’Yan
Canjin na Kasa, Malam Aminu Gwadabe yace
kwanan nan Darajar farashin Naira zai daga
sama, domin kuwa Bankin Kasar na shirin
yin wani abu a kan matsalar da ake
fuskanta.

Hotunan Rahama Sadau Tare Da Akon A Los Angeles


Rahama sadau ta amsa gayyatar da wasu jaruman Hollywood; akon da Jeta amata sukayi mata don su yi wani wasan kwaikwayo mai taken "The American King" wanda zasu shirya shi a wasu birane na kasar Amurka , Senegal South Africa da Nigeria.
Idan baku mance ba a kwanakin baya ne kungiyar masu tace fina-finai MOPPAN ta kori Rahama sadau daga kannywood bayan wani hoton video na waka tare da classiq inda ta nuna wasu dabi'u da basu dace da kundin tsarin kannywood ba.
A yanzu haka dai rahama sadau din tana birnin Los angeles don gudanar da wannan film din wanda za'a dauka a watan December mai zuwa.

Na fi so Ronaldo ya lashe Ballon d'Or — Zidane



Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce
Cristiano Ronaldo ne ya fi cancanta ya zama
zakaran kwallom kafar duniya duk da cewa bai
zura kwallaye da yawa a bana ba.
Zidane ya kara da cewa Ronaldo yana gaban
Lionel Messi wajen dacewa da lashe gasar ta
Ballon d'Or.
Ronaldo, mai shekara 31, na cikin 'yan wasan da
aka sanya sunayensu domin fafatawa wajen
lashe gasar bayan ya jagoranci Portugal ta dauki
kofin Euro 2016.
Sai dai ya yi ta samun koma-baya a kakar wasa
ta bana, inda ya zura kwallaye hudu kacal a
wasanni tara da ya buga.
Kocin na Real Madrid, Zidane, ya ce Ronaldo ne
"mutumin da ya fi dacewa da lashe gasar ba wai
don rawar da ya taka shi kadai ba, sai domin
tallafa takwarorinsa da yake yi domin su zura
kwallo."
Zidane ya ce Ronaldo ya san cewa nasarar da
yake tamu ta faru ne sakamakon aiki tukuru da
yake yi da kuma taimakwa 'yan wasan da ke tare
da shi.
Ronaldo, wanda sau uku yana lashe Ballon d'Or,
da kuma mai rike da kambun gasar Messi na
cikin 'yan wasa 30 da aka ware sunayensu domin
lashe gasar ta bana.
Dan wasan ya zura kwallaye 368 a fafatawa 357
da ya yi tun lokacin da ya koma Real Madrid
daga Manchester United a shekarar 2009.

Kompany zai ci gaba da murza leda a City -Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce
Vincent Kompany na da kyakkyawar makoma a
kungiyar, amma yana bukatar sadaukawar domin
ya rika buga wasa akai-akai bayan raunin da ya
ji.
Kompany, wanda ya buga wa City wasa sau 22 a
kakar wasan da ta wuce, ya ce ya gaji a lokacin
wasan da suka yi da Manchester United ranar
Laraba, lamarin da ya sa aka maye gurbinsa da
Aleksandar Kolarov.
Guardiola ya ce, kwantaraginsa ba ta tare a
kungiyar ba don haka babu inda za shi, yana mai
cewa "Ya ji rauni sau da dama. Amma muna
kokarin sake ba shi damar buga wa."
Kompany ya dauki kofin Premier sau biyu a City
a shekarar 2012 da 2014, amma raunukan da ya
rika ji sun hana shi katabus a bana.
Ya buga wa City wasa 33 a shekarar 2014 zuwa
2015, kasa da wasa 37 gabanin hakan.
Kompany ya koma City ne daga Hamburg a
watan Agustan shekarar 2008 kuma
kwantaraginsa zai kare a shekarar 2019.

Ba za mu kori Rooney ba —Mourinho

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce
babu inda kyaftin din kungiyar Wayne Rooney
zai je.
Mourinho ya yi watsi da rahotannin da ke cewa
an gaya wa dan wasan ya fice daga Old Trafford
zuwa wata kungiyar idan yana so a rika sanya
shi a wasa.
Rooney, mai shekara 31, bai buga wasannin lig
ba tun bayan fafatawar da ta yi da Watford inda
suka tashi da ci 3-1 ranar 18 ga watan Satumba,
kuma bai shiga wasannin biyu na karshe da
kungiyar ta yi ba saboda ya ji rauni.
Mourinho ya shaida wa 'yan jarida cewa,"Babu
wata matsala da dan wasan ke fuskanta, amma
na san kun rubuta labaranku ne domin ku sayar
da jaridunku."
A cewarsa,"Rooney babban dan wasa ne wanda
ke da matukar muhimmanci a gare mu. Babu
inda za shi- muna kaunarsa. Ba ya jin dadi ne
kawai saboda an bar shi a benchi sannan kuma
ya ji rauni."
Yanzu dai Rooney ya murmure daga raunin da ya
ji.
Kwallaye hudu ne kawai suka rage masa,
wadanda idan ya zura su zai wuce Sir Bobby
Charlton wanda ya zura wa United kwallaye 249,
ya zama gagara-badau.
But he has scored just once this season and has
not found the net in his last 10 games for
United.
Mourinho ya kara da cewa 'yan jarida sun yi
masa kazafi da suka ce zaman da yake yi shi
kadai a Manchester tamkar wani "bala'i" ne ya
same shi.

Ana rikici kan limancin Masallacin Sultan Bello

Rundunar 'yansanda a jihar kaduna ta Najeriya ta
ce ta kama mutane 14 a yayin wata hatsaniya da
aka yi kan limacin masallaci mafi girma a jihar-
wato masallacin Sultan Bello.
Rikicin ya barke ne yayin sallar Jumu'a tsakanin
magoya bayan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi da
na Dokta Khalid Aliyu wanda aka nada a
matsayin limamin masallacin na bayan tube
limamin na baya.
Magoya bayan Sheikh Ahmad Gumi na adawa da
nadin Dokta Khalid ne a zaman limamin
masallacin inda suke ganin gwanin nasu ne ya
kamata a nada.
Duka manyan malaman biyu dai sun dora alhakin
tashin hankalin kan junansu.
A wani taron manema labarai daya daga cikin
kungiyoyin musulmi mafi girma a kasar -
Jama'atul Nasril Islam ta yi Allah-wadai da
wannan lamari,inda ta yi kira ga gwamnati ta sa
baki kafin alamurra su kazance.