Saturday, 29 October 2016

An kai harin bama-bamai a Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke jihar
Borno ta Najeriya na cewa wasu da ake zargi
'yan Boko Haram ne sun kai hari da safiyar ranar
Asabar.
Ganau sun shaida wa BBC cewa bama-baman
guda biyu sun tashi ne a kusa da kofar shiga
sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi da kuma
gidan man NNPC.
Hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA, ta ce
mutum tara sun rasa rayukansu, yayin da mutum
24 suka samu raunuka.
Birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-
haren 'yan kungiyar ta Boko Haram, kodayake
yanzu ba safai ake kai masa hare-hare ba.
Dakarun sojin Najeriya na cewa suna bakin
kokarinsu na kawar da kungiyar ta Boko Haram,
suna masu kira ga mutane cewa su rika kai
rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi
ba.

Friday, 28 October 2016

Ubangiji kawai ke yi abinda yake so

– Wannan mutumin ya fadi cewa yaji murnar
Ubangiji yayin da yake addu’a
– Yace ance yaje yayi fada da zaki da
hannun sa, abunda ya faru ya zama abun
tausayi.
Yadda da Ubangiji da jin muryar shi babbar
baiwa ce, sai dai mutane da yawa sun kasa
banbanta muryar Ubangiji ta ainahi da
muryar shaidanun aljannu. Zasu ce sunji
muryar Ubangiji alhalin kawai zuciyar su ta
raya masu ko kuma yaudara ce irin ta
shaidanun aljannu.
Wani mutum dan kasar Buenos yace ya
samu umurnin da lahira , wai yaji muryar
ubangiji inda yace yaje yayi fada da zaki da
hannun sa, amma ya manta da wani abu mai
mahimmanci cewa duk wani abu na wahayi
ko mu’ujiza dole yayi dai dai da karantarwa
da littafi mai tsarki, in ka ki wannan gaskiyar
to hakika zaka fada cikin yaudara.

Ba wata aya a cikin littafi mai tsarki da tace
muyi fada da dabbobi masu hadari.
Mutumin ya saurari muryar ba dai dai ba,
kuma abun ya koma sai abun ya zamar mai
abun kaico, mutumin ya shiga gidan da ake
aje dabbobi sai ya haura katanga ya shiga
gurin da ake boye zakuna,ya fara fada da
zaki, har zakin ta kashe shi.
Wannan ya nuna cewa ba muryar ubangiji
yaji ba, saboda ubangiji ba ze taba tura ka
inda za’a kashe ka ba, kuma ubangiji ba ze
taba cewa kayi fada da wani ba.
Kullum kari ka sauraren abu da kyau karka bi
hudubar shaidan.

Yan sanda jihar Ogun sun kama yan kungiyar asiri

Yan sanda sun kama yan kungiyar asiri a
jahar Ogun
– Yan sandar shiya ta 2 na Onkan Koman na
jahar Ogun sun gano maboyar yan kungiyar
asiri
– Yan kungiyar asirin da aka kama an
gurfanar da su a kotu
Abun ban al’ajabi, sashen tsaro na yan sanda
na shiya ta 2 Onikam Legad Koman sun
gano maboyar yan kungiyar asiri a jahar
Ogun.
An gano gurin ne a Abule Ifa, unguwar Siun,
ta karamar hukumar Obafemi Awode jahar
Ogun, shugabanin tsafin guda 2 yan sanda
sun kama su, an samu layoyi kayan tsafi a
gurin su.


Mataimakin shugaban yan sanda na kasa na
shiyar, Abdulmajid Ali shi ya jagoran ci
manyan yan sanda dan, wanda ya hada da
komishi nan yan sanda na jahar Ahmad Ilyas,
sai OC na yankin DCP Suleman Balarabe,
Komandan ZIS CSP Gbenga Megbope, da dai
sauran su zuwa maboyar.

Kocin Everton Koeman na zawarcin Wayne Rooney

Kocin Everton Ronald Koeman ya ce zai ji dadi
sosai idan kyaftin din Manchester United Wayne
Rooney ya koma kungiyar.
Jaridu da dama sun yi hasashen cewa Rooney,
mai shekara 31, ba shi da makoma a United
bayan da kocin kungiyar Jose Mourinho ya ki
sanya shi a wasa.
Sai dai Koeman ya ce, Rooney "Dan wasa ne mai
kwazo kuma har yanzu yana haskakawa."
Amma Mourinho ya jaddada cewa Rooney -
wanda a yanzu kwallaye uku ne kadai suka hana
shi zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a
kungiyar - yana cikin tsare-tsarensa.
Koeman ya kara da cewa: "Ban san halin da
yake ciki ba, kuma bana son yin katsalandan.
Amma idan Rooney ya dawo Everton za mu ji
dadi."
Rooney ya koma United daga Everton a kan
£27m a shekarar 2004, kuma ya zura kwallaye
246 a wasanni 532 da ya buga.

Babu 'yan daba a kwallon kafar Ingila - Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai yarda
akwai matsalar 'yan daba a kwallon kafar Ingila
ba, yana mai yin kira da a dawo da wurin da ake
barin 'yan kallo su zauna domin kada a tayar da
yamutsi a filin wasa.
Dandazon 'yan kallo ya kawo cikas a wasan da
West Ham ta yi da Chelsea ranar Laraba.
Wenger, mai shekara 67, ya yi mamakin
yamutsin da aka tayar, yana mai cewa "ba mu
saba ganin irin hakan ba a Ingila."
Ya kara da cewa "ba zai yiwu ka yi kudin-goro ba
don kawai mutum 200 sun tayar da hargitsi."
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta goyo bayan
dawo da wurin da ake barin 'yan kallo su zauna
domin kada a tayar da yamutsi a filin wasa a
shekarar 2014.

FA tana tuhumar David Moyes

Hukumar kwallon kafar Ingila tana tuhumar
kocin Sunderland David Moyes da zargin aikata
ba daidai ba bayan an kore shi daga filin wasa
ranar Laraba.
FA ta ce ana zargin "Moyes da furta kalaman
batanci ga alkalan wasa."
Lamarin ya faru ne a minti na 90 na wasan
bayan alkalin wasa Chris Kavanagh ya ki
sauraron karar da aka kai masa bayan an yi wa
dan wasan kungiyar Victor Anichebe laifi a
da'irar mai tsaron raga.
Sunderland ta sha kashi a wasan da ci 1-0.
Moyes, wanda aka nada shi a matsayin kocin
Sunderland a watan Yuli kuma maki biyu kawai
suka samu a wasa tara da suka buga.
Yanzu dai Moyes yana da wa'adin zuwa ranar
Talata domin ya daukaka kara.

Zaben Ondo: An yi zanga-zanga a Akure

Matasa sun fita kan tituna inda suka yi zanga-
zanga a birnin Akure na jihar Ondo, a Nigeria,
domin nuna rashin amince wa da dan takarar
jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar.
A ranar Alhamis ne hukumar zabe ta INEC ta
sanar da Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar
jam'iyyar, wacce ke mulkin jihar.
Shi dai Mista Ibrahim yana bangaren PDP ne da
ke biyayya ga Sanata Ali Modu Sheriff.
Hakan ba karamin koma-baya ba ne ga gwamnan
jihar Olusegun Mimiko, da kuma dan takar da ya
tsayar Eyitayo Jegedea, wadanda ke biyayya ga
bangaren Sanata Ahmed Makarfi.
A rana 26 ga wantan Nuwamba ne za a gudanar
da zaben.
Masu zanga zangar suna goyon bayan Eyitayo
Jegede, wanda ke cikin wani bangaren jam'iyyar
Makarfi. Ibrahim ya yi takara a karkashi
bangaren Ali Modu sheriff.
Jerin sunayen 'yan takarar gwamna da hukumar
INEC ta wallafa a ranar Alhamis, shi ne jerin
sunaye na karshe na 'yan takarar gwamna kuma
sun hada da 'yan takara 27.
Yayinda da ake kone-konen tayoyi da kuma toshe
hanyoyi a wasu wurare na birnin, kwamandan
'yan sanda ya bayar da tabbaci ga mazauna
Akure cewa ba sa tare da wani hadari.
Mai Magana da yawun 'yan sandar jihar, ASP
Femi Joseph, ya shaidawa kamfanin dillancin
labarai na Najeriya ce NAN cewa, 'yan sanda sun
jaddada anniyarsu ta kare lafiya da dukiyoyin
mutanen jihar.