Tuesday, 1 November 2016

Dakarun Iraqi na luguden wuta a cikin birnin Mosul

Dakarun gwamnatin Iraqi da suka kutsa cikin
birnin Mosul, da a karon farko tun bayan
kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS sun karbe shi
shekaru biyu da suka gabata, sun ce za su ci
gaba da dannawa cikin birnin har sai baki
dayansa ya dawo karkashin ikon gwamnati.
Mai magana da yawun sojojin Iaraqin Sabah al-
Numan, ya shaidawa BBC cewa a yanzu dakarun
su a shirye suke tsaf dan fara yaakin ta hanyar
binciken kowannen gida.
Al-Numan ya kara da cewa duk da bata kashin
da aka yi a jiya talata, wanda har aka yi nasarar
kwato gidan talabijin da ke yammacin birnin
Mosul da 'yan IS suka karbe iko da shi, dakarun
su kalau suke ba tare da jin ko rauni ba.
Wakilin BBC da ke cikin tawagar su ya ce babu
alamar sassauta ruwan bama-baman da sojiji ke
yi, a daidai lokacin da suke kara dannawa dan
fatattakar 'yan tawaye daga cikinsa.
Sai dai a nata bangaren MDD ta nuna damuwa
kan makomar sama da fararen hula miliyan daya
da ke suka makale a cikin birnin.

FA ta sake tukumar Mourinho

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta tuhumi
kociyan Manchester United, Jose Mourinho, a
karo na biyu a cikin mako daya.
Tun farko hukumar ta tuhumi Mourinho kan
kalaman da ya yi kan alkalin wasa Anthony
Taylor, wanda ya shugabanci karawar da United
ta ziyarci Liverpool a gasar Premier.
Yanzu kuma ta sake tuhumar kociyan da laifin
fadin kalaman batanci ga alkalan wasan da Man
United ta tashi babu ci da Burnley a gasar
Premier.
An bai wa Mourinho zuwa ranar Juma'a domin
ya kare kansa, kuma watakila hukumar ta dauki
matakin jan kunne ko cin tara ko dakatar da shi
halartar wasan kungiyarsa zuwa wani lokaci.
United tana mataki na takwas a kan teburin
Premier, kuma ta kasa cin wasa a cikin fafatawa
hudu da ta yi.

Wanda ya sassaka kofin duniya na kwallon kafa ya mutu

Mutumin da ya tsara ya kuma sassaka kofin
duniya na gasar kwallon kafa, Silvio Gazzaniga,
ya mutu yana da shekara 95 a Milan ta Italiya.
Gazzaniga wanda ake yi masa lakabi da Mai
kofuna shi ne ya zana kofin Zakarun Turai da na
Europa.
Shi ne kuma wanda ya kera kofi mai nauyin kilo
shida da aka bai wa Brazil na din-din-din wanda
ake kira Jules Rimet, bayan da ta ci kofin duniya
na uku a shekarar 1970.
Mutane 53 ne suka yi takarar neman aikin
zanawa da sassaka wa hukumar kwallon kafa ta
duniya kofin duniya a shekarar 1971, inda ta zabi
aikin Gazzaniga, wanda ya zana mutane biyu
dauke da duniya a kafadarsu.

Klose ya yi ritaya daga buga tamaula

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Jamus,
Miroslav Klose, ya yi ritaya daga murza-leda.
Tsohon dan kwallon Bayern Munich, ya taimaka
wa Jamus lashe gasar cin kofin duniya a 2014.
Kuma ya karbi kyautar wanda ya fi cin kwallaye
a tarihin gasar gaba daya, bayan da ya zura
kwallo 16 jumulla a wasannin da ya halarta na
lokaci daban-daban.
Klose wanda ya ci kofuna biyu na gasar
Bundesliga a Bayern Munich, ya zauna ba shi da
kungiyar da yake buga tamaula, bayan da
yarjejeniyarsa ta kare da Lazio a karshen kakar
bara.
Dan wasan wanda aka haifa a Poland ya yi wa
Jamus wasanni 137, inda ya shafe tarihin yawan
cin kwallaye da Gerd Muller ya kafa tsawon
shekara 40 da cin kwallaye 68 a Yunin 2014.
Klose ya yi ritaya daga buga wa Jamus tamaula
bayan da aka kammala gasar cin kofin duniya a
Brazil a shekarar 2014, ya kuma ci wa tawagar
kwallaye 71.
Yanzu haka yana shirin komawa cikin kociyoyin
tawagar kwallon kafa ta Jamus, bayan da
Joachim Low ya mika masa goron gayyata.

Inter Milan ta kori kociyanta de Boer

Inter Milan ta sallami kociyanta Frank de Boer,
bayan da ya jagoranci kungiyar kwanaki 85.
De Boer ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara
uku a Inter a watan Agusta, bayan da ya maye
gurbin tsohon kociyan Manchester City, Roberto
Mancini.
Inter tana mataki na 12 a kan teburin gasar Seria
A ta Italiya, inda ta yi rashin nasara a hannun
Sampdoria da ci 1-0 a ranar Lahadi, kuma wasa
na hudu da aka doke ta daga guda biyar da ta yi.
Kungiyar ta nada mai horar da matasan 'yan
kwallonta, Stefano Vecchi a matsayin kociyan
rikon kwarya.
Kungiyar mai buga gasar Italiya na neman mai
horar da 'yan wasa karo na tara tun bayan da
Mourinho ya bar Inter a shekarar 2010.
Wadan da suka horar da Inter a cikin shekara
shida sun hada da kociyan Newcastle United,
Rafael Benitez da Claudio Ranieri na Leicester
City da kuma mai jan ragamar Watford Walter
Mazzarri.

'Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Mayakan Boko Haram fiye da 240 ne suka mika
wuya, bayan farmaki ta sama da kasa da
dakarun hadin guiwa na kasa da kasa (MNJTF)
suka kai a maboyarsu.
Wata sanarwa da rundunar ta MNJTF ta fitar, ta
bayyana cewa yawancin mayakan sun fito ne
daga yankin na tafkin Chadi.
Ta kara da cewa mayakan sun mika wuyan ne a
sashe na biyu na sansanin soja a yankin
Bagasola da ke kasar Chadi.
Dakarun na MNJTF da suka fito daga Najeriya,
Chadi, Nijar da Kamaru sun fara aikin murkushe
mayakan Boko Haram din da ke kasashen da aka
yiwa lakabi da ''Operation Gama Aiki''.
An kuma tantance su tare da ajiye su a sansanin,
inda Kwamandan rundunar Manjo Janar Lamidi
Adeosun ya yi musu jawabi.
Kwamandan ya ce za a ba su horo a fannoni
daban-daban na sana'oi, kamar yadda hukumomi
da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka
tsara.
Sojojin dai sun samu galabar toshe kafofin
samun abinci da kayan fada zuwa ga mayakan,
da hakan ya sa su da iyalansu kaura daga
matsugunansu suka mika wuya.
Galibinsu dai sun mika makamansu a sansanonin
soji mafi kusa da su a yankin.
Hakan dai ya kawo adadin mayakan na Boko
Haram da suka mika wuyansu zuwa 460 kawo
yanzu.
Bayanai sun nuna cewa akwai mayakan Boko
Haram da dama a yankin na tafkin Chadi.

Yadda Zaka Mayar Da Android Dinka Ta Koma Kamar iPhone


Barkanku da warhaka maziyarta shafin amanagurus. Fatan kun wuni cikin koshin lafiya ta yanda zaku samu damar karanta bayanai gami da matakan da zan zayyano maku akan yadda zaku mayar da wayoyinku na android su koma kamar iPhone.
Idan ba a manta ba a can baya nayi wani rubutu akan Yadda Zaka Mayar Da Wayarka Kamar Android 7 Ba Tare Da Upgrade Ba. To a yau kuma zaku ga yadda ake mayar da android tayi kama da iPhone.
Kasantuwar kamfanin Apple a matsayin wanda yayi fice wajen kera sababbin wayoyi da suka dace da zamani sannan kuma suke biyawa masu amfani dasu manyan bukatunsu na bangaren fasahohin zamani. Kama daga yanayin ingancin su zuwa abubuwan da suka kunsa, iPhone ta kasance tana da karfin tsaro dangane da bayanan mai amfani da ita.
Abubuwan dana zayyano a sama dama wasu sauran muhimman abubuwa ne suke sa mutane ke sha'awar ganin su mallaki ko kuma yi amfani da wayoyin kamfanin Apple. Sai dai kuma yanayin tsadar kudin wayar ya hana mutane damar mallakar ta wanda a dalilin hakan ne zan yi muku bayanin yadda zaku juyar da android dinku tayi kamar iPhone.
Abubuwan da ake bukata
- One Launcher (Dauko shi daga playstore ko kuma daga nan
- Messaging+ 7 ( sauko da shi daga playstore ko kuma ka danna Nan gurin

Yadda zaka mayar da wayar tayi kamar iPhone

• Da farko dai sai ka dauko one launcher sannan kayi launching / activating dinta akan wayarka, sannan sai ka zabi wallpaper da kuma yanayin yadda kake son menu dinka ya kasance. Duba screenshot din da nayi a wayata:
Ga kuma yanayin notification bar din wannan launcher din ke dauke da shi, haka zalika akwai search box me kyau a tattare da wannan launcher din
• Abu na biyu sai ka dauko messaging+ 7 sannan kayi install a wayar taka. Wannan shine zai baka yanayin shafin tura wa da karbar sako irin na iPhone....
Akwai wasu karin manhajoji da yawa wadanda zasu kara ma wayarka kyau dangane da kwaikwayon kirar iPhone. Akwai manjoji kamar su; iLauncher, Launcher 8 Pretty , i Call screen Free + Dialer da sauran makamantan su.
Wannan shine dan takaitaccen bayani kan yadda zaka mayar da wayarka tayi kama da iPhone...