Friday 2 December 2016

Home Mutum 100,000 na fuskantar yunwa a arewa maso gabashin Nigeria

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa fiye
da mutum 100,000 na hadarin kamuwa da
matsananciyar yuwan a arewa maso gabashin
Najeriya.
Majalisar ta ce mutanen za su fada cikin
mummunar yunwar ce sakamakon farin da ya
auku saboda rashin yin noma a yankin.
Wani rahoto da majalisar ta fitar ranar Juma'a
ya ce duk da yake jami'an tsaro sun kwato
garuruwa da dama daga hannun 'yan kungiyar ta
Boko Haram, amma manoma ba za su iya yin
aiki ba saboda fargabar sake kai musu hare-hare.
Majalisar ta kara da cewa kimanin mutum
miliyan bakwai na matukar bukatar taimako a
yankin.
Ta yi kira da a tara sama da $1bn domin kawar
da abin da ta bayyana a matsayin "babban
bala'in da ke addabar Afirka a halin da ake ciki."

No comments:
Write Comments