Friday 2 December 2016

Home Nigeria: Kotu ta umarci gwamnati ta saki El-zakzaky

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Wata kotun tarayya da ke birnin Abuja ta umarci
hukumomin tsaron Nigeria da su saki shugaban
kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta 'yan
Shi'a Sheikh Ibrahim El-zakzaky.
Kotun ta bukaci a saki El-zakzaky nan da
kwanaki 45 ba tare da wani sharadi ba.
Alkalin kotun Kolawale Gabriel ya ce tsarewar da
hukumomi ke cigaba da yi wa El-zakzaky tun
watan Disamban bara haramtacciya ce kuma ba
ta da hujja a karkashin dokokin kasar.
Haka ma ya umarci hukumomin da su biya shi da
matarsa kudi Naira miliyan 50 a matsayin kudin
fansa na tsare sun da aka yi a haramce.
A shekarar da ta gabata ne dai sojojin Najeriya
suka kama shugaban 'yan Shi'ar bayan wata
arangama da magoya bayansa a Zaria da ke
arewacin kasar.
Akalla magoya bayansa 349 jami'an tsaro suka
kashe a lokacin tarzomar.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na gida da
waje sun yi Allah-wadai da lamarin, sai dai
sojojin sun kare matakin da suka dauka.

No comments:
Write Comments