Friday 2 December 2016

Home Trump ya nada 'mahaukacin kare' a muƙamin sakataren tsaro

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya
nada James Mattis, tsohon fitaccen sojan ruwan
nan da ya yi yaki a Iraqi da Afghanistan, a
matsayin sakataren tsaron kasar.
Trump ya ce, Janar Mattis mutum ne "ƙwararre",
a lokacin da yake yin jawabin ba shi mukamin a
jihar Ohio.
Janar Mattis, wanda ake yi wa lakabi da
"mahaukacin kare", mutum ne da ya saba yin
katobara, wanda kuma ya fi suna wajen caccakar
shirye-shiryen gwamnatin Obama kan yankin
Gabas Ta Tsakiya, musamman kasar Iran.
Ya taba bayyana Iran a matsayin "kasa daya tilo
da ta fi yin barazana ga zaman lafiyar a Gabas
Ta Tsakiya".
Mr Trump ya yi bayar da sanarwar nadin Janar
Mattis ne a Cincinnati lokacin fara gangamin
"Godiya ga Amurkawa na shekarar 2016".
Ya shaida wa magoya bayansa cewa, "Za mu
nada 'Mahaukacin kare' a matsayin sakataren
tsaronmu. An ce shi ne mafi kusanci ga Janar
George Patton, fitaccen mutumin da ya yi yakin
duniya na biyu."
A baya dai Mr Trump ya bayyana Janar Mattis,
mai shekara 66, a a matsayin "Janar din da babu
kamarsa".
Shi ne mutumin da ya jagoranci bataliyar Amurka
a yakin tekun fasha na shekarar 1991 da kuma
hadin gwiwar jami'an tsaro a kasar Afghanistana
shekarar 2001.
Yana cikin sojojin da suka mamaye Iraqi a
shekarar 2003 sannan shekara daya bayan haka
ya taka muhimmiyar rawa a yakin da aka yi a
Fallujah.
Janar Mattis ya yi ritaya a shekarar 2013 bayan
ya zama kwamandan rundunar sojin Amurka ta
tsakiya.

No comments:
Write Comments