Thursday 1 December 2016

Home 'Nigeria ce ta biyu a cuta mai karya garkuwar jiki'

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Wani tsohon jami'in Hukumar Majalisar Dinkin
Duniya mai kula da hada yaduwar cutar Ƙanjamau
ko kuma HIV/AIDS, a Uganda, Musa Ahmed
Bungudu, ya ce Najeriya ce ta biyu a cutar a
fadin duniya.
Tsohon jami'in ya ce kasar Afirka ta Kudu ce ta
farko a yawan mutanen da ke dauke da kwayar
cutar ta ƘAnjamau.
Alhaji Bungudu ya kara da cewa a Najeriyar an
haifi jarirai kimanin dubu 60 masu dauke da
kwayar cutar.
Ya kuma ce rashin mayar da hankali wajen dakile
cutar ne ya janyo wa Najeriyar halin da take ciki.
Dangane kuma da nasarorin kan yakar cutar,
Bungudu ya ce, wasu kasashen na Afirka sun yi
samu nasara amma fa banda Najeriya.
Akwai dai kimanin mutane miliyan 37 da ke
dauke da wannan cuta a fadin duniya.
Ranar 1 ga watan Disambar kowace shekara, ta
kasance ranar yaki da cutar mai karya garkuwar
jiki, ta duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta ware ranar da
manufar wayar da kan al'umma a kan illolin da ke
tattare da cutar, da kuma hanyoyin da za abi
wajen hana yaduwarta da ma rashin kamuwa da
ita.

No comments:
Write Comments