Thursday 1 December 2016

Home Ana kisan kare-dangi a Sudan ta Kudu — UNCHR

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai tabbatar
da hakkokin bil-Adama, UNCHR, ta yi gargadin
cewar ana kisan kare-dangi a kasar Sudan ta
Kudu mai fama da yake-yake.
Ta kuma ce ta lura ana amfani da yunwa da
kona kauyuka da ma fyade a matsayin wani salo
na yaki a fadin kasar.
Hukumar mai mambobi uku, wadda aka kafa ta a
bana, ba ta jima ba da kammala wata ziyara ta
kwana 10 a kasar ta Sudan ta Kudu, wacce ta
kwashe shekaru fiye uku cikin rikice-rikice.
Shugaba Salva Kiir ya musanta cewa ana yi wa
wasu kabilu kisan kare-dangi.
A wata sanrwa da ta fitar ranar Alhamis,
hukumar ta UNCHR ta ce, "Ana share fagen
maimaita abin da ya faru a Rwanda" a 1994, tana
mai ambatar kisan gillar da aka yi wa mutum
800,000, galibinsu 'yan kabilar Tutsi da 'yan
kabilar Hutu masu sassaucin ra'ayi a cikin wata
uku.
Shugabar mambobin ta hukumar, Yasmin Sooka,
ta ce a duk wuraren da hukumar ta ziyarta a
Sudan ta Kudu, ta ji "kauyawa suna cewa a
shirye suke su ba da jininsu don kwato
filayensu".
Yakin basasar Sudan ta Kudu ya tilasta wa
mutum fiye da miliyan biyu tserewa daga
gidajensu.
Hukumar ta ce ta fahimci ana kikrkirar yunwa da
kona kauyuka da fade a matsayin garkuwa a
lokutan da ake gwabza yaki a kasar.
A kwanan nan mambobi uku na hukumar da aka
kafa a farkon shekarar nan suka kammala jiyarar
aiki ta kwanaki goma a Sudan ta Kudu, wadda ke
fama da rikici tsawon shekara uku.
Shugaba Salva Kiir ya musanta zargin ana
kokarin kawar da jinsi.
A jawabin da hukumar ta fitar a ranar Alhamis,
UNCHR, ta ce "ana kokarin maimata abinda ya
faru a Rwanda" a 1994 - inda aka kashe mutane
800,000 yawansu 'yan Tutsi da 'yan Hutu suka yi
a cikin wata uku.
Babban jami'i na UNCHR, Yasmin Sooka ya ce
duk inda tawagarsu ta shiga a Sudan ta Kudu
suna jin mutane a kauyuka na cewa a shirye
suke a zubar da jini domin su kwato yankinsu.
Yakin basasa a Kudancin Sudan ya yi sanadiyyar
raba mutane sama da miliyan 2.2 da suka
tserewa gidajensu.
An fara rikicin ne a shekarar 2013, shekara biyu
da Sudan ta Arewa ta samu 'yancin cin gashin
kai, bayan da Shugaba Salva Kiir ya kori
makarrabansa da kuma zargin mataimakinsa Riek
Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa da ba
a yi nasara ba.

No comments:
Write Comments