Saturday 31 December 2016

Home YADDA AKE WANKAN JANABA DANA BIKI DA WANKAN HAILA DA SAURANSU

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA
DAI SAURAN SU.
Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.
Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai
'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira
'siffatu kamal' (ta kamala).
Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne:
Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a
gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:
zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke
hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a
cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka ، a
dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin
zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa)
wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka
ma'ana kayi tsarki kenan ، to daga nan kuma sai
kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin
da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu
daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale
shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma
hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka
debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda
kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi
yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda
yake, don gashin dan Adam yakan bude
musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa
a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani
abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin
tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka
tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake
kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a
kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a
kanka.
To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game
dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da
bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan
na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina. To idan
kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi
ne sai ka wanke kafar ka ta dama sannan
kafarka ta hagu shine cikon alwalar da ka riga ka
faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan
janaba.
In wankan janaba ne haka zakayi, in na haila ne
haka za'ayi inma wanka ne na biki haka mace
zata yi, idan wankan jumu'a ne ma haka za'ayi,
wankan idi ma haka zaka yi, banbanci kawai shi
ne NIYYA.
Idan mutum zai yi siffa ta 'Al ijza' wadda ta
wadatar ba sai kayi alawa acikin ta ba, kana
zuwa kayi niyyar yin wanka din kawai sai ka
dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko'ina,
inma wani kududdufi ne ko rami ko swimming
pool sai kayi tsalle ka fada aciki, dama ka kulla
niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da
zakayi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki
da kuma shaka ruwa a hanci da facewa.
Shike nan, kuma ya halatta kayi sallah da
wannan wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya
nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika
kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika
cikar kamala, ya fika lada.
Kasancewar ba'ayi alwala ba ciki, wannan
ka'idace ta malamai cewa karamin kari
(HADATHUL ASGAR) idan sun hadu da babban
kari (HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da
babban kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai
bane idan ka kawar da karamin ace babban ma
ya tafi.
Bissalam

No comments:
Write Comments