Friday 2 December 2016

Home Wa zai yi nasara tsakanin Man City da Chelsea?

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Manchester City za ta karbi bakuncin Chelsea a
gasar cin kofin Premier wasan mako na 14 a
ranar Asabar.
Wannan shi ne karo na 154 da kungiyoyin biyu za
su kece raini a tarihi, inda City ta ci wasanni 52,
Chelsea ta samu nasara a wasanni 62 suka yi
canjaras sau 39.
A gasar cin kofin Premier ta bara, City ce da
doke Chelsea 3-0 a Ettihad, sannan ta kara doke
ta 3-0 a Stamford Bridge, yayin da Chelsea ta
samu nasara a kan City da ci 5-1 a gasar FA.
Chelsea ce ke mataki na daya a kan teburin
gasar Premier da maki 31, yayin da Manchester
City ke matsayi na uku da maki 30.

No comments:
Write Comments