Thursday 1 December 2016

Home Nigeria: '$19m za su kai-komo tsakanin mutane saboda N-Power'

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce
sakamakon shirin daukar matasa dubu 200 aiki
da gwamnatin kasar ta yi, za a samu kusan
$19m da za su kai-koma a hannun 'yan kasar.
Wasu dai na ganin cewa shirin na N-Power da
gwamnatin Najeriya ta fara aiwatarwa ranar
Alhamis, kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.
Suna kuma bujuro da dalilin yawan matasan
kasar da ba su da aikinyi da sun kai miliyoyi.
Sai dai kuma Abubakar Aliyu wanda masanin
tattalin arziki ne a Najeriya, ya ce Naira dubu 30
din da za a rinka biyan matasan su dubu 200, a
kowane wata, yawanta zai kama Naira Biliyan
shida wato kwatankwacin Dala miliyan 19.
Ya kuma kara da cewa kudin za su kai-komo ne
a tsakanin 'yan kasar, al'amarin da zai bunkasa
yalwar arziki sannan kuma ya farfado da tattalin
arzikin al'umma.
Ku saurari yadda hirarsa masanin ta kasance da
Muhammad Kabir Muhamma:

No comments:
Write Comments