Thursday, 17 November 2016

Home NNPC na ci gaba da binciken mai a arewacin Nigeria

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


A Najeriya, kamfanin man kasar, wato NNPC ya
sake komawa yankin Chadi don ci gaba da
bincike da nufin gano ainihin adadin mai da
iskar gas din da ke karkashin kasa a yankin.
A wata hira da BBC, shugaban kamfanin man
Najeriya, Dr Maikanti Baru, ya ce NNPC zai yi
amfani da wasu manyan na`urori wajen yin
binciken.
Ya kara da cewa idan har abun da aka samu ya
kai wani mizani, to kamfanin zai dukufa wajen
hakar man.
Tun a shekarun 1970 ne wasu masana da kuma
kamfanin NNPC suka yi hasashen cewa za a iya
samun mai a yankin, kuma tun daga wancan
lokacin aka yi yunkuri daban-daban don binciken
man amma ana dakatarwa saboda wasu dalilai,
ciki har da zargin cewa akwai siyasa a cikin
lamarin.

No comments:
Write Comments