Saturday 26 November 2016

Home Nigeria: Yau za a fara kada kuri'a a jihar Ondo

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Yau ne hukumar zaben Najeriya mai zaman
kanta wato INEC za ta gudanar da zaben
gwamna a jihar Ondo dake kudu maso yammacin
kasar.
Hukumar zaben Nigeria INEC tace ta shirya tsaf
dan tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a
jihar.
Haka kuma an tanadi dukkan kayan aiki da ake
bukata dan gudanar da wannan aiki.
Jam'iyyu 28 ne dai za su fafata kuma hukumar
zaben kasar ta ce ta kammala dukkan shirye
shirye na gudanar da zaben.
Kuma zaben na jihar Ondo ya dade ya na daukar
hankalin al'umar kasar, ganin irin barakar da ta
kunnu kai tun wajen tsaida 'yan takara a manyan
jam'iyyun siyasar kasar wato jam'iyya APC mai
mulkin kasar da kuma babbar jam'iyyar adawa ta
PDP.

No comments:
Write Comments