Friday 2 December 2016

Home 'Zai wuya Zakzaky ya zauna a wani gari ba Zaria ba'

Danna hoton don shiga whatsapp group dinmu 👇👇👇👇


Kungiyar 'yan uwa Musulmai ko kuma Islamic
Movement of Nigeria bai bin tafarkin Shi'a, ta
ce, ta yi farin ciki da hukuncin da babbar kotun
Abuja ta yanke na a saki shugabanta, Sheikh
Ibrahim Zakzaky.
A ranar Juma'a ne dai alkalin wata babbar kotun
Najeriya, Mai shari'a Gabriel Kolawole, ya yanke
cewa gwamnati ta saki Elzakzaky cikin kwana
45.
Sannan kuma a ba shi diyya shi da mai dakinsa
ta Naira Miliyan 25 kowanennen su.
Kotun ta kuma umarci gwamnati da ta gina wa
shugaban na IMN gida a duk inda yake so
kasancewar an ruguje gidansa.
To sai dai wasu jiga-jigan 'ya'yan kungiyar sun
fara yin tsokaci dangane da batun sake gina
gidan a Zaria ko kuma a wani gari daban.
Malam Abdulhameed Bello wanda shi ne jagoran
'yanuwa musulmin a Zaria, ya ce, sun yi murna
da jin hakan amma fa ba ya tunanin El-zakzaky
zai so zama a wani gari sabanin mahaifarsa,
Zaria.
Tun dai watan Disamba Elzakzaky yake tsare a
hannun gwamnatin Najeriya, bayan wani farmaki
da sojojin kasar suka kai wa mabiyansa bisa
zargin yunkurin halaka babban hafsan sojin
kasar.

No comments:
Write Comments